SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Da ni dake bazamu iya kare ta ba, ba gwara mu saida ran mu tun yanzu ba kafin abubuwan suzo sufi karfin mu..
Ummah Ta dago ta kalle sahura tare da sauke karamin hawaye tace….gaskiya bazan iya karuwan ci ba sam sam sam sam bazan iya ba ..
Wannan ba tarbiya ta bace sahura.
Ni dai zanje na cigaba da aikin wahalan a haka bazan iya ba kiyi hakuri kinji?
A rude ummahn ke maganan har jikin ta na bari tayi kuma saurin dakale hannun sahura ta bar wajen tana kuka..
Wani irin yanayi sahura ta shiga ciki na rashin jin dadi amma sai ta daure ta bi ta tana jawo ta tana fincikewa
Tace ke gambo kar ki tara makanki jama’a ki tsaya muyi magana…
A zafafe ummah ta juyo tace nagode da dukkan
Taiimakon ki da kulawar ki sahura amma wallhy na gwammaci na mutu dana sake kai kaina ma wannan Tsinannen shegen…
ki sake ni naje sahura ki sake ni naje neman halak dina kawai shiyafi min..
” ba yadda ta iyah da ummah sai tace To
Kije!
Kije ki kashe kanki daga nan har mahdi ya bayyana naga ko zaki tabuka wani abu.
Ni dama Sauki nake nema miki gambo da kamar kinsan abunda ke miki ciwo a duniyan nan zaki gane hakan amma kin butulce makan ki…
To wallhy ki daina zubda hawayen banzan da kike yi na cewa kina son rayuwa ma saratu babu abunda kike so mata illa bakar azaba irin namu…
Ummah ta girgiza kai batare da tace komai ba ta fincike hnnun ta jikin sahura ta wuce tayi gaba..
Da kyar ta rarrashi kanta ta waske ta tafi neman aikin amma sosai zuciyan ta ke mata nauyi da tunani kala kala..
Itama sahuran haka ta kai kanta cikin gida ta yi kwanciyar ta, tunanin ta itama take yi dama ta san dole sai an sha fama kafin ummah ta gane abunda ta ke gane mata..
Amma gani take hakan shine masu mafita mai inganci.
Ita gani take kawai a matsayin su na marasa gata da galihu, tsinnanu,marasa ilimi babu wani abunda zai yi kargo arayuwan su dole su rufe ido suyi wanda basu so din..
Ita ma bata son haka amma ko da ta zo birnin itama a dole da shi ta dogara take tallafa wa kanta sai dai babu wanda ya sani don ita kanta ba son rayuwar take ba..
Bangaren umma kuwa Tun daga ranar da hakan ya faru tsakanin su da sahura abubuwa suka dada tsanan ta mata
Duk dama sahuran tayi kokarin wajen shawo kanta amma fafur ummah ta turje..
Tun daga nan itama sai bata sake dago maganan ba kuma bata nuna tayi fushi akan ra’ayin ummahn ba ita dai ido ta zuba mata,,
Sai dai yanzu idan ta fita kasuwar su dake kusa neman aiki da shike bayan gari ne, toh daga mai bata aiki agidan giya sai mai ce mata ta zama mai musu aikiin danna a Restaurant.
Abubuwan rashin mutunci ba wanda bata gani ba
Ta haka sahurah ke shigo mata da maganan cikin salo tana nuna mata dalili
Gashi dai boro boro maganan sahurah na cewa ummahn wahalar dakan ta zatayi kawai a rayuwa ya nuna afili amma ummah sam ta ki ta bada kai ma karuwanci.
duk suna yi ne ban sani ba,
Rana guda da sahurah da ummah suka samu wani mummunan tsabani akan shigowar da wani dan harkan ta yayi bazata har bayan gida ya iske ummah tsirara tana wanka .
Duk dama anty sahurah tayi rantsuwar cewa bata san da zuwan sa ba
amma ummah sai take ganin kamar kawai sahurah ta nace ne sai ta gurbata mata tunanin akan tarbiyan ta da wayo..
hakan ya sa ummah ta roka mana temporary work na aikin gida a nan gidan alhaji buba, inda da take wanke wanke da safe ana bata abinci..da shike ma mai aikin nasu na asali ta haihu taje gida
sai aka bamu daki guda daya muna zama agidan.
Gidan ba laifi amma sai dai matar gidan na da mugun kyankyami, ga son girma da nuna isa akan gidan don haka ne ma sam sam bata son kuskure.
Tsakanin ummah da anty sahurah sam banji dadin ‘zaman su ba sabida na saba da anty sahurah sosai..
duk da yanayin rayuwar mu ita bata nuna mana gadara da kaskanci boro boro
Sati biyu mukayi anan gidan alhj sai da na matsa ma ummah suka shirya da anty sahura suka fahimci juna.
Sai dai ummah tace bazamu koma gidan ta ba tukun a tunanin ta ko idan anga kwazon ta wajen aikin ta zai sa a dan bata dama itama tayi aikin permanent da su
Alhj sabo shine mai kudi a duk yankin anguwar mu
Haka muka zauna muna aiki da shike aikin gida ne sai nake taya ummah na ,aika da sauran su.
A kwana a tashi zaman mu anan ba abunda muke fuskanta sai kaskanci amma bai dame mu,sai a cikin kwanan mu na ashirin da hudu a ranar da daddare
Muna bacci wasu mutane suka shigo gidan alhj.
kowa ya tsora ta musamman ma ni da ummah da muka tabbatar cewa barayi ne fa suka shiga cikin gidan sata,
Bayan shigar su da kamar minti 10 sai gashi ana buga namu kofar,
Kamar zan shide dan tsoro na rike kafar ummah sosai muna rawan dari..
haka aka fito damu tsomo tsomo aka hada mu da su alhaj da hajiya akasa tsakar gida.
Jaka ne a hannun su alaman sun karbe abunda suka zo daukewa daga ciki.
fuskan su duk arufe yake,
ogan su ya fara cewa mu bashi kudi ko ya kashe mu,…
Da kyar ummah ta bude baki cikin tsoro ta ce musu mu masu aikin gida ne bamu da ko sisi sai abunda za’a bamu..
ban san ko wannan maganan bane ya bata ma hajiya da alhaji rai.
ko zallan tsoron bindigogin dake kanmu ne oho
“Har ya sa suna ji babba daga cikin barayin nan
Ya ke jayayya akan idan har ummah bata da kudi zasuyi raping dina..
Hankalin ummah in akwai karshe wajen tashi
Ya kai nan..har ta mance bindiga ne akanta wajen roko da magiyan da sunan Allah akan su rufa mata asiri amma ba imani ko kadan aran su
Ji nake kamar sun kashe masu gadin gidan ma don babu motsin kowa..
Nan in banda kuka babu abunda nake yi..
haka suka damke ni zasi kwantar dani agaban su ummah Tazo da gudu cikin kuka tafada akai na tana dada rokon su su kyale ni cikin kuka mai ban tausayi da tashin hankali..
duk wanda yake da imanin wajen sai da ya sauke mana hawaye amma ko ajikin su..
Na rude sosai ina cikin tashin hankali har sai da na budi baki nace ma ummah,in har za’a min fyade toh lalllai zan iya mutuwa a yau ta yafe ni….
Kamar na dada taurara mata rai ta dada rufe ni ta kankame ni tace sai dai akashe ta amma kam bazata bari a cutar dani ba..
Dariya barayin nan suka shiga mana
Yace ma ummah shi ba zai kashe ta ba amma zai koya mata darasin da bazata taba mantawa ba
A bisa bata masa lokacin da tayi yanzun..
“Innnalilhi wa inna ilahi rajiun inaji ina gani yasa aka kai masa ummah na cikin dakin mu…
Ya bita ciki saura na kanmu sa bindiga
Ba abun da nake ji sai motsi da kukan ummah wajen minti 14 sai gashi ya fito yana gyaran wandon sa…
A wannan lokacin karamin bugawa zuciya ta tayi ina ta kokarin kare kaina daga tabewar hankali..
Dai dai da shigowar wani a wargaje yana cewa ogah is time..muje kawai babu lokaci
Duk sun fahimci kansu sai suka hanzarta suka bar mu anan…
Da uban gudu na mike na shige dakin
Ummah ne a takune agefe ta rufe jikin ta da kunceccen zanin ta tana wani irin kukan dake taba min kokon zuciya na…
agaban ta na zube ina bari duk na kasa sake muryan na domin kuwa kukan dake damuna ya harde min magwaro tamkar idan na bude shi zai harde ne in mutu.
kuka kawai muka rungume juna munayi ba wanda ya iya magana mai tsayi..
Har Allhj da hajiya suka shigo suka bamu baki kamar da gaske..
A daren da bamuyi bacci ba tsaban kunci.
amma sai dai kuncin bai kai wanda muka fuskan ta ba bayan an gama bincike game da barayin