HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

duk fushin asarar da su alhaji da hajiya sukayi kaf suka sauke shi akan kowa musamman ma mu maikatan gidan..

Karshe ma ta sa aka bincike ummah a caji ofis cewar ta hala samarukan ta ne ta hade baki da su don su cuce su.alhhj ma ya goya mata baya wai ai ba ataba zuwa musu sata ba sai da ummah ta fara aiki da su.

Da kyar anty sahura ta taimaka aka gano gaskiyar lamarin aka kyale ummah

haka suka kora mu ni da ummahn,wajen masifar ba amana adalci ba har ummah ta kona kafar ta da ruwan zafi tsaban bacin rai da takaici..

Alhj har da ce ma ummah na ai dai dai kenan
A ganin sa dama wacce bata da miji kam ai watsasiya ce..
abun yamin zafi sosai

 

Bayan haka Gidan anty sahuran muka sake komawa ta tausaya mana sosai…

Yanzu hakan anty sahura da ni ke sa ma ummah magani a kafarta daya kumbura sosai yana fid da ruwa da kyar take dingisawa take fita gwanin tausayi…

babu wanda yake tausaya mata abubuwa sai chagude mana sukeyi,

wata rana ma sahura ke ciyar da mu rana da yamma da dare..

Tunani sosai ya sata agaba damuwa da sacewar imani sai ya soma shigan ta sosai..

Dadin karawa da taga yan maza sun fara gane akwai budurwa anan har an soma kawo hari ..

Hankalin ummah sai ya tashi yaKi kwanciya,sai ma ta yanke fita neman abincin kwana biyu tana zaune tana sakewa da warwarewa tana kuma bada hankali sosai wajen jinyar kafar ta don har ya bushe yana rufewa..

Yau cikin watan mu biyu har da sati guda Bayan rabuwar mu da rayuwar mu a kurwala .

A daren yau ne ummah ta yanke makan ta daukar shawaran sahura

Zata je kamar bazata je ba, amma ta riga ta yi tunnanin ta ta hada calculation din ta alamun kuma sun fi tasiri a zuciyan ta..

Hakan ta je ta samu sahuran suka sake kulla fahimtar juna

Suka warware niyyar su akan saving rayuwar da zasu bada karfi akai da cimma burin su na rayuwa..

Sannan ummah ta ce” duk abunda zatayi zatayi ne sabida na tashi na tsaya na da kafa na a duniya,
Tana samun hakan har abada ta bar hanyar….
Sai abunda rayuwa kuma tayi…

Sahura ta dada karfafa mata gwiwa tare da bata tabbacin kwanan nan burin su zai cika

Kuna zasu zama mutane kamar yarda suke muradi
Komai zai daidaita..
Duk sunyi hakan ne tare da alkwarin boye min Komai…

Sirri ne tsakanin su wanda sukadai suka shirya shi

Ina gidan sai kawai nake ganin wani sabon sHakuwa ya shiga tsakanin ummah da anty sahura…

Sai naga ummah yanzu ta watsar da neman kudi
Anty sahura ke bamu abinci mun dada dawowa tamkar gida daya jini daya..

Abun da yafi bani mamaki shine yadda suka sa kai akan wasu abubuwan,kamar wanka kwalliya, sa sutura koyan magana da dan tawalidu na yan birni naga duk umma na koya wajen anty

..na dauka ko duk strategy ne na neman wani aikin tunda ga wahalan data ke sha awajen har da rainin wayon yan birni.

Wani wata gudan suka dauka suna shiri..

Da shike sun sa abun arai lokaci kalilan ummah ta iya sa suturan da anty sahura ke bata

Ta kuma iya sa powder da jan baki ga wani sabon Wayo da ta karo ma kanta don yanzu na ji da salon suna ummah ake kiran ta wato fadima…

Abu kamar wasa, suka shirya tsaf ranar asabar da yamma suka kama hanyar Adress din SSA danjuma..

Gida ne mai kyau mai tsari,amma daga bakin kofar gate aka dakatar da su.

Mai gadi yace kuka ce wajen oga kuka zo…ummah tace eh..shiya bani wannnan ta yi masa nuni da confidential
Card…yace miye sunan ku…
Duka suka fada sahura da fadima

Baice komai ba ya juya ta shiga dan dakin su ya buga masa waya…
Suka yii magana
Yace abada ummah wayar..

Ta na cewa hello,

Ya dago muryan ta amma mamakin ya hana sa boye dan takaitaccen dariyar da ke damun sa arai…

Yace kin zo da mutaner ki su kamani ko?..

Ta gyada kai kamar wacce take gaban sa tace kawai nazo wajen ka ne….

Yace fadimatul fauziyyat. I like that da wuri kika shiga hankalin ki..i said it Ure a smart girl dama na sani…
Ita dai tana shiru

Yace’..Yanzu kin san me?

Ki jira ni anan inda kuke zan bada mota yanzu akai ku quest house dina ku jira ni ina zuwa tace toh..ta mika waye ma mai gadi..

Nan ta sanar da sahura yadda sukayi ko minti 5 basu kara ba aka zo aka fito da mota kirar jeep aka dauke su zuwa guest house din ssa danjuma..

 

 

 

 

 

 

 

*WATTPAD VOTE AND FOLLOW @SURAYYAHMS*

 

*OFFICIALCATTY????*
[2/23, 23:24] ‪+234 802 646 5734‬: *????BRILLlANT WRITERS ASSO????*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™jan2019
????????
*SAMARIN SHAHO*
????????
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*

_YA HAYYU YA QAYYUM_

_PAGE8_

Bayan isar su ummah da minti 20 sai ga shi ya shigo da yan mata biyu wanda akallah bazasu fi shekaru 22 zuwa 23 ba…

Kowacce ta rike sa sai wasan banzan su suke, anan ummah ta dauke kai tana Allah ya sawwake ta ga yarta saratu a wannan irin rayuwar,tunanin haka ya sa bata wani dago ta kalle su ba har ya sallame su ya zo ya zauna suka gaisa da ummah da anty sahura..

Tunanin sa ko anty sahurah yar uwan ummah ne amma haka fir suka ki gaya masa asalin relationshp din su.

Chan ya sa aka kawo musu abinci da sauran su,suna ci yana tanbayar ummah abun da ke tafe da ita,

Ba bata lokaci tace “ranar kace idan ina bukatar taimako zaka taimaka min,

Dama aiki Muke nema ta wajen ka.tayi nuni ita da anty sahura..

“yayi shiru domin kuwa dama Ya sha mamakin zuwan tan sosai amma bai kai mamakin da ya sha ba yanzu data furta aikin take nema kuma tawajen sa.. .
kenan fadima zata iya kwana da namiji? Ko dai wani abu ne ya same ta?..yana rayawa aransa yana kallon ta…

Cahn yayi murmushi yace fadima kenan,ai ni dama na baki a farko sabida nasan baki gane ni waye ba ko?

a hankali ta gyada ka

Yace, aiki kam bazaki rasa shi ba ko dan abun da ya faru tsakani na dake zan duba na gani

Sai dai akwai sharadi,ta dago ta dube sa yace “kin tabbata kin shirya ma aikin da kika kawo kanki?

Ummah tayi shiru, wani bugun zuciya ne take famar danne shi amma sai tayi yake,tace na shirya Zanyi…

Sai dai fa kasan damuwa ta baifi na sami abun da zan tallafa rayuwata ba ne,so acire maganan jin dadin rayuwa da rudin duniya aiki kawai zanyi…

yadda tayi maganan yasan kunci da takaici ya sata furtawa Sai yayi karamar murmushi yace toh ai shikenan,

Ki rike alkwarin aikin ki nima zan rike miki naki alkwarin deal?..

Ta dan gyada kai ta dube sahura..

Nan ya cire kudi kimanin 5ok da kati mai dauke da adress ya ajiye kan table yace ga wannan ku saka kaya ku zo nan anjima da misalin karfe 9.

ummah ta dauka ta bada sahura ta duba,strip club ne amma na manyan mutane…

sahura tace mungode sir,yayi murmushi yace idan dokan aiki tafara ba gudu ba ja da baya…
ni ne shugaban ku.

ummah ta mike da cewa mun maka alkwari yace to sai na ganku…nan suka fice suka koma gida..

zuciyar ummah cike yake da damuwa amma haka take bunnewa suka siyo kayan da zasu sa da dan abinci da sauran abunda zasu bukata na kansu da sabon sana’ar su

ummah cemin tayi ta same aiki amma zata fara gwadawa domin aikin dare ne, kuma yana da kyau sosai za a bata kudi dayawa.

ganin ita da anty sahura ne zasu tafi yasa na kwantar da hankali na ban yi mata musu ba..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button