HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Nan na mike ina kokarin ficewa .

Ya dada hade rai Yace saura kuma nazo na kama ki a inda kika saba lafewa kina iskan ci da yan iskan nan marasa tarbiya irin ki,..

madallah ma kinsan yanzu nine aka bar min ke agidan na ko?to ki kiyaye kan ki da ni saratu.

A ladabce nace to ,sai ya juya kansa ya ce
Kuma layin mai goro zakii bi kar ki sake kibi bakin titi kinji na gaya miki kenan.

Gyada kai kawai nayi
Bance uffan ba na sabule nayi waje na kama hanyar kasuwa…

Ina fita Ihu ya sake ya soma rawa yana kirari makan sa adakin shi kadai
” Kiriiiiiii baram bam bam bam bam kaii kai,..sai ni babaji dan gidan goggoji sara dai a hankali…. dawa sai maza,, .. duk wanda yayi jiran tasha dani da shi zamuyi kwanan mota.

Yiiihuhu sai ni babajii dan goggoji yau ango kake tartil babu hafsin.

Kikiki ya fashe da dariyar kuruciyan zuci Mai shake da jahilci da tsananin mugun ta.

hahahaha yarinya yau naki taka kare kwanan ki sai agadon babaji dama chan nagaji da cin durin uwaki…

Ya koma kan gado ya kwanta galala cikin tunani yace”Ga nan rabi bazaura na jira na alayi kwana nan zan yaga ku na auri ta na huta.. Na gaji.

Haba,itama tabi duk ta hanani sakat babu dama nace zan ci nata durin agaban gambo dan nasan munafurcin mata sarai.

Cikin shakekken nishadi yake maganan sa’yanzu duk sai sun gane kuran su.

Ya koma ya dada juyi cikin maganan zuci wanda zai tabbatar maka da ya kullace ummahn ya ke cewa”hnmmmmm Kina wasa dani ne gambo,yo ni me zanyi da saiwar jikin ki da yaya bukar ya gama shanye wa?dama chan dan kuruciyar ki na gani.

dukan ku ai akan tarko na kuke lokacin ku ne yayi,kinga kafin ki dawo daga gaisuwan mutuwar karyan dana miki.

Lokacin har wannan shashashar yar nakin ta san ni waye,

itama da sannu zata haura kan qayar dana daura mata shi yanzu….

kai bari ma na fita saboda naji dadin ganin komai ya tafi min dai dai idan kuwa sageer yamin kuskure nasu ya kare agarin nan.

dariya ce akan fuskan sa ya dau hular sa ya fice hanyar kasuwa.

 

 

_FIRST CHAPTER REVIEWS I NEED SOME MOTIVATION_ ????????, _yana ji na gaji ne_ ????

 

 

 

 

 

 

*Follow Wattpad@ SURAYYAHMS*
[2/23, 22:35] ‪+234 802 646 5734‬: .*????RILLIANT WRITERS ASSO????*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }

 

™/SAT5/ 2019????
????????
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
????????

 

_A TRUE SENSATIONAL STORY_

~_Story written by_~
*SURAYYAHMS*????
*OFFICIALCATTY????*

 

*_WATTPAD_ @SURAYYAHMS_*
@ IG:Surriem-sule_

 

*#Lovestory2018/19*
*#romance#purefiction*
*#Destiny at fault..*
*Any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence”i give no permission for any comparison All my stories are strickly mine,beware copycats!.*

 

*hmm It seems like the universe has given me soo many special maryams THIS PAGE IS also for this exceptionaly special maryam watoh”MARYAM SANEE(mamuhgee)GOD will bless you for me#ride or die with us#die hard is uz????*

*SURATUL HUJURAT*

*2.”Wa La Yagtab”:* Do not backbite each other. Its a major sin equivalent to eating your dead brother’s flesh

 

_PAGE2_

 

 

Umma na da kafa take takowa zuwa tasha don haka ta dau Lokaci sosai don sai wajen karfe 10 na safe ma ta kai kan titi.

anan ma zaman diris tayi tana jiran motan haya koda kuwa akori kura ne ya kaita cikin yankin su inna wuro amma shiru babu wanda ya wulga…

“nikuwa tun da na foce a gidan Tafiya nake sanye da hijabin uniform dina bana kallon kowa.

Gashi dama hankali na ba a kwance yake ba sabida yanayin lungun da baba babaji yace na bi.

wajen shiruuu ne babu mutane sosai,ni kaina Allah Allah nake na samu na fice..

Sai da na kai Daf da bakin gargada naji wani kara kamar an fasa tayar mota sai da na dan razana ,ko samun daman juyi banyi ba naji an shakuro ni ta baya an matse min baki da karfi…

Firgici na shigayi cikin tsainnanen tashin hankali da tsoro ganin sageerr ne a kaina yana faman kokuwa da ni…

Ka sake ni..ka sake ni nace..nan na shiga tsala ihu neman ceto.

Shikam Baice uffan ba ya jawo ni da karfin mallaka yayi wani hanya dani daga nan ban sake sanin meyafaru ba..

Daga bangaren ummah kuwa har yanzu bata yi dacen mota ba, har tagaji da bata lokacin da zaman jira, chan da azahar sai ta tashi ta soma daukar niyyar takawa da kafa kadan kadan zuwa kauyen su inna wuron.

Akwai nisa ba laifi.
ummah tana tafiya ne kamar bata yi,
in tayi ta gaji ta samu dan inuwa ta kan tsaya jira ko wani zai bi nan ta sami wanda zai amince ya kaita ciki amma kusan duk wanda suka shige ba wanda ya amince ya taimaka mata har da fuskan sani.

Ummah ta ga abun mamaki sosai
yau dai gashi da kudin ta take rokon abun hawa amma duk suka turje sam baza su dauke ta ba.

Gashi Ba halin komawa gida ga wahalan tafiya kuma tasan halin baba babaji bazai taba amincewa da hakan ba.

A haka ta daure tana tafiyan ta har magribh ya rufa ana neman ishai lokacin tana dab da shiga babban kasuwar yankin su inna wuron.

Nikuwa sai Wajen karfe 8 saura na bude ido kan wani benchi na tsinci kaina ba abunda ya same ni amma dai an cire min hijabi

,…kuka na fashe da shi tare da mikewa zaune ena duba dan iskan nan wato sageerr”ashe haka maza suke? Ashe duk kalaman bakin sageer karya ne macuci ne dan iska?.meyasa zai kawo ni dakin sa ya ijiye ni?

To wallhy sai na masa rashin mutunci, anan mutuwa ko ni ko shi na fada a zuciye hankali na yayi mummunan tashi.

Cikin wannan bambamin naji ana kokarin bude kofar, kuuuuu ciki na ya tsure jin hayaniyar mutune ” muryan baba babaji na soma ji..don shi yafi na kowa kauri.

“hannu na daura aka..”Wayyo Allah na,na shiga uku,ohhhh ni saratu
“handi mmbani”
Shikenan rayuwa ta ta kare yau..

“Munafuki ,ai yau karyan ku ta kare bude min kofa maza ….na ji babban aminin baba babaji na cewa daga waje

Sageer kuwa sai bada hakuri yake

A tsaye na mike na daura hannu aka zuciya na na duff dufff kamar zai leko waje
Sai gwaff aka turo kofar..
A tsorace na firgita hawaye ne suka biyo bayan rawar da jiki na yake yi

La haila ha illa lahu muhammadar rasullillahi sallahu alaihi wa salam SARATU!!!!

Eh lallai kam saratu yau kinji kunya,toh yau sai na kashe ki agarin nan…baba babaji ya soma bari yana kumfar baki.

Ihu na so na tsala duk gaba daya naji rudani na neman zautar dani,a tsorace na shiga bashi labarin iya abunda na sani “baba wallhy wallhy

Ni ban san me yafaru ba
Ka tanbaye sageer wallhy bani da masaniya akan komai shiya kawo ni nan
Allah ka tambaye shi .na kara sautin kuka ina rantsuwa.
Masifa abokin sa ya shiga mana baji daya kamar kisan kai muka aikata..suka tsorata mu sosai
Barin ni da na kasa gane komai a wajen sai rantsuwa nake ina maimaita abu daya.

Amma Kamar baiji ni ba yace “Ke Kinci ubanki, zancen banza zancen wofi yo ke din ne ban sani ba ko shi sageer din ?

Ohhh mani zaki kawo ma shahshanci “wato har kina da bakin magana ko,?

Na girgiza kai cikin kuka alaman a’a,cikin shessheka nace wallhy gaskiya nake fada maka baba,

Nan Ya dada hatsala. “inayi ki nayi,? saratu …saratu..ya daka tsalle a fusace zai jawo ni abokin sa ne ya damko sa yana basa hakuri..

Sam nakasa gane meke faruwa, meyasa komai ya juya kamar ni na kawo kaina dakin sageer me suke nufi da ni?wai meyasa baba yaki daukar magana na wallhy ban san komai ba.Hasali ma haushin sageer din nake ji da ya kawo ni nan tun tuni ya ajiye ni..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button