HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Anan aka kammala komai cikin Sauki yazeed shika dai yasan meke aukowa.

Safeenah da hajya asmau da mrs ruth duniyar su tayi haske da suka ga file din amma basu ko lura da ba original papers bane don wasu ma babu stamp ajiki bai fito ba,amma basu lura ba

Suna nan sun dauka sarah na aiki akan blue file ne kadai…

“Amma duk da hakan Don su tabbatar sai da suka aika aka gano musu sannan suma suka leka suka duba da kansu suka gani ehhh blue file ne a gaban ta..

Safeenah kuwa bata da damuwa duk dama tasan yazeed na fushi da ita Amma samun red file yasa ta sa aranta kwananan ma zata mallake sa inta ci gasa so is better ta kyale sa tayi concentrating

Sai chan Washe gari da yamma liss..
Ya shigo building din straight ya shiga ofisshin sarah…

Wanda ya bata mamaki sosai..

Ta mike ta gaishe sa a ladabce fuska ba yabo ba fallasa,nan ya dire mata asalin original file din ta yace mata daga ministry yake yana so ta fara aiki akan wannan file din kafin ta daura da wancen.

Batayi musu ba ta karba a hannun sa ta duba taga ni,she got intrested sabida yawancin layin aikin ta ne aciki,

Cikin iya tsara magana ya nuna mata muhimmancin yin aikin ta asirrin ce,as a professional advice.

Sosai take ganin burgewan sa yanzu kam afili

Sai tayi masa godiya ta fara aikin akan asalin file din ta akan lokaci ba tare da ta sanar da kowa ba..

Haka kawai jikin ta yake bata maybe akwai dalilin daya sa ya bata advice din tayi abubuwan ta assirii..

 

Daga wannan rana bata sake ganin sa,haka kowa ma ya dauke zafi aikin kawai suke .

Tsaban yadda safeenah ta ke shan lecture da training yasa ta sa rai matuka akan lashe gasar nan,gani take kamar anyi an gama kawai..

Har Sati biyu chas ya cika,

Wankan ranar da ban ne,
Don musamman ummah tayi sadaka da sassaafe domin yarta sarahn tare sa mata adduar sa’a

All black duka akace su sa,
Yau din light make up tayi mai dauke numfashi sai ta sa multi colour veil tayi kyakywar rolling da shi..
Sosai tayi kyau..

Haka itama safeenah da ke gilgil don har make up artist aka kira ta tsaka mata wanka a yau…

Sarahn ma ta riga su isowa sabida haka basu ga dame ta zo ba..

Itakam da shike bata sn komai ba duka file din guda biyu tayi mastering dinsu ta yi arranging din presntation din kowanne a computer ta..

Ga waje ya cika makil da staff da officials da sauran mutanen dake zageya da organisation din ga manyan manyan businesa men ready to share their deals da sabbin investors..

Sai washe washen hakora ms ruth da hajiya asmau suke yau burinsu zai cika sarah zata sha kunya safeenah zata burge kowa..

Don abun ya tafi musu dai dai haka suka nace
Aka sa sarah a farko..

Sabida idan taje tayi kwaben ta ta gama,sai ace safeenaH ta zo tayi wanda ya fi nata armashi domin ta lashe gasar..

Isowar mr persident da iyalansa aka mike tsaye..
A zahirin gskiya leke take ko zata gan sa don ta san dole ne yau yazo nan din

ai kuwa sai gashi abunda bata taba ganin sa da shi ba “…wato jumfa yasha dark brown wanda ya matukar ba ma kyan sa wani sabon kyaun…

Theres no daubt that kowa ya kalle sa ne out of admiration

Sai ta tabe baki,tunanin ta kawai don kwana biyu bata gansa bane and then she feel hes kind to her..

Safeena kam kasa hakuri tayi ta shiga masa ta ido, anan ya dauke kai ya daure fuska amma bata damu ba sai ma sai ta shiga sakawa aranta cewa yau ita zata bata wannan haddaden wankan ranta fal ta zauna

Nan aka soma Jawabi akayo komai cikin nasara kamar yadda aka saba..

Aka kuma basu award dukan su biyu na participating,don da ma sai ka cika ake kaika wannan matsayi..

Bayan ana danyi refrshment nan aka cire haske a hall din gaba daya sai babban majigi dake haskaka wa

kowa na kallon rubutu bororo bororo daga lungu da sakon hall din

Manyar manyar judges ne a teburin gaban
Don haka aka fara kirar sarah bukar ..

Gaba daya sai taji bugun zuciya sai ta lumshe ido tana tuno da maganganun ummahn ta nacewa kar ta karaya tana tare da cin nasara…

Daman ummahn tace zata zo nan din don haka ta bude idanun ta a hankali ko zata ganta amma ko sa ta sauke su suka hade waje daya da yazeed

Ba tan tama tasan sun kalle juna ta wani irin siga sai ya bata murmuahin mai dauke da Karfin gwiwa…

Ta dada lumshe ido for the first time fuskan mahfud ta gano yana murmushi…

Kawai sai ta haura kan step din ta shiga hade haden projctor da nata programe din

Lokaci guda ta gabatar da kanta cikin nitsuwa da kwarjini.

Wasu kam ma fuskan nata kawai suke kallo ayayin da take bayanin ta na gabatarwa

Tana kammalwa aka bata oder ta gabatar da file 5b wanda dama shi ne red dn

Su mrs ruth Wani shuuumin murmushi suke sakar ma juna su irin this is the moment..

Gani suke lokacin faduwar sarah ta kama

A take safeenah ta soma gaggayra jikin ta tana lura da make up din ta tana jiran ta ji anyi blastering din sarahn akan stage sai ita taje ta bada show.

Anan ita kuwa sarah ta bude file 5b ta shiga asalin shirin wanda ya matukar razana mutane uku anan,

It took them time to assimilate the shock..

Da wuri mrs ruth ta zaga wajen masu electric ko za’a san me za’ayi a hana ta karasawa amma ina it was late

Safeenah mrs ruth da hajiya asma haka suka zuna suka kalle sarah tana gabatar da presentation din red file din nan tassss cikin kwarewa da iyawa..
It was a horor movie for them…

Har wani rawan jiki safeenah keyi idanun ta sunkada sunyi jajir
But how coul dis be?

Sarah ko bata ma san me ake ciki ba gashi Har ana mata tambayayoyi masu zafi tana bada profeSsional responds
Abunda da ya dada burgewa shine akwai grouo din company mai karfi da basu taba sa hannu ma wrha winner ba amma sai gashi yau sune gaba wajen gwaji ma sarahn..

Sosai ta kayatar..amma sai tasha mamakin da ba a bukace tayi dayan file din ba akace ta sauka

Anan aka hada file din ta aka buga,
Sai aka fara kiran sunan safeenah moh,…
Wato an kira suna yakai sau uku sannan ta mike a matikar tsorace ga idanun ta sun ciko harkar da kwalla..

Tana tafiya a zage c8kim sanyi tana kallen mumyn ta dake shake da tashin sense sun rasa me zasuyi guda daya a lokacin…
Komai ya wargaje ya lalace musu gashi basu san dalili ba,

Abu kamar na aljanu,su kansu sun san suna sauke da file din sarah amma how comes sarah ta yi presnting dinsa..

Safeenah dake kan stage kirjin ta ne ke bugawa sai rawar murya take faman yi kamar ba ita bace akasa sani the 2nd time winner and the queen of whra…

Ita dai sarah na zaune sai goge ma Allah take tana dada yaba taimakon yazeed aranta Sai ta ce thank god yanzu kenan da banyi wannan file din ba da ya zanyi? Huhhn god tahnk you,a nd thank to sir yazeed he’s really an angel..

Haka safeenah ta kwaba damuwar ta akan stage ta sauka bata ma iya amsa wasu question din ba tsaban ta razana jikin ta sai rawa yake ta kasa controll
So tana sauka tayi waje ta shiga wash room ta fashe da kuka mai zafi agabn mirror

Ba daman zu hajya su bita don idan suka tashi zaa zarge su da wani abu
Ba bata lokaci kuwa ka hada resul aka kwala sunan sarah bukar a stage asba winner the newest and the youngest president of world human right activist and independant female induatrialiast…

Tsaban yadda wajen ya dauka da cheeering da tafi ya sa ogogin su suka dada aminta eh lallai she derseve it don suma idan suka samu 80 percent vote akan zabin da suka yi sukan samu award mai girma daga chan united nations org..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button