SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Kuka ummah ta fashe da shi tana wayyo Allahn ta ta shiga uuku
..su anty sahura ne da alhj shayal suka yo kaina
Aka debe ni ruwa ruwa zuwa asibiti..
Ban motsa ba har sai da aka samin ledan ruwan guda biyu sannan na soma dawowa hnkalin na ,wani irin ciwon kai nake ji mai dauke da cunkushe war tunani
Lumsasshun idanuna ke juyi a hankali ina kallon su sunyii cirko cirko musamman ummah dake ruwan hawayen har yanzu…
Na lumshe ido ina jin su anty sahura suna min sannu sannu ita da alhj shayal amma sam ummh ta kasa zuwa kusa dani…
Har aka sallame ni muka koma gidan mu,…
Tun daga mota nake kuka ban sake kallon ko daya daga cikin su..
sabida haka ba wanda ya iya tankawa har muka sauka
Daki na na wuce na fada kan gado na shiga kuka mai dauke da rudani. ..
Daga palour ina ji ummah ke ce musu kar ku daga hankalin ku ni zan mata magana ni kadai…
Alhj yace mata are you sure? Cikin dauriya ta gyada kai..anty sahura tace to mu zamu jira ki anan…
Daga nan ummh ta zo ta same ni ..
Gefe da ni ta dan zauna daf ban ma sani ba ta miko hannu a sanyaye
Ta shafo suman kai na da bari a bude….shiru na dan yi ina jan Zuciya daga bisani na dada nitsar da kaina cikin pilow alaman bana bukatar jin wani maganan ta,
sai naji tace saratu” ki yafe ni saratu.
Saratu kar ki guje ni, ni mahaifiyar ki ce baxan taba yin abunda zai cutar dake ba a duniya ina kaunar ki saratu…
muryan ummah ya sauya sosai dan ni kaina jin maganan nata nake a chan kasan kwakwalta da hayoyon jini na…
hankali na ya tashi
Amma haka Na daure na mike na zauna idanun wa mu duk sun kada sunyi jajir…na dube ummah da muryan fushi nace haba ummah,anya ummh tace kuwa ke ?ummah meyasa zaKi saka kanki a wannan mummunan kazamar hanyar?ban taba tunanin zaki aikata hakan ba ummah shin me zakice ma Allah,a kauyen mu idan suka ji kina haka ai kowa sai yace haka dama halin ki yake na gaskiya ummah meyasa kika yi haka…? Na dan fashe da kuKa.
Tayi shiru ba tace komai ba,tana sobbing a hankali tana jan hanci..
Tace kina da gaskiyan ki saratu komai ma zaki iya tambaya ta kuma duk wanda yaji nayi hakan zai sha mamaki
amma ki sani bazan taba yin wani abu haka kawai ba indan kaina ne har abada na hakura da duniya sai dan dan ke sarah,ke kadai ce madubi na bana son kiyi rayuwa irin nawa,tace saratu ki saurare ni na nema miki rayuwa mai kyau nan da satu biyu zaki bar kasan nan ki soma rayuwa mai kyau ki cuika burukan ki da alkwarin mu,ta kamo hannu na cikin jimami tace ina zaki cigaba ma mahaifiyar ki biyyaya?
Na yi shiru, ina binta da kallo,ni dai sam sam na kejin na tsani komai i cant believe that ummah ta dawo dai dai da karuwai sabida ni…haka kawai nake jin bakin ciki sai na gwammaci gwara na mutu da wahala da na sata cikin wani hali..
da karfi na fincike hannu na na mike tsaye cikin dacin rai da masifa nace ba wani biyayyr da zan miki ummah muddin baki bar wannan sana’ar ba, natsane shi,bai dace da ke ba..kuma bazan taba sake karban wani abu daga gare ki muddin baki bar shi ba ayau din nan…makaratar da burin duk na yafe su..
Nan Ta mike ta kamo ni zatayi magana na shiga firgici ina magana a zuciye nace sam mu bar kayan nan anan da duk abunda ta mallaka mu koma wani wajen na hakura da rayuwa mai kyau din..muddin sai ta dawo haka kafin na same shi…
Duk iya yadda ta so tayi controling dina haka naki na turje sai maganganu nake ina borewa wanda yasa anty sahura da alhj shatal shigowa..
Kaya na ne a kasa ina kwasowa ummah na maidawa acewa na zan dauki dan tsumman da muka zo da shi, na bar mata gidan ta..
Ranar Na sa ummah kuka sosai hankalin ta yayi mugun tashi..
Karshe sai da anty sahura ta wanka min mari sannan na dawo hankali na na yi shiru,
Ita ta fara bani labarin asalin abunda ya faru da ummah tun ranar da akayi raping dinta a hotel don abata kudin jinya na kar na mutu,da duk wani abun da suka faru strip club haduwar ummah da alhj shayal kaf ta rero su tsaf bata boye min komai ba…
Tace min bani da hankali ashe? Tace toh nine silar sa ma uhmman ki ra’ayin fitar dake daga wannan bakar rayuwa sai ki kashe ni saratu, Waya gaya miki haka rayuwan take tafiya?
Wato kin gwammaci irin rayuwar da zai kaiki ga halaka da bakin ciki ya kashe uwar ki than wanda ummahn ki ta dage ta sa kanta akai bada son ranta ba don ta tsiratar da ke?
A lokacin na dada da sumewar tsaye ina kallon ummah..
Wani irin halin bakin tausayi da razana na shiga
A sulale na koma na zauna kan gado na kife kai na in kuka mai zafi..
Haka kawai naji ina ma nasan abun haka ne tun farko da na mutu kawai na barta ta huta ma rayuwan ta,
Ganin nayi sanyi na kuma shiga wani hali ya sa alhj shayal ya kamo hannu na ya fitar da ni daga dakin ya bar su su biyun.
Shi ya zaunar dani ya shiga rarrashi na sosai yana bani hakuri da kalamai masu ratsa zuciya da sa tausayi sosai
Sai yau nake sanin duk abunda ke gudana daga
Tushen sa…
Duniya gaba daya naji tayi min zafi sosai..
Dan zaman da mukayi da shi ya bani shawaran naje na rarrashi mahaifiya ta din kuwa ta bar wannan hanyar da nake tunani yanzu burin su duk ya koma kaina ne sannan na dauka wannan shine asalin qaddara rawuyar mu.. Na mance da komai.
Na amsa shi tare da basa tabbacin zanyi hakan
bayan tafiyar su da anty sahura
Ni da ummah ne a gidan,
Gaba daya sai ina jin Nauyin naje na same ta da maganan haka itama ta ke dawainiya da fargaban haduwa da ni..
Sai da nayi bacci na tashi chan dare naje daki na same ta,
Anan nake fitar da abubuwan dake raina na tausayin ta da bakin cikin abubuwan da suka faru da ita..
Magana mukayi mai nauyi mai cike da Donkin fahinta da manyan manyar alkwari masu karfin gaske. . .
A wannan daren ummah ta ke sanar dani cewavta bar wannan harkan har abada kenan tunda yanzu tana da abunyi mallakan kanta,nika dai ce agaban ta yanzu
Nima nace,nayi mata alkwarin share mata hawayen ta kuma insha Allahu zan cika mana burin mu,zan yu kokori naga na goge mata mummunan kaddarar data gina mu akai da alkhairin da nake shirin yadawa ma al’ummah anan gaba..
nayi ma ummah alkwarin a duk inda mace ko wani marar galihu kwantankacin irin namu ke neman hakkin sa ni zan kare masa
Shi a ko ina yake,
Ummah ta sa min albarka,ta kuma ce min wannan shine bakar gaddarar mu da ya zama mana bakar siiriin da dole mu binne sa ,wani bazai sake jin wannan maganan ba.
Tace”Daga yau zamu dauki matakin gyara rayuwar mu da kanmu tunda ba abunda muka rasa…
Ta kuma ja min kunne akan na dauki sahura da alhj shayal abmatsayin yan uwan mu dun ta tabbatar min yanzu haka babu komi aransu game damu sai fatan alkahiri da samun cigaba….
Haka, har aka kira asubahi muna zaune muna tataunawa..
Washe gari da muka kimtsa nan ne ta ke nuna min komai na makaranta na,
Zanje karatu a france,
Cikin makarantar da yafi kowanne tsada a kasar ta bangaren ilimin fasaha dan adam sabida na samu kwararen ilimi da basiran sarrafa rayuwa ta cikin sauki …
Haka rayuwan mu ta kasance.
Na dawo tamkar kwai a tsakanin su su ukun..
Anty sahura kullum tana dada kara min karfin gwiwa akan na kyautata ma ummah kar na taba mance wa da ita a rayuwa..
Shi alhj shayal ba abunda yake so na sa araina illah abubuwan dake gaba na da zan fuskanta na karatu.
so duk wani stratergies da sarkakkiya na shige shige da dogaro dakai ya bayyana min su…
Musamman yadda Ya lura ilimi na kyauta ne daga Allah ,bana daukar lokaci nake gane abu uwa masu dumbin yawa kusan komai akace min nakan sa akaina nayi shi akan kari hr sai na samu gamsuwa..