SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Abun ya dame ni sosai…
Yau na fara jin ashe bazan iya daga kowani gwiwa ba…she lost all hope
my heart becomes so heavy,inajin zafin abun araina fiye da yadda kake tsammani..
Sai dai bansan nauyin da yayi zai iya hanani sukuni ba,
I lost control over myself mahfud..
catherine ke tare da ni,ina ganin kuma ta tsora ta ne Shiyasa ta bani giya,ai kasan bana sha ko?
Shi dai kallon ta kawai yake tana pouring heart din ta…
jimami take yi ciikin wani shakurarren kuka ta kuma cewa”huhhh amma bansan meya sa na sha ba yau din im sorry…
Kuka ne mai karfi ya kufce mata wanda yayi kokarin kaita kasa cikin tsumayin sa da rudewar tunani..
This time around mahfud bai bari hawayen sa sun sauko ba, ya kamo ta jikin sa ya dan rungume ta batare da ya fadi wasu kalmomi masu yawa ba ya shiga rarrashin ta yana ce mata its ok..
A lokacin ana neman karfe hudu da minti arbain da biyar na safiya,…
Duk hankalin sa ya gama tashi ya rasa meke masa dadi..
Bayan kamar minti 10 da sassauata kukan nata ya shinfida ta akan gadon ya shige bathrum ya hada mata warm bath…
cikin lallami ya sa ta shige ciki ta kimtsa kanta..
Gaba daya baida gwarin gwiwa,amma hakan ya kaucar da duk wani tunani aran sa ya hada mata warm milk..
Daure da towel ta fito daga wankan kanta ne ke bugawa sosai sabida halin data ke ciki ga azaban gajiya da bacci dake bin jijiyon ta she’s super stressed
Dakan sa ya kamo hannun ta ya zaunar da ita gefen gadon ya dauko milk din yana bata a baki har ta kai karshe
Tun kafin ya kai cup din kan take ta kishingide ta lumshe idanun ta tana maida nunfashi ahankali,
Kallon tausayi ya tsaya binta da shi tsawon minti goma bai motsa ba…
Ko da ya dan yi yunkurin taba ta don ta shi ta suturce kanta a gani yayi ta sake sai ninshari take mai dauke da ajiyan zuciya….
Gwanin tausayi ya shiga shafo gefen fuskan ta”cikin wani yanayi da zai tabbatar maka alkwarin sa da tabbatacen amanar sa a kanta da yau ya kulla azuciyan sa..
Lallai wannan babban ciwo ne a zuciyan ta amma ta zabi ta gaya masa a duk da ma bata cikin hankalin ta…
Tunani yake shin sarah ma tana jin irin abunda yake ji aransa game da ita kenan..? Gani yake kawai don ita akayi shi a duniya duk dama bai taba gaya mata yana kaunar ta ba, sosai kaunar tan ke ratsa hanyoyin jinin sa…
Dama ya taba sawa aransa cewa tabbas rayuwar sarah na baya suke masa katanfmga daga bayyana mata yadda yake kaunar ta kuma yake son ya kasance da ita..
Amma yau komai ya wuce tunda ta sanar da shi mafi munin labarin ta amanan ta qaddarar ta da raunin ta…
Dama shi kam bai boye mata komai game da nashi rayuwan ba duk dama babu dadin ji, amma ta nuna masa iya amanan ta da tausayin ta, ta bashi karfin gwaiwa..he knew he have to do the same now dan ita ma ta bude masa nata..
Toh me ya rage in ba ya gaya mata yana kaunar tan ba,?kallo ya sake bin ta da shi, cikin ransa ya titse yana rokon Allah ya sa sarah ta amince da shi yace” insha Allahu ni zan aure ki i will wipe away all ur sorrows sarah…im here . Ya karashe ahankali yana dada duban kyakywanr fuskan ta.
Sake saken kauna amana da tausayi zuciyan sa ke kan sakawa ayayin da ya gyara mata kwanciyar nata ya rufe ta da soft duvet comforter sa Ya juya ya shiga bayi..
Wanka yayi shima ya sauke nauyin dake dawainiya da zuciyan sa…
Kafin nan biyar ya buga ana shirye shiryen kiran sallahr asubah.
Sai ya dakata yayi sallahn sa sannan ya kishin gide gefe da ita atake wani gajiyayyen bacci yayi awon gaba da shi..
Bacci mai cike da yanayin ajiyan zuciya suje kwasa dukan su biyu musamman ita sarah da shike yanzu ne giyan ke asalin fita a jikin ta…..juyi take son ranta tana neman juye nauyin zuciyan ta akan baccin.
Sai wajen 7.56am ta bude idanun ta gani tayi haske ya dan fara dokar windown sa da shike upstairs ne kuma windown glassses ne..
Shiru tayi na dan lokaci daga kwancen kamar bata gane inda kanta yake ba tukuna..don sosai kanta ke warwarewa lokaci guda ta soma tunanin abuwan da suka faru jiya…
Bit by bit komai yake dawowa mata wani mummuanan tsoro da fargaba ne ya ziyar ce ta take ganin kamar a mafarki komai ya faru…
daga cikin bargon sai tayi juyi a hankali tana feeling naked bodyn ta dga cikin towel din dake neman karkacewa da kansa anan ta dafe kai cikin rudani ta juyo a dan sace “don ta tabbatar makanta ba tare da namiji yau ta kwana ba …
But where is he? Don ita kadai ce yanzu akan gadon ba kowa
Ko da taga yanayin kwanciyar sun a shatin bedding din She has to closed her eyes tsam tsam sabida wani azabbaben kunyar da ya rufe ta,nan ta daure dai ta shiga duba ko ina da kwayan idanun ta anan ne take ganin alaman kamar wani abu ne ya faru wanda bai kama ta ba..
Har ta fara Kawo tunanin sai kuma rudewan tunanin hade da tashin hankalin tuno da abubuwan da tayi jiyan ya sa ta mike a kan gadon da sauri kamar mai ciwon hauka …
Zuciyan ta har na sama da kasa tsaban ta rikice
MAHFUD!!!!!ta kwalla masa kira amma shiru babu shi,
Da sauri ta Ja curtain din dake jikin window tana duba saba t inda ya saba tsayawa bata gansa…
Cikin rudani ta juyo nan idon ta ya ci karo da wasikar sa akan madubi..
Da dark blur pen ya rubuta”
Zama tayi gefen gado bayan ta dauko
Tafara karantawa a hankali”
_”forgive me..da na jira har sai kin tashi a bacci na fada miki but im helpless.. heroien, nasan zaki iya wannan don kin riga da kinci gasar_
_u won the battle of your destiny, and for this you must win too.. becos your confidence is still with you,abinda ya faru jiya ki dauka ba komai ba ne illah wani qaddarar da_ _rayuwar mu ya zo mana da shi tare dake..idan kin tashi ki shirya kije ki karasa abun da kika fara.i will neva let you back down from this.. A yanzu ne kike da bukatar ki zama abunda kike so a rayuwan ki..yau nasan idan har akwai digon yarda dani azuciyan ki zaki fahimci me nake gaya miki yanzu wanda bazan iya fuskantar ki na fada miki ba_
_go sarah lokaci yayi da zaki zama macen da kike buri,today i feel like im not ur role model but ure my role model._
_Zan jira ki anan sama idan kin karbo abun da ya kasance naki ne ki taho ki same ni,i have a confession to make_ .
_yours Mahfud lingard_
Sauke ajiyan zuciya tayi tayi zugum cikin radadin tunanin yadda ta zubda kan ta ajiyan gaban sa,komai ma cunkushe mata yake dada yi a zuciyan ta da kyar ta lallaba ta shiga bath ta kimtsa kanta sananan ta dauro alwala tayi sallah..
Duk jikin ta a muce yake..musamman idan ta tuno da abubuwan da ummah ta dade tana mata tsoro game da bayyanar siiririn su a wajen wani”musamman namiji,” wa iya zubillah me ya kaini shan giya’tafada makanta cikin zazzafan nadama.
Hawaye ne suka wanke fuskan ta tuntuni ta ma arasa wani tunani daya zata bada hankalin ta kai..
Amanan su da ummhan ta data ci wajen bude sirrin ta jiya ma mahfud.
Ko nadaman shan giyar data yi ta bata kimar ta a idon Sa..
“Koko zata rufe ido ne kawai ta fuskance aBunda mahfud din yake gayawa mata a wasikar sa..
Sam ta kasa sa hankalin ta waje daya..
Ta dan jima a haka daga bisani ta tashi ta shirya ta fuce zuwa masaukin ta..
Da shike bata taba kwana wani waje ba ya sa yau take ji daban da tambayoyin da sauran team mates din ta ke mata..
Amma bata cikin yanayin da zata amsa ma kowa maganan sa musamman cath da ke shakkun abunda ta aikata mata ajiyan.