SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Duk dama bai kawo aransa su suka sa aka mata alluran ba..
Tsakanin sa da safeenah yanzu abun yayi sanyi sabida kullum acikin kona ta yake da halayen sa,sai ta rika ganin kamar hankalin sa nakan sarah amma wani fannin sai ya nuna mata kishin ta ne kawai ..
Sosai ta shiga wani irin haki da zuciyar ta komai ya cunkushe mata amma bata iya ganewa..
Kiran hapsy ne ya soma shigowa bayan sarah ta sauko,
Ita ta sanar da ita abunda ya faru na rasuwar mahaifiyar dijenh.
Tsaban yadda ta ji ba dadi sai da ta nemi waje ta tsaya ta dafe kai tana hawaye mai cike da tausayi..
A lokacin sai Bata je gida ba san da taje ta duba gawan … sannan ta ba da dije karfin gwiwa sosai kamar yadda mahfud ya koya mata.
Ko kadan batayi noticing din wanda ke bibiyan ta ba.
Tana tafiyan ma tunanin rayuwa kawai take,
A yau Hapsy ne kawai tasan cewa ta samo shaidu masu amfani.
Washe gari Da safe kamar mai zazzabi haka take jin kanta haka taci ranar baki daya bata iya ayyana komai ba in banda aikin lallaba zuciyan dije da bata karfin gwiwa..
Da yamma sai ga aljan ya kira su hjya ya sanar dasu cewa shaidun da sarah ta nemo sun iso…
Anan ma tace masa good..
Tunda sun iso yanzu zai iya aiwatar da aikin da suka bashi akanta.
Sarah kuwa Masauki ta sa aka basu sai dai bata samu daman haduwa da su ba akan sai goben kawai karfe
3.00 dai dai a wajen sharia zasu hadu.
So washe gari da safen
Batayi niyyar futa da wuri ba amma sai aka dame ta da kira cewa ta zo dije bata da lpya.
Yadda ake magana awayar gani taje kamar dagaske dije na wani hali..
Duk sai ta soma tunanin ko dan mutuwar mahaifiyar ta ne har yanzu ke damun ta..
Dama tasan zai dauke lokaci kafin ya sake ta…
Ta san an zalunce ta.
Haka ta shirya agurguje sukayi sallama da ummah ta fuce,
Tana kama hanyar gidan da su dije dake a dai dai kwana nan wasu motoci manya guda biyu suka shakure ta suka tunkuda ta cikin nasu suka tafi da ita..
Lokacin karfe 9 saura ne ma safe..
ko da ta dubi mutanen motar duk maza ne kuma bata gane ko daya acikin su ba.
Wani gida suka kaita, suka daure ta kan kujera na tsawon awa 3 ba wanda ya lekota
Daga bisani chan wani ya zo ya mata allura ta tafi unconcious..
Bata sake sanin inda take ba
Har lokacin sharia yayi babu sarah..
Kowa ya hallara babu ita sai kiran layin ta ake amma taki dagawa.
Shi kuwa yazeed nitsuwa yayi yana duban yadda kowa yake nasa bambami don yasan dole akwai abunda ya faru..
Mrs ruth ce kan gaba wajen sake kawo maganan kankatar sarah ma aikin nan..
Ita kuma hjy asma take cewa hala don taga mahaifiyar dije ta rasu ta ke ganin bazata iya facing case din ba..
Anan ba irin maganganun da basu akawo ba ,…mafi akasari suna dangan ta shi da cewa ai yaranta ke damun sarah…
Ta ajiye su tana wasa da hankalin su..
Abu tun karfe uku Har wajen karfe biyar saura ana jira,
Sai yazeed ya zame ya je gidan su.
Kamar ba abunda yake damun sa ya gaida ummah ya kuma gabatr da kansa ,amma bai fito fili ba
Anan ya nuna mata cewa daga kasar waje ya diro yanzu yana so ya san inda sarah ta ke don yaje ya same ta yana da muhimmim aikin da zai bata…
Ba laifi ummuh ta gaya masa ai kiran ta akayi a gidan su dije..
Abun ya bashi mamaki amma Ko kadan bai nuna tashin hankali akan face dinsa ba ya ke tambayar ummah, a haka har ya kama hanya yayi hanyar gidan su dijen.
Yana dosu kwana yaga wasu maza na kokarin tsallaka titii sai leke leke suke…
Ya sa ido yana dan duban su with less serioussnes sai ga shi chan dayan ya fito a cikin motar sarah suna kokarin barin wajen
Da shi..
Mamaki ya hana sa cewa komi sai ya batar da kaman sa ya shiga binsu tsala tsala..
Wani gida suka shige bayan kamar mintuna 10 suka sake fitowa amma wannan karon babban jeep ne sai motar sarahn a baya.
Sai da ya bari sun fice shima ya shiga binsu wajen har wani hotel suka shiga ..
Yana ji yana gani suka shiga da wani katoton jaka wanda su hudu ne amma suke kokuwa da shi ciki
Shima sai ya buya gaba daya bai bari sun san da shi ba.
“Wani abu na gaya masa cewa sarah ce a cikin jakar nan..
Amma sai ya fuske ya jira su har suka bar wajen suna barin hotel din
Ya je straigh wajen recptionist,cikin iya salon zance sai ya ruda ta da cewa tare da su yake sunyi mantuwa ta bashi key..
Salon sa da kuma yanayin yadda taga zubin sa yasa ta hakura ta bashi key din..
Da yana tafiyan sa ne cikin kasaita amma yana wucee ganin mutane ya haura sama da uban gudu ya kai dakin da aka ajiye sarahn.
Yana budewa kuwa ya hango ta Kwance babu dankwali bare rigar suit din duk ancire su an bar da dan karamin vest mai guntun hannu dake ciki
Wanda har shatin bra din ta yake nunawa
Sai bacci take kwasa sabida maganin awa 8 aka bata dai dai lokacin da suka shirya shirin su.
Wayar ta kuwa tuni suka kashe mata shi don haka duk wanda yake neman ta a ranan bai same ta..
Haka dije taci kuka har ta gode ma Allah….
Ganin ran kowa ya baci da abunda sarah tayi musu yau
sannan anan ma shirin maida shaidun gida washe gari ake idan ba ga a sarah ba..
Tunanin su tunda abun yakai ga haka Sai a kashe case din tunda ma mahaifiyar dije ta mutu ai shikenan..
Su hjya asma Masifan karfin hali kawai suke amma ransu yayi matukar dadi..
Wannan shine kankat gashi jira kawai suke wanda suka tsara musu zance su shigo su bada information din ai sunga sarah a hotel tun safe..
Sai aje duka a kamata
Shi kuwa yazeed baiyi kasa gwiwa ba ya dauke ta, yaune rana ta farko da sarah ta shiga hatsarin da baida alaka da sanin faruwar sa..
Sai yayi kokarin saka mata jacket din suit din za ya dagota a hannun sa yayi saurin haurowa da ita suka bi lifter
Daure fuska yayi ya fuce abunsa bai ko bada keys ba anan dakin ya bar musu..
Sai dai bai daga car dinsa ba ya shiga nata da shi suka bar hotel din
Anan organisation Ko da aka kawo news din sarah na hotel kamar yadda suka tsara maganan? …
fitina da tashin hankali bai tsaya anan ba sai da aka kira asalin mahaifin yazeed alhaj nafiu Attah aka sanar da shi.
Cikin tsananin bacin rai da bakin ciki su hjya ke xprssing rashin jin Dadin su…cikin salo suna dada sa wuta akan case din.
Tsohuwa ta sha mamaki matuka,…batayi tunanin haka sarah take ba
Lokaci guda aka gauraye wajen aka shiga emergency meeting da hajiya bilkisu akan za aje a kama sarah red handed
Sai ayi mata hukunci
Tsohuwa da alhaji nafiu ne kawai suka rage a office suna jiran adawo da ita a mata hukunci.
Gashi informat din ya tabbatar musu da kasancewar sarah anan
yazeed kuwa bai tsaya ba sai da suka yi nisa chan cikin wani quest house ya ajiye ta daf tana firgicin farkawa
A lokacin kuma members Dukan su da suka isa hotel din a dane suke suga niyar su ya aiwatu…
Don haka basu lura da motar yazeed ne anan babu motar sarah ba.
Cikin tsananin mamaki haka suka bincike ko ina anan hotel ba su ga sarah ba basu kuma ga alaman ta ba
Zufa da ciwon kirji lokaci guda ya kama hjya asma sai insisting take adada dubawa
Har mrs abdl rasheed rani yaji haushi ya fice abunsa.
Anan suka bar mrs ruth da mrs asma suna jimamin abun suna dada dubawa cikin tsananin firgita
Sauran members su suka je suka sanar da tsohuwa da alhj nafiu cewa karya ne babu sarah a hotel kamar yadda aka fada musu..
Dai dai nan kiran yazeed ya shigo wayar mahifiyar sa, ta dauka cikin zakuwa tace wai ina ka shiga ne anata faman rigima anan?.
A dan birkice yace mum ba lokaci, its about sarah.