HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Nan ya kawo wani murmushi mai ciwo
Baice komai ba ya juya Shi ya fice a dakin ya barta anan..

Kuka ne mai karfi ya kaita kasa tanayi har tana jan shesshska..

Cikin ranta bata taba tsammanin son datake yi ma mahfud yayi tsanani ba sai yanzu amma taki sam ta amince da hakan a matsayin sa gani take shakuwa ce kawai.

Sai dai ya zama mata dole ne ta san ko shi waye ne da wannann sirrin na ta,..

Dama ba agane asalin halin mutum sai baka tare da shi…baya tare da kai

Kuka mai dauke da rudani kala kala tayi daga bisani ta mike ta koma suite din ta inda sukayi ban kwana da catherine da sauran mutanen ta
Ta wuce airport.

Cike da tashin hankali take tam amma taki sakewa ta nuna ma kowa sai dube dube take, tunanin ta ko mahfud zai dan leko..

Haka kawai idan tayi wani tunani sai taga kamar shes wrong amma
Kuma dalilin ta na yin hakan sun fi karfi aranta

Yau ko da ace son mahfud din ne a aranta ji take ya zama mata dole ta sadaukar da shi da ace mutumin data yarda da shi fiye da kowa,mijin da zata aura wata rana ya zo ya tona mata asirin ta, sam ba kanta ma take ji ba mahaifiyar ta take tunani don ita kadai tasan yadda ummah ke dawainiyan goge tarihin wannan kuskuren da suka tafka baya da anty sahura akanta.

Har sai da akai kai karshe ana kiran sunan ta a receptionist sannan ta tashi ta tafi wani boyayyen gurbi a bangaren zuciyan tan baiso rashin zuwan mahfud din ba,

Tun da ta shiga jirgin ba abunda take tunani illah yadda zata dena tunanin mahfud tayi abunda ke gaban ta..

Karfe 5 saura dot ta iso nigeria…

Sai dai wannan karon a lagos state ta sauka inda ummahn ta gaya mata ta tsaya.

 

*VOTE FOLLOW @SURAYYAHMS*

 

*OFFICIAL CATTY*[2/23, 23:33] ‪+234 802 646 5734‬: ????: *????BRILLlANT WRITERS ASSO????*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™jan2019
????????
*SAMARIN SHAHO*
????????
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*

_YOUR BIRTHDAY IS OF NO DIFFRERENT TO MINE,we are two living bodies in one soul,i love you to the moon and back#temi tope adeniyi happy birthday to us._

_PAGE 10_

Nazo cikin kasar india a washe garin ranar da za’a bamu cikakken gurbin fafatawa na zaben kwanaye da zasu samu karin girma da daukaka a harkan career su na gaba..

_Dev singhania imperial_ _college of human right and philantropism india_ .

Kasashe bakwai ne muka samu shiga kama daga China,india,south africa,nigeria,usa,bahrain sai mu yan france.Anan duka muka hadu 7 first class students team daga makarantu daban daban wanda suka samu shiga kenan kuma ba bata lokaci aka fara fafatawa..

Wata shida ne kawai so Kowa akan bashi cases na true life events aga iya kaifin basirar sa da hikimar sa.

“abubuwa dayawa sun faru Daga kadan kadan ake disqualifyn teams yanzu haka saura team biyu ne.
France and india.

” anan mahfud yayi ajiyan zuciya mai nauyi duba da lokaci ya tafi sosai,asubahi ya kusa dosu su..sai ya dada kame hannun sarah dake tayi pouse itama sai ta da ta kankame shi da shi don ya gyara musu position din su sarahn tana daga kwance ajikin sa,

Shiru ne ya ratsa wajen sarah bata sake furta komai ba,da shike ma ayayin datake maganan tin daga farko sunyi kukan zuci sosai amma yanzu hawayen ne kawai yayi saura a fuskokin su.

Duk jikin sa yayi tsami kuma ya sace sai ya sa hannu zaii tallafo ta ,kafin yayi wani juyi sai ta dan kwace kadan daga jikin sa tana shirin mikewa tsaye..

Still suprise da yaga tana layi har yanzu amma sai ya daure ya kure ta da ido har ta tsaya da kanta ta harde hannu tana maida masa kallon nitsuwa..

Tace”gashi yau na zo fafatawa na na karshe and i just completed my final rounds today”my hero,ta dan dube mahfud din tace “kasha cemin zan lashe gasar nan,cos u have full confidence in me ko?

Ya gyada kai a hankali

Ta dan tabe baki a takaice Tace
I too feel the same way..nima na yarda da kaina sosai akan haka, na dauka ko zan iya taimako a kowani irin yanayin rayuwar da dan adam zai shiga a duniya..

Na dauka ko kwakwalta da zuciya ta tana shirye da daukar ko wani labarin cin zarafi na rayuwar dan adam….

Kaima ka yarda da hakan Ko?

Kafin ya gyada kai tayi murmushin takaici gami da share hawayen ta da suka dada saukowa”

A hankali ta furta “but i dont think i can handle it anymore,i dont wanna win anymore.i think its over mahfud ive lost my confidence today..
anan ta karashe cikin wani sassanyar kuka mai dauke da raunin zuciya.

Yana shiru tukun but He clearly understand her “yanzu yake fahintar komai wato case din da tayi na karshe na matashiyar budurwa vashika da mahaifiyar ta shi ya sake tuno mata bakar rayuwan da suka binne da ita da ummahn ta”a baya

Shima kukan ne ya kufce masa marar sauti,amma sai ya cije yana share hawayen sa a dabaran ce

Anan ya mike ya karaso daf da ita ya na shirin kamo hannayen ta dake karkawa tare da sautin kukan dake fita.

A nitse Yace”Sarah….cikin hankali ba tare da ya sake magana ba ya shiga jawo ta jikin sa don ya taya ta calming mood din ta,anan sai ta birkice masa cikin kukan dake cinta rai sosai tana cewa no,kar ka ce komai mahfud..nasan bazaka taba cewa bazan iya ba…but believe me im weak,i cant..im helpless now.

Zai sake magana ta dakatar da shi tace”….

“Ka tsaya kaji ni,im just like that girl vashika kaina nake gani a rayuwan ta mahfud,na daure na daure sosai…but everthing its toturturing me…ko haryan zu baka fahimce ni bane..hero, vashika is just like me babu wani banbanci…!

sai dai me ya faru da mahaifiyar tan da tayi tunanin da na so da ace ummah na tayi wajen kare mutuncin ta?she too was raped countlessly on the street,mahfud maza shida suka keta haddin mahaifiyar vashika duk don akan ta na neman taimakon da zata rufa nakan ta asiri batare da ta watsar da kanta ba

But vashika is dead now”Yanzu duk da mutuncin mahaifiyar tan ma ya tabu don ta bata lpya da kariya it all in vain?…ai gwara mu musulmai ne, but them they sufferd alot sabida tsananin al’adan dake zagaye da abubuwan bautar su da kuma dokokin tsarin tarbiyan su…life is soo unfair to them hero.

“vashika ta mutu,she died with her dad’s uncompleted child…irin wahalar dana sha shi ya kashe ta,yanzu maman ta na fama da radadin zuciya irin wanda muka ji dani da ummah na bakar qaddarar rayuwa,ga fama da sabon ubangiji da rugujewar tarbiya,amma kaga ni nata ya dauke mata yar ta ,ita kadai ne yanzu a duniyan nan sai tarin bakin ciki da kunci…
I think her own is even worst.

Tun da na fara case din na nake ganin abubuwan da ummah ta so nagane ada chan amma ban gane ba..

Dazun da muka je wajen gawar vashika Naso na ba mahaifiyar ta tabbacin rayuwar ta zai banbata da yadda take tunani,i wanted to be there for her

But she told me alots of things,abubuwan data gaya min shi ya dada karya min zuciya ta,..

abunda yafi damu na shine tace”da ta san in ta tsaya jayyaya wajen bada kanta wa wani namijin tun farko zai kawo karshen rayuwar vashikan ta da bata bata lokaci ba but tayi jayayyan a farko ta kare mutuncin ta agaba kuma she was raped mercilessly for the same reason,..
it was also a hard time for her kamar yadda ya fada kan ummah na,..now i get it
Shiyasa kawai sai na fara tunanin kaina..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button