SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Sai kowa ya dakata ya dube ta …irin whats this woman trying to say here
Shikuwa Cikin son ya dada zafafa plan dinsa yace ,ah a hajiya ban fahimce ki ba fa menayi wanda bai dace ba anan?
i gave evryone his credit,sarah did well ,ao kema kin gani da idon ki kowa abunda yayi nake fada ko ba haka bane…?
Tace i seee,so sarah did well,mmm na dauka ai mutane biyu ne anan suke fafatawa ashe mutum daya ce,
Zai yi magana cikin fushi tace dakata fidelis,na lura da kai son kai kake so ka shigo da shi and i wont allow that,
Ta watsa masa harara mai cike da alaman kalmomin ” nasan ka kasani,kai dan iska ne marar mutunci so idan ma baka jiki akayi kana aiki akai it wont hapen on my doghter…
Tsaf ya karance ta sai shima ya bita da murmushi mai dauke da taken “so what? I will do what i want…
Mutane kuwa suna kallon su ba wanda ya iya motswa wajen bare su gane me suke cewa da idanun su..
Hajiya asamu ne ta juya ta dan dube sarah daga nesa cikin masifa tace” this is WHRA,im repeting myself Duk wanda ya zo da wani mugun halayen sa ma gwara ya bari dan baida mafaka anan kungiyar”a shirye muke da tone asirin sa
Duk wata yar iskan yarinya da zata kawo mana duniyanci anan organisation din zamu fitar da ita we are ppl of respect and dignity….
yadda take maganan da comanding voice yasa kowa ya sha jinin jikin sa akayi mata shiru tana kammalawa tace ma safeenahn muje…
Sosai sarah ta gane da ita ake yi,amma abunda ya dame ta shi ne wannan warning din?
a ganin ta sai dai ace da wata ake yi amma iya sanin ta bata taba tsayawa da wani da sunan wani abu daban ba inba aiki ba..
a office din su, su ya su manyan sai da aka sake shigar da maganan sabida mr fidelis ya gama nuna musu yana tareda sarah 100 percent.
anan har mrs ruth ke gaya masa idan har ta kama shi da wani abu na daban wannan karon ba rufa asiri sai ta sa an tayyara shi a media…
dan wannnan sabanin da suke samu kwana biyu ya fahimce asalin sun tswangame ta ne ba wai kawai dan yarsu ba
Ranar sarah na office sec ta turoo kofa tace mata hajiya asmau na neman ta.
Duk dama tasan nasu baizo daya ba amma haka ta daure ta taho,
Zaune ta same su achan sama sun kame fuskan su babu alaman walwala..
tace salam alaikum can i come in?
Minti 3 sannan aka ce mata yes..
Tama shigowa suka bita da kallon hadarin kaji wanda ya sata sunkuyar da kai kasa..
Ta daure tace you called me maaam
mrs ruth tace straight up to the point meye hadin ki da fidelis?
Abun ya bata mamaki amma sai ta nitsu tace hes my curent whra supevisor maam..
Kallo ta bita da shi irin naji wannan rainin wayo
Hjya asmau ta wurga mata file gaban ta tace take this and read it aloud
Ta sa hannu ta dauka gaban su ta shiga karanta wa
Its a rule and legal actions ma duk wata Humanatarins activist na org din wanda za a wanzar ma duk wanda tayi comiting zina da officials ko aka kama ta da ire iren sexual crime and culprits.
Tun Sarah tana karantawa ranta ya fara baci ,yau ne rana na farko da taji ta kai har wuya wai shin me matan nan suka dauke ni ne?
haka dai ta cije ta kai karshe tana gamawa tace ta gama..
sauke ajiyan numfashi hajiya asmau tayi tace i hope u get tha in to your skull
.
Budan bakin sarah tace i dont understand maam.
Wht did i have to do wirh this?
Sun sha mamaki yadda ta bude ido tayi maganan sun fahimci ta fara gano me suke nufi da hakan ne..
mrs ruth ne ta dubi hajy sai suka danyi wani irin glance mai dauke da kallon raini da wulakanci..
Kinji Wai bata gane ba ko..
Mmm to zaki gane…ta dube sarah tafada mata hakan a tsime.
Sarahn bata sake cewa komai ba..
Hajya asma tace u can leave now
Daurewa tayi tace thanks…
dan hawaye har sun ciko mata tam a idanun ta
so this ppl are thinking that im worthless har da zan yi tunanin bada jiki na wa namiji kana aiki?
oh ya Allah Ko kadan basu daraja tunanin su akaina ba,and i hate when ppl judge me …ta fada cikin ranta tana saukowa daga saman.
daga gefen dayan site din mr fidelis yake ganin saukowar ta aransa ya san ba ayai mata dai dai ba, don yasan idan mrs ruth da hajya asma sun hade waje daya sai a hankali..
Sarahn adaddafe tayi aiki cike da tunanin meyasa yau aka bata sexual legal purnishment personally ta karance…
abun ya sosa mata rai sosai…ta tsani abunda zai taba mutuncin ta..
sai wajen 6.0pm ta samu fitowa as usual ita ta raka hapsy waje suna tafiya tana tambayar ta wai shin meke damun ki me yau sarah.
A kasale tace babu komai hapsy, am just tired
Tayi murmushi tace hmmmmmmmm ok, ai yanzu zamuje gida zaki huta so pls chill ok? Nasan duk don kin gaji damu ne
yadda tafada maganan yasa sarah murmushin dole tana cewa ” hapsy kenan, kin nace sai kin san ko wani abun aka min to shikenan dai we ll tlk about it tomrw..
anan suka rabu hapsy ta shige motar mijin ta juyowa da zatayi suka ci karo da mr fidelis a gaban ta..
Da kyar ta kwakwalo murmushi tace good eveniing sir,
Bai amsa ba ya mayar mata da murmushi…
yace sarah bukar,ina zaki je haka?
Tace im off sir heading home..
Sai ya dada taku kadan yace are sure komai dai dai ?
Asin kin tabbata kowa ya gama duties dinsa na yau ?
cikin mamakin tambayar tace yes sir ai yawancin ma an tafi gida its late..
Yayi shuru daga bisani yace ok
ta gyada kai a ladabce zata bar wajen yace sarah…
Lets have a word in my office now..
wani dum dumm kirjin ta ya buga da har zata ce nooo sai ta kawar da tunanin..
tasa ranta indai har ka kulla gaskiya tsoron me zata ji?
besides he’s only good to her bai kuma taba kawo mata maganan banza ba..
Da wannan tunanin ta ce yes sir …minti 2 bata kara ba ta biyo bayan sa..
Ko zama baiyi ba yace Mata sit down a dan tsakure ta zauna..
Duk sai ya rasa ya zai gaya mata manufar sa da ita..
daga bisani ya dauko laptop ya kawo ta gaban ta so close jikin sa kamar zai goge fuskan ta da jikin ta..
a dan daddafe ta kauce masa ,yana daddanawa daf da daf jikin ta kamar mai shirin zai nuna mata ko koya mata wani abun amma sai taga wani abun da ban yake yi..
Kamar zatayi magana sai tayi shiru dai…
Anan yayi gathering courage yace yay kikayi shiru kuma sarah muyi tadi mana..
Ta dago ta bashi kallon irin what? Kafin ta budi baki tayi magana yace
Me ya faru ne dazu naji asmau da ruth sun kiraki is there anything serious u can tell me ..
…
Ta danyi shiruuu daga bisani tace no sir babu komi
Yasan zata ce hakan yasa yayi murmushi Yace
sarah kina da saurayi ko?
tace no sir…why?
ya dada yiin murmushi nan ya dago ya dube ta yana bata wani lallausan kallo…yace dama nasan babu ruwan ki kekam,amma duk da haka kinsan hatsari ne babba hjy asmau da mrs ruth su sa ma mutum ido…sabida idan suka kama ka da wani laifin sai Ceton Allah..
tana shiru dai tana binsa da ido…
yace amma kinga idan kina da wanda zai tsaya miki a sama ko da nan gaba kinyi wani abu ba wanda zai ci miki mutunci….
Anan tace but sir,idan har bani da laifin komai bana damuwa da opinion din wani i wll just do my job.
impressive yace, yana jin confident voice din nata dake fitar da kalma camly
Yace sarah kenan,ure a principled lady amma am fraid bazaki kai nisan kwana akan career ki ba
Maganan sa sai ya sa ta sake murmushi tace why not?
Yace sabida kina bukatar uban gida kamar ni,wanda zai tsaya miki achan sama,ehen kin gane ko? Ya karashe da wani irin shuumin murmushi