HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

“Babu sallama sai buuut mu kaji mutum akan mu

“in….a i…n…a wuni baba babaji’”sum sum aziza ta tafada a rakube tana do tabi gefen sa zata wuce waje don tsoro muryan ta har na rawa

nima firgit na mike kirji na na bugu .nace sannu da shigowa baba

Ya wani daka tsawa
Ke aziza!! Zo nan

Kuka ta soma yi don karama ce yar shekara 9

ya jawo ta Zafff ya wanka mata tafi a kafadan ta..zatayi kuka yace” yimin shiru Munafuka,bana hanaku shigowa lungun nan ba? Wato kune iyalan kai gulma waje ko..yanzun
Me kika zo yi anan

“tsut ta kame bakin ta dake bari tana jimami “Uhmmm uhmmm baba ,dama na zo gayan aika ne.

“eh ..ehh baba kayi hakuri aika ta zo

Yace “Aika? wajen wa kenan.

Ya juya ya tsula mana razanananun idanun sa

Tace” Dama goggo rabi ne tace addayo ta zo ta debe kwanukan ummah..

Nasha mamakin karyan da aziza ta yi yanzun sai na sake baki ena kallon ta
na kasa cewa komai

“kuka ta fashe da shi tana bashi hakuri..daga bisani yace wuce ki bani waje

da gudu ta fincike tayi waje. sai binta da ido nake bayan ko sake kallo na batayi ba..

harara ya watsa min sannan ya shiga ciki

bance uffan ba sabida komai ajere na bari daga abun da nasan zai ce yana bukata na miko masa .

tsaki ya ja bayan ya ga hakan.

kenan baida dalilin da zaisa nayi masa wani kwakkaran aiki bare ya sake samun daman gaya min maganganun batsa dana cin zarafi kamar yadda ya saba.

Ina ganin ya zauna yana waya na sabule nayi waje din nasan zama ni da shi inuwa daya ba alheri bane tunda aziza tayi min hanya sai na bari akan shine makara ta

Fita na ke da wuya Ashe ranshi yayi mugun baci dana fuce din ,a ganin sa ya samu wani damar baza min halin sa tunda umma bata dawo ba tukun.

Ko cin abinci baiyi ba ya rufe ya biyo baya na

Cikin rashin sa’a kuwa
Ina fita na ci karo da sageer a bakin kofar gida
tsayawa nayi ena rokon sa ya tafi don kirjina har bugu yake min kar baba babaji ya fito ya riske ni da shi a tsaye.

Mun kai kusan minti 10 muna sa’in san magana amma da kyar sageer ya amince ya tafi a dole wai shi da gaske yake zai aure ni..

Bayan tafiyar sa Juyawa da zanyi sai cahraf muka hada ido da baba babaji gani nayi yana leko bayan sageer daya kusa lumewa daga lungun gidan mu..
na sunkuyar da kai na kirji na na bugu wani irin mugun kallo yamin ya kada kai ya wuce abunsa

ni kuwa ganin baice komai ba ya sa na bari a hala baiga komai bane sai na sullebe na shiga gida.

Akan hanyar sa Dariyar mugun ta yayi sosai har cikin ransa yace ” yarinya kenan,ai dama yaro yaro ne,ni babaji bazan taba rainon dan damisa na bar ma na dawa ba wannan karya ne..

Dama chan ena ta farautar sarahtu Amma daga yau ena ga komai ya kare

Wannan ai Sageer ne dan gidan halliru mai nama hmm”dan gidan wanda nake bi bashin filin gona ta daya gina gidan sa ya kasa biya na dan jaraban talauci..kayyah!!!
…ya karashe da wani shu’umin murmushi

Nikuwa Hankali na kwance na zauna a daki,
Sai wajen 8 saura suka kuma shigowa da umma na

A ladabce na sake gaida su
Na kimtsa ma ummah kayan sana’ar ta don dama masa take siyar wa a babban kasuwar kan tudu itake da babban rumfa don ummah na akwai azama da hikima irin na matar karkara.

Hiran su suke yi irin wanda na tsana don sosai kawu babaji yake soka ma umma maganan banza kuma bata isa ta rama ba..

wani bin har yakan ce mata yar bariki goyon farar hula wato karuwa kenan

Umma na bata da hayaniya sabida bata da ilimin komai amma a ladabce take mayar masa da suka in abun ya ishe ta….

abu daya ke bani haushi yadda yake saurin wasa da hankalin ta ta wajen juya magana..

in har yace abu kaza ne bata isa tayi musu da shi ba yafi so ma tabi bayan sa ko kuma tayi shiru kawai

Duk randa ta haura ko akan gaskiyar ta ne sai ya soma dukan ta yana zagin ta ta uwa ta uba,umma na kuwa tunda akayi hakan sau biyu sai ta dena bashi daman haka kwata kwata duk abunda yace yanzu sai dai ta hau kai itama ta dada zuga shi ba don son ranta ba.

Ni kaina nan na sha deban jibga a hannun sa akan samarin dake biyo ni kofar gida

a hakan ma wata rana na san karya yake min amma ban isa na tanka ba haka zasu min lisss
sai dai daga baya umma tabani hakuri

Suna na zaune Wayar sa yayi kara ya dauka

Yace”Wai yaya ne kam zulai?
dan shiru yayi daga bisani ya kwaroro salati
Yace”Hmmmm duniya kenan tabbas anyi mana rashi kai kai kai bari to zan neme ki kawai…

Ai Wannnan maganan ma ku barshi haka zan zo da kaina ma gobe
Yana kaiwa nan ya katse wayar yana jimami,.

Ummah tace “Me gida lpya kuwa…?

bari kawai gambo..ya ya mutsa fuskan kalar jimami yace”ai zama bata kama ki ba Gobe zaki je chan dindima inna wuro ne ta rasu yau din nan da dare.

“Innalihhi wa inna ilaihi rajiun,. Allah ya ji kan innna.. Allah ya sa ta huta amma babaji ciwo tayi ne haka?Sai naga kamar jiya jiyan nan yafendo ta gaya min inna wuro garau take tana ma filin roron gyada.

Ni dai ina daga gefe ta bakin kofa Ina shiru uffan bance ba

“nan baba ya hatsala”Ke da Allah rufe mun baki gambo,da
Cahn mutuwar sai ya zaba wanda zai dauka ne? bana son shashanci da neman tsugudidi fa”

Ummah ta tabe baki tace “ahhhhh toh Allah ya baka hakuri
Mai gida Nace ba?
Goben da su zulai kenan Za muje ko?

“ban sani ba ..ya mike a fusace kamar zai mare ta
wanda hakan ya sani sulalewa chan nesa da bakin kofar kadan na rakube.

Ke kadai nace zaki je, da daban aure ki ba ai su nake turawa..wai nikam rashin kunya zakimin ne gambo?

Uhmm uhmmm..umma tace kamar bata damu ba

Tace Allah ya kaimu goben..daga nan taja bakin ta tayi shiru

Shiru ne ya ratsa wajen ban sake jin motsin su ba..
nima bacci ne yayi nasaran dauka na a gefen bakin kofar ban sani ba

gurnani da sambaton baba babaji ya sa na firgita. cikin sanda da tsananin kunya na mike na kama hanyar soro ba wanda ya sani kamar kullum naje na kwanta kan dakali.

Bayan sallah asubah
Wanke wanke na ke yi ayayin da dai dai kun mutanen gidan mu ke fitowa .

Yanzu kam babu wanda yake kulani sosai a gidan..
su yayu na ma kamar tsine min sukayi ..ai idan mace takai haka a gidan uban ta ba aure to karuwa ce”().

“‘yawwwa Gambo ya kamata ki fa hanzarta ki kama hanya maza maza ayi wankan inna dake.
cewar baba babaji.

“toh me gida ummah ta amsa..Nan ta shiga shirin ta tsaf.

Bayan na kammala dumame na rusuna na gaida su” tsaban kallon da baba babaji yake aika min a sace ya sa na kasa cewa komai na daure fuska.

umma duk tana lura da yanayi na amma sam na kasa gaya mata tafiyar tan ne bana so kwata kwata sam hankali na ni bai kwanta ba.

Gashi ya sa ma na ido ko tari umma tayi sai ya amsa”

hakan mukayi rabuwa da kaikayin magana a zucin mu umma ta kama hanyar dindima.

Tun tafiyar ta komai ya sauya Acikin nishadi baba babaji yake, don sosai fuskan sa ya nuna hakan duk dama yana yi yana fuskewa yana shan qamshi..

tunda umma ta tafi ko hutawa banyi ba don tamkar baiwa haka ya maida ni
Yau da safen har wanke masa aswaki da kasar takalmi sai da nayi

“karfe 11 saura ne,sai na dan jinguna kadan ena jiran lokacin makarantar rana yayi,nan naji an kwalla min kira…

gani baba,na shigo na rusuna gaban sa.

je ki bakin kasuwa wajen mai shayi zai baki aika ki kawo min..

Nace toh azuciya naa ina tunani”Tabbb yanzu fa ya ci dumame jibgi guda ko mai zaiyi da aikan mai shayi oho”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button