SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Baba laure ne akai na cikin masifa kamar zata wanka min Mari
“Sum sum na dago a kasale na shiga watseke wa tare da mutsuka ido Daga lungun da na rakube ena gyan gyada wa a hankali na daddafe na mike a ladabce nace”
“Ena wuni baba Laure”
..ban amsawa. yi maza ki wuce gidan ku tun da ke kunnen kashi ne dake …maza wuce ,fitinanniya kawai.
Nace”Baba dan Allah kiyi hakuri ki barni na dan kara lokaci anan walhy bazan dade ba zan tafi…
Bata kula ni ba ta shiga zabga kira cikin gida dan dama daga gefen zauren su muke
“Dan asabe ,kai dan asabe… Maza kawo min dorinanan nan yar fiskan wa kawai
Jin haka ya sa Tuni Na matsa gefe a tsorace
Ido na suna neman cikowa da ruwa amma sam naki tafiya na tsaya ko zata tausaya min
“aniyar ki ta biki saratu tirrrrr da irin hali naki..wai ace mace kamar ki da girman ta sai tabi ta gallabe mutane da rakube rakube a gida kamar kyanwa,..saratu anya ba wani abu kike boyewa ba kuwa?”
“A’a, baba laure walhy babu komai ni bana boye miki komai ..kawai na idan gaji ne daga makaranta sai na kan huta anan kafin umma ta dawo sai naje gida.
Harara ta watsa min tace”Da Allah yi min shiru yo mani zaki yi ma shariah saratu? kai ungo naki ta zungure ni da karfi…”surfe kuke yi ko nika a makarantar da zakice min kin gaji kina hutawa?,ta daura hannu a kugu tana bina da mugayen harara cikin masifn ta kuma cewa
“hmm toh waye ma bai gano ki ba a kauyen nan yanzu..
Ke fa tun da ubanki malam bukar ya rasu kika soma neman hanyar tozarta uwarki gambo”
“Kai amma albasa batayi hannun ruwa ba sam. gambo dai ita ce ta soma aure acikin matan marigayi malam bukar duk don ta kare mutuncin kanta da naki amma gaki nan kina yawon jawo mata masifa a gari ai ena ji sarai a makwabta jiya a na cewa har kwana kin tabayi a zauren gidan su bintu diyar malam buba.
A take na sunkuyar da kai na kasa.
“to bari kiji saratu .. nikam dai nafi karfin ki ba dani ba sai ki canza lale.
Kuma kinsan Allah? kawancen ki da yata hansatau ma yau din nan na soke shi ,Bafa zanje wanjen gambo kai kara ba, wannan karon har wajen kawun naki dan goggoji zanje na kai ki,wallhhy in baki fita a tsabga ta ba zaki san kuwa kin tsukano tsuliyan dodo.. maza zo ki fice ayi gaba chan Allah ya tura keya.
“har yanzu Kaina a kasa yake bance komai ba Hawaye na sun taru suna son su sauko kasa amma na hana su, cikin taushin murya mai ban tausayi nace.
Ayi hakuri dai baba laure Allah ya huci zuciyar ki duk abunda kika ce naji
Insha Allah…
dakata.. Ta katse ni azafafe yi waje!!
Ban motsa ba “ta dan tura ni da karfi, A sanyaye na kalle ta kalar tausayi na juya na gyara jelar makaranta na na soma tafiya akan layi
Tsaki mai kauri ta watsa daga nesa enaji tana kan zagi na
Gabanin magrib ne don haka waje ya soma rufewa da duhu
Tunanin me zanje na tarar a dakin umma ya sa ni fashewa da cun kusashen Kukan takaici
“Shekara na goma sha hudu ne kacal a lokacin nika dai umma na ta haifa
A yanzu ena aji na biyu a makarantar gaba da primary a nan bayan tashan kurwala
Yau kuma rasuwar baba na malam bukar wata goma sha uku kenan cas..
Baba ya bar mata uku mama na ne amarya
Ina da yayu biyu maza yaya hamza da yaya mati da yayu mata manya guda shida guda huda daga cikin su duk an aurar da su bisa al’adan mu na fulani tun suna shekaru 11,12 13 yanzu saura laraba ne da lami yan shekara 12 suma duk an sa ranar bikin su
Gida daya muke har Yanzu da yan uwa na da kishiyoyin mama na’
“kawu babaji ne,bayan ya auri ummah na ya ba ta izinin ta zauna tare dani a kan daki na na gado don baba na baida dukiya sosai dama makeri ne abakin kasuwan garin mu
daki daya na samu a gadon sa daya barma na kuma shine wanda mahaifiya ta take ciki yanzu
“makarantan boko da na keyi har yanzu shine Babban wutar fitinan dake cin ummah a gidan mu .
Don kowa ya zuba mana ido ne yana jira yaga madakatan tarbiya na
Umma ita kadai tace bazan yi auren wuri ba sai nayi karatun bature tun baba na raye.
Tun Bayan auren ummah da kawu babaji nake cikin fitina da tashin hankali.
Don kuwa nika dai nasan mummunan halin da nake ciki a hannun kawu babaji wato wanda ya maye dakin mahaifiya ta a yanzu.
dan iska ne maci amana azzalumi..gashi mugun gaske ne don ko ni nan ena matukar tsoron sa
Kawu babaji irin kasurkurmin jahilin dattajo ne masu sa ido da kahun zuqa ma kowa musamman yan mata da samari..
kai kawu bai bar kowa ba wajen tada zanne tsaye tsegumi da hade haden magana a gari..
Amma dai yana da rufin asiri manomi ne kuma Shima yana da mata biyu sai dai suna chan gidan sa a bayan layi enda ya kafa babban majalisan gulma da bare deden sirrin mutane,
Yanzu haka Bana ganin sa sosai
Don sai ranakun kwanan sa da ummah yake zuwa dakin mu
Tunda na cika sha uku dama yayi mummunan samin ido,amma yanzu daya auro ummu na wani abu daban nake ganewa tattare da shi
wato a duk lokacin da nayi laifi idan zai buge ni sai ya rika cahkumo min nonuwa na yana hayagi da jiki na a nasa yana mammatse ni cikin wani irin kokuwan da bana gane kansa,.don ko na tsaya waje guda ya bige nin baya bari na sai ya rika jana yana fizgo ni jikin azzakarin sa wanda ban taba jin ya kwanta lumui ba in yana duka nan .
Shiyasa duk randa zai zo kwana gidan mu kwana da umma sai na dau lokaci a wani wajen sosai in na fakanci anyi bacci sai na zo gida na kwanta a soro baki alekum
Na dan dauki lokaci ina haka ba wanda ya sani.. Badon ma korafin mutane ba da Umma na bazata san ena zuwa gidajen kawaye na ena rakubewa don naja lokaci ba
Ummah Tayi fadan tayi fushin amma babu mafita waje na don sam na Kasa samun sauki kuma tsoron abun da zaije ya dawo ya hana ni kawo wannan maganan wa ummah.
gashi sam bana so na hada ta fada da sauran matan gidan don ba sa kaunar ta tun da ma bare yanzu data riga su aure.
shiyasa ban taba gaya mata sukan kore ni a Wulakan ce daga dakunan yayan su da daddare ba,yanzu duk tunanin ta idan baba babaji yazo mata,ni ina chan tare da sauran yan uwa ina kwana.
“Allah sa ummah na ta dawo”.na fada tare da sauke Ajiyan zuciya na shige cikin babban gidan namu
Banyi magana ma kowa ba na isa shashin namu
a gefe na ajiye jakata na shiga bayi ganin babu kowa ya sa na dauro alwala kawai na shiga sallahn magribh.
Zan iya cewa Bani da ilimin addini dan Ban wani iya nagartacen sallah ba sabida islamiya daya ne damu a garin mu wato islamiyan zauren malam shehu.
Anan kuma daga karatun sallah ba abunda ake tsinta amma naso ace nayi karatun addini sosai saboda baba na yana da ilimin addini dai dai kwarkwado shiyasa nakan ce tarbiyan sa daban take da kowa.
Ina zaune har wajen isha ba wanda ya shigo abun ya bani mamaki
Riga na da zani na kwama na dan hingine akan tabarma a dakin ummah ena tunanin rayuwa.
Assalam Alaikum
Dum kirji na ya buga na leko mukayi ido hudu da aziza yar makwabtar mu
“Waslm ya dai aziza?
“Uhmmm Yawwa Addayo dama wai ana
Kiran ki ne a waje
Nace Ni kuma aziza Waye wannan din ?.
Tace “Sageer ne mai shagon askin hayin nan.. ta washe baki zatayi dariya..
Na ce”Shhhhhh ke da Allah yi magana a hankali mana na dan leko gefe da gefe ena lura.
Nace”Jeki kice bazan zo ba yayi maza ya tafi
“”Ah ‘ahhhh amma amma Adda..adda… yoo
Cikin bude ido nace “ki wuce kawai kiyi abunda nace miki aziza bana son wani bayani