SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Kuka dije ta dan fashe da shi,tace Allah zai tona asirin ki,magana take da zuciya cikin harshen fulatanci,
Inda tsoron sa da rudanin quilty conciense yasa ya hatsala ya amsa mata da cewa abunda ya dace dake ne nayi miki”
Baiyi tsammanin ko kadan don ya yayi yare akwai wanda zai ji ba don yasan tsakanin su da sarkin garin su yanzu kowa zai so a rufw maganan sabida kaff a tsorace suke da fargabn fitowar gaskiya..sai ya shiga zagin dije
Charaf sai a kunnen sarah sam baiyi aunen yanda yagan ta yar gayu ga ilimi da kwalisa har zata ji yare ba..
A take ta mike tsaye cikin mamaki tace what?
Sunan sa ta kira cikin masifa…
So malam barau dama kasan da gaskiya kake boye mana ..?
Mamaki ya sa dukan su kallon ta
“tace ka maimaita abunda ka fadi da yare ka maida shi harshen da kowa zai fahimce ka..
Tsohuwa tace kuma kar wani ya sake juya harshen sa anan…
Tuni gardi ya rude..sai ya kuma kwafsawa da yace ba dai kina jin yaren ba…?
Dan karamin tsaki mrs ruth tayi cikin ranta tana Allah wadar da bakauyen mutum
Murmushin takaici ya kufce ma sarah sai ta ta mayar masa da amsar da fulatanci yadda zai tabbatar ba kame kame ma take ba..tace masa yayi bayani idan bahaka ba zata sa a kulle sa kullewar har abada..
Mrs ruth dake ganin wannan wasar zai iya juya musu sai tace enough sarah, ya isa haka mana..
Pls Kar ki takura masa ki bar sa yayi magana.
Sarahn da shike abun ya riga ya shakure mata wuya sai taki saurarawa
tace but maam me za’a jirah Tunda yanzun ya fada da bakin sa ya aikata ma wannan yarinyar hakan,ko dan ni kadai nake jin yaren su ne
Ta juya ta kalle su sarkin sigar ai yanzu dubun ku ya cika”tace ranka shi dade kai ma shaida ne,nasan kaji me yace
Sarki yayi tsuru tsuru kalar marar gaskiya yana hmmmm hmm uhmm
Tace”Malam buba ka maimaita abunda kace ko nasa a maimaita maka da recording camera.
“Hjya bilki na lura sai tace
Ya isa haka sarah,barshi kar ma ya maimaita,ai yanzu mun gane gaskiyan so babu sauran magana
Cikin son ta dada ruda sa tace Next….aje case din wancan matar da ya sa mata wuta…
Cikin rudewa yace wallhy bani bane,mayu abokan ta ne suka saka mata.
Jin haka yasa Sarah ta dada hatsala adan fusace tace kai da yan garin naku ne mayun ko?
Ko ba Kaine mijin ta da ka fara kawo ma jama’an gari kazafin matar ka maiya ce ba?…
Kayi amafani da cewa zasu yarda da kai sabida kai dattijo ne suna ganin bazaka yi karya ba badon sun amince da cewa kai ma mutum bane da yake da ikon tafka kuskure a zaton sa
Sarki zai yi magana hajiya asma tace tsaya,
Ta juya ta kalle indian team din Da suka zage suna sauraran yadda sarah take gudanar da aikin cikin gamsuwa da bayanan ta
Amma”don ta fara cusa musu wani ra’ayin sai tace”Wannan case din ai tsakanin mata da miji ne,sarah i think you shud mind your words ki barsa ya fadi wacece matar sa dakan sa don shi ya zauna da ita ba ke ba.
Maganan sai yaje garas a kunnen ta.
Murmushi kawai yazeed yayi,..sosai ya dago wani abu
anan wajen mrs ruth ma takara da nata point din duk don su murda maganan suke gwada cewa ya za’ayi sarah tace ta gano gaskiyan tsakanin mata da miji ?
Dan karamin juyin da suka cuna ma zancen sai ya fara shiga kan mrs abdl rashed rani, da shike dama shikam dan culture ne kuma ya saba da tsinannen al’adun su na chan kasar india
Har da cewa ai macen da bata da tarbiya ne kawai zata san meke tsakanin ma’aurata tun batayi aure ba..”
Duk sai suka bi suka kauce ma case din sabida su rusa sarah su dada hatsala ta .
.
Karshe shiru tayi tana jin su suna masa tanbayayo marasa ma’ana da kargo …
Bayan ga gaskiya nan ana gani afili
Amma duk da haka tsoron idon sarah gardi yake yi sosai,…
Ita kuma a ranta tasa cewa duk rintsi sai ta tona asirin mutumin don ta gama sanin gaskiyar lamarin sa.
haka aka tashi na ranar a 50-50 sarah ta tabbatar da gaskiyan cikin dije na gardi ne
Amma basu bata damar warware maitan da aka daura Ma mahaifiyar dijen ba
Yazeed da mahaifiyar sa basu ce komai ba tukun dama nasu sauraro me da wanzar da hukunci ma mai laifi,…
Tsohuwa ce ka aka brta a tskiya, wani xUciyan yana ce mata aqidan su mrs ruth dai dai ne sarah karamar yarinya ce case tsakanin miji da mata bai kamata tayi nisa akai ba.
Daga wani bangaren kuma tana ganin kwarewar yarinyar da basiran da Allah ya bata wajen fito da gaskiyan lamari..
Kwana biyu aka bayar na tabbatar da gaskiyan lamarin maitar mahafiyar dijeh,
Gashi kowa ya sani ba shari’an maita a kotu.
Dole su din ne zasu warware case din..
Tun Daganan sarah ta san dole ta nemo shaida mai karfi wanda zai sa gardin na dan dolen sa ya tona asirin kansa
Ta dai ci nasarah akan na dije cikin sauki an gano shi…tasan kuma dole ayi masa hukunci aka abunda ya aikata mata amma sam bata so ya tafii a banza da abunda ya ma mahaifiyar ta.
Bayan an watse kowa ya tafi Daga gefe ya tsaya yana duban yadda take tafiya daga gani yasan case din ne yake taba mata zuciya tunani ne fall cikin ranta.
Murmushi kawai yayi ya wuce sama inda yasan tabbas anata shirye shirye ne na munafurci don dazun dama shiru yayi don ya gano wani abu gane da mutanen sa.
Bai shiga ba ya tsaya yanajin su Mrs ruth da mrs asma suna dada kawo maganganu indirectly akan kankantar sarah ma aikin ta gaban wayannan bakin,
Maganganu suke kamar suna bada facts akan abunda duniya ke ciki”
Suna yi suna kwo misalai kala kala akan organisation dinsu.
Musamman tarihin yan matan da suka shude wanda aka kama su da laifin kala kala aciki har da wanda ya kusa sauke darajan organisation din su shekara 10 daya wuce.
Cikin salon maganan nasu sosai suka saye zuciyan wayannan bakin har suma suka tsinci kansu da bin wannan ra’ayin sosai.
Hjya tsohuwa ce ta furta cikin zakuwa cewa’tana jin tsoro kar wannan sarahn itama ta kawo musu hadari, tana ganin kamar next time ya kamata su sa a tsarin gasar WHRA akan sai mace mai aure ko wanda take da namiji tsayayye zata cika filin shiga gasar.
Dadi kashe su mrs ruth tace ahhh toh,..
Shiyasa naji dadi a lokacin safeennah yar wajen hajy…
Kunsan kuwa…cahraf sai yazeed ya katse maganan nata da bude kofar sa..
Murmushin dole su biyun suka sakar masa.
Ya gaisa sama sama da mazan ya zo ya zauna kusa da tsohuwa..
Dama ta saba da shi don itama tamkar god mother sa ce,…
Ganin sa ya sa ta dena jin bayanin mrs ruth tana tambayar sa dama baka tafi gida ba?
Cikin salo Yace kema ai baki tafi ba..so,nima nazo naji hirar da kike yi ne ,tayi murmushi tace ruth ke gaya mana abunda ke faruwa anan
Sai ta dan maimaita masa point din su na cewa yanzu bazasu na bawa fili ba sai mai aure ko wanda is engaged zaiyi qualifyng duk dama ya ji daga wajen amma sai ya nuna abun yayi masa shima..
Hakan ya matikar ba hjya asma da mrs ruth mamaki don sai da suka kalle juna ..suka tabe baki.
Mrs ruth tace”tsohuwa kinga kamar safeenah da cahn ai ita akwai yazeed kuma duk munsan shi zai aure,..
Sai zuka danyi dariya duka shikuwa ya tsime tare da dan daga kafadar sa jikin jan aji…
Yace but we wernt engage kuma i kunce sai aure ko engagement..
Hajya asm ne ta karba maganan Cikin son ta yarfa sa tace” duk da haka lokacin safeenah erah biyu tayi amma ba wanda ya taba samun wani lapses sabida hankalin ta na waje daya …Yo meye maraban ta da macen dake gidan miji since ta iya ajiye kanta ma namijin daya .?