SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Lokaci guda kirjin ta ya buga tace what? Sarah
Ina take meyasa me ta ?
Kowa sai ya mike tsaye tsohuwa ce tace a samata shi a hnsfree
Don tun da chan basu ko kawo tunanin ko wani mummunan abu bane ya same ta musamman da su hjya asma suka rika cusa musu mugayen maganganun su..
Muryan yazeed suke ji garau yace musu mom sarah was kidnapped..
Amma bani da time din bayani sosai sabida motar ta nake using za ayi trcking dina.. so Do me a favour ga number daya kira ta last nan a wayar ta na samu a duba da wuri aka masu..
Hankalin su ne ya tashi sosai,kowa na jero nasas tambyar wasu suna cewa ina sarahn take? Wasu suna ce masa ina yake ,duk suka ruda shi
sai ya Kasa aje kansa waje daya yace kawai suyi bincike shi zaiyi handling komai..
Nan take case ya sauya aka turo number aka kai offishin masu bincike
Daga nan kuwa har spy din su hajya ya gaya musu yazeed ya samu wayar sarah da motar sarah har ya bada information..
Amma baice yana tare da sarahn ba
Wani sabon tashin sense Kamar zata sume cikin tsannanin tsorata suka shiga namen layin su aljan dun su san abun Yi
Cewa yayi su kwntar da hankalin su tunda yazeed yana tare da wayar zasu yi tracking dinsa kafin polisawa su gane su..
Hakan ya faru kuwa sai dai wajen da suke na da nisa sosai.
Daga nan kuma lokacin dayake wayar sarah take jinsa duk dama idanun ta a lumshe suke.
Ruwa ya kawo ya tallafa mata ta sha sannan ta shiga tanbayar sa meya faru da ita.
Anan ya mata bayani abun ya matukar tsorata
She bacome weak sai ta fada kan gado ta fashe da kuka mai cin rai..
Sosai hankalin sa ya tashi, ya shiga rarrashin ta yana bata karfin gwiwa amma ina tsoro sosai take ji yanzu kam
Har sai da ya jawo ta jikin sa yana bata comforting smooch sannan ta samu ta nitsu..
Sun kai wajen mintuna 20 a hakan yana shakar dumin jikin ta tana shakar nashi..
Wani abun yasa ya dube wayar sa anan jikin button din yake ganewa cewa ana reading locatiom dinsa
Sabida tsaro ya sa ya kame wayar su baki saya ya kashe,
Sannan ya sauya musu
Daki
Itakam Ta kasa tunanin komai sabida abubuwan sun daga mata hankali matika..
Kenan kashe mahaifiyar dije akayi dagan gan? Whats so special in this case da har za yi wasa da rai?..sosai ta shiga cikin damuwa tana kawo tunani kala kala.
Daga gida kuwa ummah ne dakan ta a ofisshin,bata ga yarta ba kuma wayar ta baya shiga..shine take tambayar ko sarahn tana nan amma sam su hjya billy suka kasa sanar da ita komai..
Da ganan kowa yake nadaman yadda ya tsananTa harshen sa akanta musamman indian team..
Cewar hya billy to lallai akwai makarkashiya mai girma a wannan case din
Dole za a tsare gardi har sai anga dawowar sarah.
Ita ma ummah ta kasa basu space daga ace sarahn na waje kaza sai ace tana waje kaza duk don sun ga ta mugun daga hankalin ta..
hankalin su abtashe yake amma sun yaba da yadda ummah ta sa ido sosai akan tarbiyan yarta sun lura cewa sarah is wel guided Nd monitored at home..
Ba kamar yadda aka cusa musu ra’ayi akan tarbiyan yan mata irin ta ba.
Ana neman karfe 10 na dare ummah ta tsanamn ta lallai sai an bata sarah tayi mata magana
Da kyar hajya billy ta zaunar da ita ta mata bayani, ranar kwana zaune duka sukayi anan ummah ba abunda take illah hawaye..
Anan guest howus kuma mrs ruth tace ma si aljan kar su bar wajen har sai yazeed ya kunna wayar sa sabida dole ne su san ko shi ya dauke sarah don su san abun yi
Ita kuwa sarah Tsoro da tunani yasa ta dukun kune waje daya,..har zazzabi mai karfi yana neman shige mata.
Dan dolen sa ya zauna da ita ajikin sa yana comforting din ta har ta samu tayi bacci da kyar
Shikam bai runtsa ba kallon ta kawai yake
A ransa yana saka abubuwa da yawa..
Har cikin ransa yana so ya mallake ta ya shiga rayuwar ta.. yaga tana mutuwa masa sai yake ganin kamar ma gashi Allah yana ta bashi daman cikar burin sa.
Murmushi kawai yake yi agaban innocent face din ta yana tunanin ranar da sarah zata furta tana kaunar sa dakan ta..
Don Shika dai ya san me ya shirya mata aransa.
Washe gari da safiyan Allah da suka tashi,
Bayan sun gaisa take cewa tana so ta kira ummahn ta..
Yace no we cant use any phone sabida ana tracking din mu..a yanzu yadda zamu tafi gida ne kawai zamu nemo..
Tace ohhh ya Allah, toh su waye wayannan me nayi musu haka? toh sai mu cigaba da zama anan kenan. For how long ?
Kar wani abu fa ya same dije ina nan.. this ppl call me bcos of her what if thy have her now?…look i need to do something now…gaba daya yazeed kallon ta yake ta na neman birkicewa tana maganganu cikin tashin hankali..
Tsaye ya mike ya karaso wajen ta tana kan magana…ya lura hawaye ne tam idanun ta masu dauke da tsoro da kuma fargaban abubuwan da suke faruwa..
Ajiyan zuciya tayi ta dafe kai” tana cewa Allah ya sa itama dijen ba wani abu za’ayi mata,i wonder who the helll is doing this
Meye riban sa toh? I wish thy cant just leave them alone and face me in dai har gaskiyan ne basu so..
Hawayen ta ne yayi droping cikin tsananin damuwa da tashin hankali ta sunkuyar da kai kasa tana tare wa
Yayi dan murmushi ya riko shaking hands din ta duka biyu yana dan murxawa… kamar zata kwace amma sai ta kasa anan ya jawo ta jikin sa a hankali ya rungumeta yana cewa its ok sarah..
Ya isa haka.. dije tana nan lpya.. kece kawai baki nan and i know sabida kar ayi case din aka yi miki haka
Yanzu abun da zakiyi shine ki kwantar da hankalin ki ,u gonna be fine
Relax ok?
Nan ta dan daga daga jikin sa ta dube sa cikin sanyin jiki tace ok”
But…..
Heyyy stopp..ya dada tsare ta da cewa..
Yanzu yadda zamu fita anan ne kawai matsalar you just have to calm down ok?..da kyar ta kwakwalo murmushi ta gyada kai
Cikin sanyi ta zame ajikin sa ..Kan gadon ta koma ta zauna yana cigaba da binta da ido..
Daga bakin gate kuwa anan mutanen aljan suke rarrabe suna monitoring din shiga da fita a boye sabida sun tabbatar da cewa yazeed na nan amma ba su san ko yana tare da sarah ba.
Cahn ana neman karfe 10 na safe tashin hankali daga both side ya hana su ma jin yunwa daga bisani…
Yazeed yace mata zai fita amma zai dawo yanzun nan..
Mikewa tsaye tayi zatayi magana, ya mata alaman a’ a…
Tun da ya fita sai Bayan kamar 10 minutes ya shigo,…tace what happen zamu iya tafiya yanzu ko?
Yace no, amma zamu raba hanya…come on get ready ya fada yana dada leke ta window.
Rigar suit din nasa ta dada gyarawa a jikin ta sannnan ya riko hannun ta suka fito daga dakin a sace yana yi yana dube dube har suka kai bakin wani lungu ta baya acikin guest house din.
Gani tayi an ajiye wani drum gefe da katanga alaman shi ya shirya ..
Yace hurry up comn zoki hau..
Batayi musu ba ta hau ya dale shima ya taimaka mata ta sauka har kasa ta baya..
Ko damuwa da gurjewan da hannun ta yayi batayi ba ,ta dago tana jiran sa, sai taga ya ce kiyi sauri ki isa bakin titi,ni zan taho da car din ki yanzu if not idan suka same mu tare wani abu mummuna zai iya faruwa da ke..go now.
Har zatayi musu ya ce mata,if you dont want dije’s life to be in trouble you wll hurry up you must go sarah bamu da lokaci..nan ya juya ya koma
Itama ta kama hanya ta shiga falfalawa da gudu
Zuwa bakin hanya.
Yana gama reading time din daya dauka ya taho ya shiga motar nata ya danna horn da karfi yadda zai dada jan hankalin su nan aka bude masa gate ya fito…