HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

mechanic ne sabida uniform ne ma ajikin sa yayi musu sallama yace yana neman mrss sarah bukar,tace nice..waya baka wannan motar.

yace nima aika kawai aka bani na kawo oga na ne aka bashi aikin gyaran ta tun jiya da daddare ne..
But yace min daga nan yake..

Har hapsy zata fara masa tambayoyi sarahn ta katse da cewa
tohh thanks, ta karbi makullin suka wuce..

suna haurawa sama lokaci guda ta daure fuskan ta,

Hapsy tace meyey hakan sarah ?Ai da kin bari mun tambaye shi Nifa bangane komai ba…

Sarahn tace hapsy ina son nasan waye ya gyara min mota na ne kawai yanzu
kinsan wani abu kuwa i dont trust anyone anymore…

Maganan nata yasa hapsy ta dago ta kalle ta ta san dole akwai wani abu..

Office suka shige inda tasa sarahn ta bata labarin komai da ya auko tsakanin ta da mr fidelis da kuma yazeed ajiyan

Tace kin tabbatar da maganan da nake fada miki na cewa bana bukatar taimakon kowa a rayuwa ta ko hafsat?
i mean ki duba ki gani kowa fuska biyu yake daura ma kansa…

Da kyar na samu na fita a tarkon mr fidelis a saukake wannan kuma kinga shima zai fara draman sa i dont think i wud like it ko da wasa…
a dole zan tsayar masa i dont need his help

Hapsy ta jinjina tayi ajiyan nunfashi tace haka ne sarah dama, sanin halin mutum sai Allah…

But amma yazeed da girman kan san nan? A gaskiya yadda akace baya shiga hidiman mutane yasa nake tantama..

U know what sarah ni dai zan baki shawarar ki fara tuntubar sa kiji ko shine ya kai motar gyara kafin ki yanke hukunci,
Dont be hasty in making decision wannan ba halin ki bane..u need to relax

Ba tace komi ba ta dan jingina da chair,”mahfud ne ya fado mata aranta lokaci guda sai ta shiga mumumman jin bugun zuciya da tsananin kewar sa.

har bata san sanda hapsy ta gaji da surun ta tayi waje ba..

bayan kamar awa 4 ta fito da file a hannun ta zata wuce kicibis sukayi da shi inda suka watsa ma juna kallon Kallon…
Anan ma tare suka furta “sorry”

Sai ta tsinci kanta da kasa tambayar sa duk dama dazin da zafi zafi ta dauki abun…

As usual bai bada kai ba har ya juya zai tafi, tace emmm excuse me?

Ya juya a nitse ya dasa mata killer looks dinsa mai dauke nunfashi..

Ta fuske tace” i mean not to offend bt kaine ka bada mota ta gyara?

wani irin karkace kansa yayi irin what? Me kike cewa..

tace this morning nazo ban ga mota ta awaje ba, kuma nasan kai kadai kasan da abunda ya faru, but a mecahnics brot it back yace wani ya bashi ya gyara from this org….
So pls are you?

cikin rigima da jan aji yayi furzan iskan irin ai shikam ma ya mance da hakan Ya faru sai ya dube ta yace”no,bani bane..

And besides indai jiyan ne ai ba ke da ni kawai bane a building din nan others too….so Plz can you excuse me,

kaiwa nan ya juya yayi gaba ya barta anan tsaye tana binsa da kallon mamaki..

“Ohh mmm yana nufin kenan mr fidelis ya kai min gyara ko me,? msww rainin hankali kar ma kafada mana…nan itama ta juya tayi gaba abin ta..

Haka rayuwa ya kasance kwana biyu sosai abubuwa suka sha kanta..

gashi yanzu boro boro ta ke fuskantar barazana daga hajiya asmau mrs ruth, fiye da yadda safeenahn take bata..

Don tsakanin ta da safeenah sai dai ta gaya mata maganan banza mai shake da kaskanci da barazana wanda bai ya tasiri sabida sarahn bata ba da kai sosai a wannan fannin..

Sosai ta maida Hankalin ta wajen aikin dake gaban ta har ta gama da ofishin mrs fidelis

nan tayi sashin hajiya billy da mr president wato mahaifin yazeed shima ta gama tsaf babu matsala don sune suke dealing da harkan industriliast na business din ta a wannan competition din..

Sai dai anan ta dada gane halayen yazeed da kwarancewar sa don dukkan aikin da za a koya musu da training din da zasu yi putting
Shi ake sa shi ya musu training as a professional business tutor.

duk yadda takai da dauke kai da rashin nuna tana kula da kwarewae sa sai daya ci tura sabida sosai yake playing zuciyar ta cikin hikima inda dan dolen ta zata ji ya burge ta..

Theres no daubt that he is smart and intelligent
Don har wata rana in ta dube shi tana tuno da mahfud din ta,

Iya sace zuciya da kalamai ,Shan qamshi,dauke kai da miskilanci.he claims he does everything out of free will babu wanda yake sa shi yayi ko ya bari..

Ko safeenah moh ma tayi tayi ta rika nuna wa cewa ita ta daban ce awajen sa amma broadly and maturely yake dakatar da ita agaban kowa da kowa…
Musamman gaban idon sarah,..
A cewar sa theres time for evrything dan dolen ta ta nitsu ta dena daukar kanta sarauniya a cikin hall din a duk lokacin dayake musu training

sai yanzu sarah take kawo wa maybe duk wani taimakon da ya mata akan mr fidelis ranar bai dame sa ba kawai yayi ne don ya san darajar dan adam kamar iyayen sa…

A hankali take jin ya burge ta,so professtional streak,He is just the type of man she want amma ko kadan bata kai abun zuciyar ta sabida gudun rainin shi…

Hutun kwana uku aka bayar,daganan aikin ta na karshe zai fada wajen mrs ruth ne sabida itace senior matron na humanatarian and human rights couciL.

kusan matsayi daya suke da hajiya asmau amma fannin philantropist take amma da shike an sha korafin ko dan safeenah yar hajiya asman ne yasa har yau ba asamu wanda ya tsige ta akan competition din ba yasa aka dakatar da ita aka daura mrs ruth akan gaba wannan karon…

Gashi wannan karon kowa na son canji musamman colleques da client din da suka riga suka sa soyayyar su da yardan su akan sarah bukar..

Kowa dai ita take so taci duk dama rashin lura yasa bata san ra’ayin nasu ba.

Yau ne ranar da sarah ta soma zuwa shashin mrs ruth gashi sam bata jin dadi sosai musamman data lura kwana biyu kamar ummah bata jin dadin jikin ta amma sai tana boye mata…

karfe 7.45am na safe tana sauri sauri ta ajiye jakar ta akan desk ta wuce sama tayi report gaban mrs ruth suka ci karo da hapsy

babe? Har in zo zaki wuce tafada tana kwalo ido ma sarahnn..
Murmushin tayi ataikce tace “kefa kinsan inda zanje bana son nayi kuskure bare asamu abun fada…hapsy tayi murmushi tace toh goodluck..ni ina nan..
Suka maida ma juna smiles sarahn ta wuce

Knock tayi amma shiru hakan yasa ta tsaya kusan minti 30 tana zagaye anan amma bata kula ta ba..

Har ta juya da niyyar komawa kasa sai taji taku da motsin mutane nan ta tsaye tana maida kallon ta bakin stairs..

ohhh sai yanzu ma take zuwa ashe ma bakowa office din nake ta knocking,,cikin zuciyar ta ta fada tana duba hadadden feminine watch din ta..

Mrs ruth Tunda ta ganta ta dauke wuta, sai yatsine take tana tahowa cikin kasaita..

Good morning madam ,
mai aikin da ya biyo bayan mrs ruth da jakar ta ya fada ma sarah cikin zumudi da murnan ganin ta

murmushi kawai tayi sannan ta amsa da morning cikin sanyin murya mai dauke da yaba so da kaunar da suke nuna mata

hakan ya matukar bata ma mrs ruth rai, dai dai sarahn tana cewa welcome maam…

bata amsa ba ta juya cikin fushi ta daka ma securityn tsawa…jakae ta ta fauce tace “just get out kun cika raini da tsoma bakin inda ba ce ba…who ask you to talk ?
Yana shirin bada hakuri ta kuma daka masa tsawae
can you pls get out t tana maida musu hararar dukan su ko ajikin ta…

Sarahn was like me kuma wannan yayi gaisuwa fa kawai yyi Ba wani abu ba ….tabe baki tayi tana kallon securiti na sauka tsuliya a zage…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button