SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Nan ta biyo bayan ta cikin office din amma bata shigo ba sai ta tsaya daga door ta sake knocking…
Bata ko kula ta ba ta kuma daure fuska har sai da ta gama duk zagayen ta ta zauna kan chair din ta sannan ta furta
“yes”chan kasan makoshin ta..
wani irin bacin rai ne ya tokare kirjin sarah, don ta tsani wulakanci but yazama mata dole tasan yadda zatayi da wannan mutanen tunda ta riga ta san halayen su akan ta….
Not withsatnding ta shigo ta tsaya,fuska ba yabo ba fallasa tace”heres my report maam
Mrs ruth tayi kamar bata ji ta ba kusan minti 3 sannan ta ja report din ko budewa batayi ba ta ja tsaki, ta jefar gefe” i dont think i have time to waste on this rubbish…
Ki je ki sake dubawa gobe ki kawo min
Out of curiosity sarah ta tari nunfashin Ta da cewa maam ai baki duba ,i need to know where i go wrong so that i can amend easily…
” Easily?to ke me kika sani da zan fada magana kiyi min jayayya…
Ta fada tana mikewa tsaye cikin kasaita” harara ta watsa mata tace toh banga dama ba ne, kije kawai kiyi abunda na saki idan kuma bazaki yi ba shikenan you are on your own,mmmmmm?
Cikin sanyin jiki sarah tace sorry,sorry mamm ba tare da ta sake magana ba ta sa hannu ta dau file din ta fice waje..
tsaki ta ja cikin ranta take cewa i will make sure u fail
anan wajen kam dama kisa aranki baki da matsuguni wawiya kawai..
Haka sarah ta koma da file din office sai dai gaba daya ta kasa gane ina zata kama ba ako duba ba bare tasan ina nedai dai inane ba dai dai ba…
gefe ta ajiye tayi tagumi tana tunani haka dai ta cinye wannan ranar bata aiyana komai ba..
Haka kuma ya cigaba da kasance wa a kullum sai taje office din mrss ruth da safe amma bata taba bude file din ba haka zata sake aiko ta da shi hade da maganganun banza masu cin rai,
Duk tana haka ne don ta bata ma sarahn lokaci har azo hada result ace ta fadi fannin humanatarin sai su bada safeenah points mai karfi..
Abun ma matukar damun sarah gashi yau akalla saura kwana biyar komai ya dage sun riga sunci kwana 9 a banza da ita da mrs ruth..
Hakan ya sa hankalin ta ya dada tashi ta shiga neman mafita reasech da sauran su ba dare ba rana most of the time ko taje gida ma basu samun lokaci da ummah sai da safe…
Yau ma haka ne Lokacin tashi nayi sai ta sai ta dauke ta wuce gida da shi abun ..
It was almost 6.pm yamma amma Gidan shiru bata ga kowa ba,hakan ya sa ta shiga kwalla kiran ummah,ko ina sai chan data sauko ta waje sannan suka ci karo da ummahn sanye da hijabi alamn yanzu ta shigo gidan ma
aabun ya bata mamaki tana dosu ta tace ummah? Dama kin fita ne ai har na tsorata ina ta neman ki
Umma dake fama da zazzabi sosai sai tayi murmushi tace” saratu har kin dawo neh? ai nima baki nayi na raka su nan kasuwa don suga sabon tsarin abincin kajin da na shirya zan shigo da shi…
Murmushi tayi ta dan jingina jikin ummah suka maida ma juna gaisuwan mai shake da so da kauna daga nan suka shige ciki..
Cahn dare suna zaune a dakin ummah sarah Ta dago ta kalle ta tace ummah kwana biyu sai naga kamar kin rame ko bakijin dadi ne
tace ah ah, saratu hakan ma rashin zaman ki sosai ya sa kike ganin haka..nan ta daga kai ta kalle agogo tace gobe baki da aiki ne?
kallo ta dan ummah dashi cikin rashin gamsuwa amma sai ta fuske tace” ina da shi ummah, kawai dama inaso na dan zauna kusa dake ne yau sai naji kamar baki da lpya…
ummah ta mike cikin dauriya tace idan zaki rika damuwa dani haka ashe bazaki fuskanci abunda ke gaban ki ba…
Ni lpyata lau saratu kije kiyi nacci gobe ki samu kije aiki akan lokaci..
Ita dai hankalin ta bai kwanta ba amma tasan halin ummah sosai wajen boye damuwatta tunanin ta ma kar dai bata son ta kula da ita ne ta bar aikin ya sa take biye mata cewa bata jin dadi…
a hakan dai suka yi sallama ta tafi dakin ta ..
Washe gari da safe sai gashi ta zo duba ummah ko motsi bata iyayi bare tayi magana ga jikin ta yayi zafi sosai.
Sosai hankalin ta ya tashi, ta rika cewa ai dama nasan baki da lpya ummah meyasa kike boye min?
a gurguje ta shirya ta sa ummahn amota suka nufi asibiti….
Wanda ya dauke a wajen awa 3 ana duba ummahn..
Lokacin ana neman karfe tkwas da minti hamsin saura a office..
Mrs ruth ne a farfajiyan office din sarah ta tara juniors da maaikatan ta kafff, tana dirin masifa..
Hapsy a tsakiyan wajen tace”maam mahaifiyar ta ce ke asibiti shiyasa bata zo ba amma tace tana hanyar zuwa..
Just shut up, tafada cikin hatsala…
Kece zaki gaya min mahaifiyar ta bata da lpya ? Da hakan ne kuke tunanin zaku rike hakkin jama’a..? I just wonder who choose you two don banga da alaman kun shirya ma zama anan wajen ba.
aikin banza aikin wofi i just hate working with unprofessional jerks..
Kowa yayi tsuru tsuru suna kallon ta na dirin bala’i tana zage zage tana disqualifyng sarah , dama duk masu kaunar ta dake wajen.
Babu wanda yake jin dadin maganganun mrs ruth din, come to think of it sarah bata taba latii ko da na second bane takan zo kafin lokaci yawanci…
Ana cikin hakan sai ga safeenah da hajiya asmau cikin shigar su na alfarma
Ganin anyi cirko cirko yasa take tambayar mrs ruth meke faruwa anan?
kafin ta budi baki tace zata amsa sai ga sarah cikin sauri tana kokarin haurowa inda suke wani irn mugayen kallo ta bita da shi tace just look at her ga nan shasha shan da nake jirah…
Kowa sai ya maida kallon sa wa sarah,
wanda tuni jikin ta ya bata ba lpya ba…
a dan sanyaye ta karaso tana yi tana duba wrist din ta a fakaice its 9.am dai dai..
da kyar tayi hadiyan yawo tare da sauke asirtaccen ajiyan zuciya ta dago tace “good morning maam im sorr….
cikin tsawa tace hold it…
Mrs asmau ta
ce,ah’a a ruth? kar dai sai yan zu take zuwa aiki?
itama sai Ta juya ta dubi sarah cikin wani iron kaskantacen kallo tace” toh? Gaka hajiya dakan ta,hmmmm ure welcome ma..dama haka take miki anan din?work is starting by 7..and I cant belive this this is nine am..
nan ta kamo hannuun sarahn da karfi ta juya ta kalle wrist ta duba time ta kuma jan tsaki ta harde rai tana kada kai.
Cikin son ta dada zafafa abun
Safeenah kuwa agefe sai tanayii tana danyin dariyar mugun ta kasa kasa sigar tsokana tasan duk dan ita su mrs ruth suke wannan badaqalar..
Sarahn na shiru batayi saurin amsawa ba sai da ta nitsu kafin tace” its was an emrgency maam it wont repeat it self…
Amma Kowa ransa sai da ya baci anan,
musamman da mrs ruth ta kuma dakatar da bayanan sarahn cikin masifa…
tace” ki fada ma wasu banzayen irin ki ban da ni
ki kalle ni da kyau ni ba dattijuwar banza bace, did you think i came here just to joke with you, to idan kin dauki abunda muke yi anan wasa ne sai kije duk inda zaki je ki yi playing cards din ki su su duba miki project dinki as for me you are out of my session…
Kar ma ki sake kawo min kanki offishi na
A take hapsy ta dago cikin razana tace but maam na gaya miki uzurin ta akan lokaci, her mum was critical
mrs asm tace wil you shut up,waya sa bakin ki?
Mrs ruth tace barta ai nasan munafucin su wato ni suke so su maida ni mutumiyar banza who know wani wajen yawon banzan ta ma taje zasu zo nan suna mana karyan banza da wofi…
Toh Da girma na i wont take any unserious shit over ,…my dead body..
jalal, daya daga cikin ma’aikatan wanda shima ranshi ya gama baci tsaki ne ya kufce masa bazata