HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Haka dai suka cigaba da bin tsari tsarin da aka gindaya musu har aka gama accepting foams din su aka shigar wajen minister zai yi signing ya bada files..

Suna ta jira tsawon lokaci a waiting room Chan da rana daf ana kiran la’asar sai taga safeenah ta mike tsaye cikin farin cikin ta fice waje…

Jim kadan kawai sai taga mrs ruth tare da hajiya asmau sun shigo tare ana ta wasa da dariya da su anan ana raha,…

Tsaye ta mike cikin girmama wa ta gaisheh su amma suka share ta Sai suka dauke kai kamar basu ganta ba..

Suna shigewa paloun minister straigh suka samo sauran political friends dinsu..

Fili ne na taimake ni in taimake ka, yawancin yan siyasan sun san mrs ruth da hajiya asma suna da matukar muhimmacin wajen kare laifi da rufe sa musamman idan wanda zai taba rayuwar su ne su sun san yadda zasu rufe sa tun kafin yaje kotu ko filin sharia.

Shiyasa suma suka sa rai yau za abada safeenah fifiko wajen presntation sheet

Don haka sukayi amfani da wannan daman agaban su minister yasa hannu aka bada clerk ya shiga typing sheet din da zai raba musu don su san yadda za’ayi…

Sai aka debe manyan topic da works din aka saka a red file mai tajen 5b
Blue mai taken 2d din kuma aka sa masa topic sama sama inda ko anyi presnting ma baza abada muhimnacin akan sa ba ..

A wannan lokaci Sosai zuciyan sarah yake bugawa don sai yanzu kanta yayi hitting dalilin zuwan su mrs ruth din…

Wani irin take ji aranta tuni ta soma tunowa da kiran sunan Allah zuciyan ta tana rokon sa adalci da nasara..

Itako safeenah kamar an yaye mata bakin fushin dake mamaye a ranta take ji,don kuwa gani take idan ta samu wannan damar ta lashe gasar her next plan bayan auren su da yazeed zata sa a kore sarah ne a organisation din gaba daya..

Dai dai nan aka ce musu su shigo palour inda su hajiya suke da minister,

Tuni safeenah ta iso ciki wajen su mrs ruth gefe da su ta zauna a shagwabe

Sarah dake rakube a Wani chair aka nuna mata ta zauna tana dada reading bugun zuciyan ta..

Dan karamin formality da shawarwari minister ya basu,sannan ya ce ayi musu handling presentation sheet dama a doka sai clerk ya karance sakamakon dake jikin forms dinsu da suka kawo kafin ya bada file accoding to wanda yafi kokari..

Amma da shike file din a sealed suke sai aka sa number 5b and 2d

Daf yana shirin yin haka sai ga sectery ta shigo ta sanar cewa akwai important visitor

Ko da minister ya tambaya sai a kace ai supervisor ne daga offishin president din WRHA

Wani irin bugu kirjin su hajiya asma yayi amma sai suka fuske..

3 minutes basu kara ba sai ka turo kofa..

Yazeed ne ya shigo cikin wata haddadiyar formall look all black gaba daya yana tafiyar sa cikin nituswa kaf sai da ya ruda wajen da sassayan qamshin jikin sa da gwarjinin sa..

Sai ya dauke fuska Tamkar bai san ko daya daga cikin su ba. ..

Suka gaisa da minister cike da ladabi aji da kwarewa anan yayi bayanin abunda ya kawo sa..

shikuwa minister yace masa ai sun gama komai saboda haka he’s free ya taking over..

Wani zazzafan zufa ke keto ma mutane uku awajen,hajya asma ta riko safeenah dam sabida ta lurah kamar jikin ta yana so ya tsanan ta karkarwa kar tayi magana da tona musu asiri gaban yazeed din..

Haka yazeed ya karbe foarms din dake hannun clerk abun mamaki sai yaga an tsame sunayen su ajiki duk an goge

Kenan idan suka gama cin hancin su sai a maida sunan sarah akan na safeenah sai ace haka aka akawo..

Baiyi reacting ba sai yayi murmushi kasan makoshin sa..

Ya dauka forms yace sarah da safeenah duka su zo,sai ya zuba akan table yace kowa ta dauki nata ta karance..

Mrs ruth kamar zatayi kuka haka ta kife kai, hjya asma kuwa ido kawai ta kura masa dama ita kam ta gaji da halayen sa sosai kiris ya zame yanzu ranta ya bursting…

Haka kuwa akayi sarah ta ja nata, safeenah ta dauki nata da kyar don hannun ta har rawa yake idanun ta sun ciko sosai da ruwa..

Haka dai ya tsaya tare da su kowacce ta karance sannan,
Ya sa clerk ya bada presentation sheet wanda suka rufe a envelope.

Shi blue din da suka sa akayi domin sarah shi aka bada safeenah.
Ita kuma sarah a ka bata red din.

Su mrs ruth basu iya daurewa ba suka fice ta barsu anan..

Safeenahn ne ta iya dan daurewar har aka sallame kowa ya fito rike da file dinsa…

But kowanne a rufe yake cikin katon envelope sun dai san file ne amma babu wacce ta san kalar nata sai shi yazeed da su mrss ruth da shi kansa minister.

Anan wani hamdala mai cike da nishadi sarah ta mike ma ubangijin ta
Batayi nauyin baki ba

bayan sun fito su ukun sai ta ce ma yazeed ta gode,he noticed that she was scared at first kuma taji dadi matuka da taimakon da ya mata a yau din…

Safeenah dake gefe da shi a lokacin jira takee taji yadda zai amsa sarahn sai ta kunce masa hauka..

Har iyanzu gani take akwai conspiracy,ba haka kawai yazeed yake wannan abun ba

Sai yayi shiru bai ce komai ba ya gyada kai amicably ma sarahn..

Murmushi mai kyau ta mayar masa for the first time,itama ta gyada kai ta juya zata tafi..

Tsakin safeenah ya so ya dakatar da ita,amma bata juyo ba.

Shikuwa sai satar kallon ta yake tana tafiya dagan gan inda zai dada sa safeenahn saka wani abu azuciyan ta game da su.

Hakan ya dada hatsala ta ta shiga masa surutu
Cikin bacin rai da takaici duk dama ta san sarahn tana jin ta sosai..

Sai ya shiga shan kamshi yana kaucewa wanda yayi kama da na rashin gaskiya

irin baya so suyi aquing agaban mutane amma sam safeenah bata dena ba..reaction din nasa sosai yake bata mata rai

Duk habaici da maganan da safeenah take sarahn ta ji,musanman ma cewa data yi yanzu ta fahimce shi,wato duk inda mistress dinsu take nan za agansa ba bata lokaci…

Ko tsoron ya taba wanka mata mari akan wannan maganan bata ji ba.

Shikan sa yasan safaeenah ta riga da ta haura sosai ranta ya sosu

So sarah dake gaban su sai tayi saurin bace musu ta haura step su ta barsu suka bi lifter..

Tana daf zata ja motar ta
Ta fice suka kuma cin karo da shi a dai dai kwana yana tsaye yana dube duba alaman wani abu ya ke jira..

But what cud have happen yanzun nan fa suka bar wajen ta dauka ma ko da suka bi lifter sun bar arean wajen tuni

Kamar zata wuce amma sai ta dan tsaya calmly ta sauko ta same sa tace excuse me sir?.

Ya juya a dan dame suka hada ido yace uhmmm?

Ta dan yi quick smile tace hope theres no prblem

Sai ya sake fuskan sa Yace no, babu komai ina jiran safeenah ne ta mance jakar ta a sama..

Gosh,sorry.. tafada tana shirin juyi sai ga safeenah ta iso nan wajen..

Yanzu kam ji take bazata iya daukr wannan rainin wayon ba,wato jira suke ta dan bada space suyi maganan su ko? don haka tana isowa ta wanka ma sarah wani lafiyayyar unexpected mari..

Tabi ta da tsawa mai cike da hatsala tana cewa” dont you have some respect?
U keep seducing him alwys wai ke baki gajiya ne?Baga shi kinsami abunda kike so ba to menene kuma”leave us alone…taa karshe furiously

sarahn da abun ya ci mata rai ta dago zata yi magana ta sake katse ta da cewa

pleassse leave us alone….mrs seducer,…
ni duk wani kisinan ki da munafurcun ki na gane so just cut it okay?

Dai dai na yazeed ya iso wajen zai yi magana

sarah kuma ranta ya rika yagama baci sai tace masa stop..

Nan tayi tsaye face up tana kallon safeenah da fuskan da ya kusa ruguza mata zuciya don tsoro…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button