SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Da haka ya dada cusa min Ra’ayin sarrafa basira na ta hanyoyi daban daban. Har ya hada ni da wani computer engineer a russia akan idan naje zamu na comunicating zai na nuna min abubuwan daya kamata ta internat…
Alhj shayal ne ya soma tafiya abunsa ya mana bankwana
Sannan muka koma sabon gidan mu daya bamu kyauta mai shegen kyau .
Yanzu haka ummah na ne kawai zata zauna gidan..
Ranar da na tafi karatu ranar anty sahura itama ta je garin su wajen iyayen ta,
Munsha kuka kam amma da hakan muka rabu kowa ya sa niyyar abunda ke gaban sa
Yanzu ummah Ta fara tunanin fara aikin ta a matsayin managing director na gidan kaji da gidan gonan t duk dama alhj shyal ya tabbatar mata da cewa bata bukatar sai ta je makaranta muddin tana da fasahar rike sana’a da tatttali komai zai tafi mata dai dai tunda ga maiakatan ya ajiye mata su kuma akwai kayan Aikin zamani..
Rayuwar ta take a tsaftace kuma a saukake Hatta ssa danjuma baisan da hakan ba,
Sai dai tunda anty sahura ta tafi ummah bata sake jin duriyar ta,
Tun tana damuwa har ta dawo ta rusuna ta na binta da addua o…
Nikam dama baifi sau daya muke waya a sati guda ba.din abubiwan danaje na tara achan ya banbanta da wanda na ke gani anan…
BAYAN SHEKARA BIYU
… Yanzu haka shekara na 19yr dai dai kuma ina aji biyu a higher institution din mu,..
“anan din off classes nayi na wata shida ina koyan abubuwan da na yi missing sosai don na kamo standard din tsarin ilimin su,kuma sai da na kammala kafin nafara attending karatu na na gaba da secondryn a sir marknickels college france one of the most expensive,indurious and ambitous schl a kasar baki daya.
A zangon farko Abubuwa dayawa sun faru dani, sabida na je ne da zuciyan yin abunda ya kawo ni don haka bani da aboki ko abokiya kuma ban daura makaina shiga hidiman kowa ba,..
hasali ma da kyar na saba da abubuwa dayawa anan.
‘Saukin da na samu shine
Bamu da yawa a duk ilahirin makaranta ba zamu fi 400 ba all over the world, Don kuwa duk wanda yake makarantar baya zama fayau nikaina a lokaci kalilan na fahince cewa duka students din makaranta ma gaba dayan su miskilai ne kowa kansa yake gani kuma yake ji
social events din is very rare a haka shi din ma akanyi organising dinsa ne in a very educative way “dalilin haka ya dada sa ni sosai na kara shiga hankali na dan dole na na waye na san me ake kira kama kai, jan aji rike mutunci da tsare harshe daga yawan surutu,
A lokacin Komai ilimi da basira na nake sawa na koya,thy all belive that dan talaka bazai taba zuwa nan ba.
“Sir marknickel waje ne wanda ake amfani da basiran dalibai ake nuna musu yadda zasu sarrafa shi ta hanyar basu daman shiga harkokin daya shafi career su da dama a kafafan harkoki na duniya…!
“Karatun littafi dana na’urar computer da nayi akallah bai fi na shekara guda ba,a shekara na biyu na fara shiga salon tsarin makarantar kamar yarda suka tana dar
i wanted to be an influential industrialiast and a philantropist..
ma’ana zanyi harkan kasuwan ci na business mai hade da tallafin kulawa da dan adam…
Anan Malaman mu kamar iyayen mu haka suke wajen bamu muhimmaci da shawari na gari basu taba nuna maka gazawar ka karara sai dai su baka constructive critism ta inda zaka kara samun karfin gwiwan akan abunda ka sa agaba.
_wani dogon ajiyan zuciya tayi sannan ta dago ta kalle sobby eyes din sa,dake shake da nauyin zuciya, rudani da tausayin ta kusan Na tsawon minti 5 sannan ta dauke kai ta cigaba kamar ba ta san tana yi ba”_
Tace”Nima anan na hadu da kai _mr MAHFUD LINGARD_
“he’s my true hero and a role model,shi ba dalibi bane amma anan makarantar ya gama last few years,
He’s now humanatarian ba sa’a na bane,don a tsaye zai bani shekara akalla shekara 8 ko 9 na haihuwa i think he’s 27years old now amma ya kai duk matsayin da nake so naje a rayuwa ta..
Duk da Yanayin rayuwata ya sa na dan banbanta da sauran mata wajen sa kai da jajircewa gashi bana kula kuwa sosai amma shikam sosai nake jin kaunar sa Har cikin raina.. i don’t mean love na soyyayya kawai burge ni yake yi sosai.
A zahirin gaskiya idan na dube sa sai na rika gani kamar future na ne yake displaying a hidimonin sa, don duk yadda nakai ga son taimakawa jama’a araina ya wuce nan, sannan yana da kudi sosai baya kuma da girman kai sai dai kamar ajinin mu ne miskilan ci da ni da shi we r almost the same in this aspect…..
Na dai ji anacewa mahaifin sa sa wani babban craft scientist ne wanda yake aiki da world class team wato kungiyar scientist na duniya mai taken NASA,come to think of it mahfud Lingard is every woman’s dream,very gentle, he’s tall
Healthy looking and a very sexy charming prince…
Duk da ma bana sa kaina akan hakan amma nasan dole ne duk wanda ya dube sa yace ya hadu
Cos He’s no different from a perfect world class model.
Ni dai tun Lokacin da na fara ganin sa nake kokarin bin tsarin sa a dabaran ce musamman a duk lokacin da ya zo mana presentation a humanatarian lecture hall …
da shike fannin sa nima nake idan aka dawo layin career ta na philantropist
Yanzu haka kamar ma shine assistant official na kungiyar ilimin taimakan alumma da bada tallafi gaba daya..
Nakan bada hankali a ko yaushe wajen jin labarin sa da misalin sa dan wani bin har sai ya sa mu kuka musamman iri na da muke da boyyyaen ciwo a zukatan mu..
Ranar da na zo daliba na farko a competition dana kare wani muhawwara tsakanin mu da gwarzayen dakarun makarantar sound philantropist a america ranar ne muka dawo abokai da ni da shi.
Sabida ya tsaya min a lokacin da nake yi sosai,sannan yaba da duk himman da nake sawa wajen kare client dina
Sosai ya fahimci abubuwa dayawa a tattare da kalmomi da zuciya na wanda ni kaina bansan ina fitar wa ba…
Kullewar abokan takan mu bai dauki lokaci ba sabida nima ina yin sa sosai, i just take that as an opurtunity..
Daga nan kuma sai ya bude min hanya yana dada sa ni jagoranci a kan competiton daban daban a kasashe a duniya yana dada fitar da danyen basira na da hazaka ta…
wani bin idan abubuwan suka mana yawa har nakan manta da gida da kowa ma sai mr MAHFUD..
I become so attached to his ways..soo talented ta kowani fanni har da wajen bani shawarwari
Don ko da na kawo masa maganan career ta na industrialiast shi ya bude min hanyar da na samu shiga young business woman class a online daga kasar germany,
registration da duk wani hayaniyar programes din duk shi ya min..you can imagine how generous he is.
A haka Kafin na kai aji uku na saba da duk wani wahalan shige da fice
Da taimakon best friend dina mr mahfud na dada zamowa jajirtacciya abun kwatan ce cikin dalibai..
Ina aji na hudu na mallake share a companyn sarrafa wheels a japan
So mukan je a lokaci lokaci tare da shi muna harkokin mu.
Yanzu ina namen shekaru na 4 kenan a france ban taba zuwa nigeria ba.
“Ummah ne ta ke zuwa a duk lokacin data samu sarari ta duba ni..
ita kanta tasha mamakin yadda na dauki rayuwa anan da muhimmanci
Da kuma manyan abubuwan dana sa agaba na na cigaba take
gashi jinin su ya hadu da mahfud kamar yadda nawa ya hadu da shi sosai..
Yanzu haka shi nake kira hero shima yana ce min heroine…. _anan ma tayi murmushi kafin ta cigaba_