HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Kallon ta yaje yana so ya gane ta amma ya kasa bada brain dinsa amsa daya A dik maganan da yake fada sai yana ji kamar ma saratu yake kai kukan nadaman sa amma kuma aganin sa ba itan bata ce agaban sa…..har yaushe saratu zata daukaka haka?

Sosai suka fahimci juna a kalmomin nasu da wanda take furta masa da wanda yake bata amsa a cikin nitsuwa kamar bashi ba.

Sukan su dattijai sun sha mamakim yadda suka ga baba babaji ya nitsu a gaban sarah yana magana mai kama hankali,

Tunanin su hala dan dama ance sarah ta mugum kwarewa da sanin halin mutane sa bi da su ya sa ta samo kan baba babaji

Har ta gama ta hada maganganun ta a report tasa shi a jerin wanda za a kai su rehabilitation center a ajiye su ana basu kula

Sannan ta kafa programe mai karfi a dan karamin makarantar primaryn kurwala da asibitin gwamnati sabida wayar da kan jama’ar garin.

Har sai da ta zo tafiya,bakin kofar gidan sarki an cika tamm da jama’a,matasa yara da mata.. tsoffi da kakkani makil a kofar sarki hammayo na da inda aka kora su da ummahn ta,

A ranar kowa yayi tururuwar zuwa nuna farin cikin su ma sarah data zo musu da wannan cigaban,banda abubuwan alheri data raba musu na more rayuwar dan adam dama kiwon lpya
Akalla ko wani gida kafff kurwala suma sa tsarabn da ta zo da shi..
Musquioto nets,blankets,mganin sauro su kansu da sauran su kowa ya wadatu da shi sai murna ake

Anan ma dai dai ku ne basu hallara ba kamar irim su baba babaji sabida ya saba da tsanwagwama kuma riga am haramce mishi shiga cikin mutane.

Agents din ta na gefe,ta tsaya ganan kowa cikin jawabin ta ,ta musu nasihan akan mummunan abunda suke aika ta ma kansu na jahilci da cin zarafin nakasa da su.

Sai ta hada da abunda suka mata ita da ummah cikim hikima Tas tasss ta wanke su sai da jikin kowa yayi sanyi,
sannan ta dawo Tana ganin yadda yayun ta suka dawo tsoffi karfi da yaji ga yara gaban su rututu sai ido suke fitarwa tsaban takauci da wahala.

Ta so ta sanar da su itace saratu sai ta tuna da ba ita kadai bace anan da mutane ta zo.
Its her personal life that she wont like to publicise it

So bayan ta gama bayanin ta sanar da sarkii ci cewar nan da wata guda zata sa a zo a dauko duk wanda ta sa sunan su,har da baba babaji..

Da har kamar zata shige mota kawai sai ta fasa tare da ce musu tana zuwa.

Gidan mahaifin ta ta wuce direct, ta same su nan tsakiyar gida ana ta san barka Da ita.

Sun sha mamakim ganin ta amma ji take bazata iya barin garin batare da ta sanar da wani nata cewa ita bace..

Nan suka mata fadan ci
Zuciyar ta kamar zai fidda ruwan hawayen da yake zuba

Amma haka ta daure ta sa aka taro mata kan yan uwan ta da yayun ta a tsakar gida su ya sun su.

Duk sun tsorata sun dauka ko wani sukayi ma musamman

Sai da ta bari kowa ya nitsu sannan ta soma gaya musu asalin itace saratun su..

Kanwar su, yar su.wanda suka tsangwama Suka kora anan kurwala

Cewar ta ya zama dole
Ta sanar da su ita waye tunda jini daya gare su,mahaifin su daya sannan duk da sun guje ta ita tasan duk inda kaje ka dawo hannun ka bazai rube ka cire ka yar ba
.

Cikin tsananin tashin hankli da mamaki kowa ke jin ta har sai da ta gamsar da su eh ita din ce,Masu suma sun suma masu fashe wa da kuka sun fara, a hakama mafi akasarin su sun tsorata matuka

Don haka kowa ya rusuna gaban ta yana neman gafara ta cikin nadamam rayuwa..
Ba a jin na wani.

Da kyar ta lallaba su
Wasu sai boye fuskan su suke ,yau su yaya mati da yaya hamza ke kuka sharbe sharbe agaban ta
Anan suka shiga tambayar ta labarin ummah

Inda ta sanar da su rayuwar su mai shake da cigaba,kwanciyar hankali da jin dadin rayuwa..

Kowa sai da yaji ragowar imanin sa ya motsa
Tabbas wannan alhakin ne ya gauraya musu zaman lpyar sa da kwanciyar hankalin su..

Gashi Allah ya saka ma gambo ya kuma daga saratu,
Sannan ya kaskantar da dukkan wanda suka zalunce su..

Kowa sai da ya bata labarin sa,jikin jimamin nadama
Inna wuro kam tuni Allah ya mata rasuwa

Ganin zata bata lokaci ya sa ta rubuce cheque mai kauri ta bada babban yayan su yaya mati ta kuma masa bayanin yadda zai ciro su ,akan ya raba ma kowa da kowa kudin isasshe tare da musu albishirin ta yafe musu haka ma umman ta.

Anan Duk suka hada baki cikin jin kunya suka ki amsar kudin data rubuce musu,kowa na fadar kaicon sa akan irin bakar wulkanci da tozarcin da suka jefa rayuwar ta aciki

Sosai ta zage tayi kuka sabida bata taba tsammanin nadaman su ya kai haka ba,

Ko a mafarki basu yi tsammanin zasu sake ganin ta ba bare kuma
Har a wannan yanayi

Da kyar da nasiha ta sa suka amince

Bakin cikin su daya shine da suka ga alaman kamar ta yafe sun me amma bazata sake haka zuria da su ba..

Basu so ace ga nasu nan Allah ya daukaka amma
kuma baya tare da su ba..

Amma ganin girman abunda suka mata da kuma saurin yafe musu da daraja su da tayi yasa
Suka mata uzurin haka..

Tsakanin su sa ita sai dai a sunan yan uwan taka but no family attachment.

Sannan ta roki alfarman cewa kar su fada ma kowa itace saratu muddin sun san ba zai rufe bakin sa ba..

Domin bata son hakan yayi sanadiyar kasa samun daman ta zo ta taimake su akan kari..

Tace “Idan da jama’ar gari zasu gane ita ce, nadaman da koke koken zai jawo mata koma baya wajen mance da abubuwan da suka riga suka shude

Haka kowa yayi mata alkwarin,har suka rabu cikin amana da jimamin juna..

A lokacin sai taji wani sanyi na ratsa ta fiye da na koyaushe

Ko da ba ace komai ba yau tayi magana da wanda ya dasa mata bakin ciki a duniyan ta
Yau Dakan sa agaban ta ya fada mata nadaman sa
Ta ga sakayyar Allah kiri kiri atattare da shi..

Sannan maganan da yan uwan ta ya sa ta dada jin sauyin yanayi, a yau ko ma yaya ne tasan mahaifin ta zai yi alfahari sa ita tunda bata watsar da zuriar su ba..

Haka suka kama hanyar airpot

Tana gani jerin yan uwan ta ne agaba wajen mata
Hannu, sai da naciki ma ciki

Sai gani ake suna share kwalla amma ba wanda ya lura da make faruwa
Har si sarahn suka bace

Abun ya matukar girgiza familyn ta don kusan sati gida suka dauka suna jimamin abun

amma Haka suka rike amanar ta ba su fada ma kowa saratu bace sarahn
Haka suka raba kudin tsakanin su cike da sama ta albarka..

A chan abuja kowa rayuwar ta da yazeed ba wani canji yadda suke haka yake tafiya

Tana dai kan missiom din ta na sa shi dole ya baiyana mata sirrin abunda ke tsakanin sa da ita..

Bayan sati biyu a washe garin Ranar talata,

Wani abu ya hada baba babaji da sageer achan bayan gari inda yake nomar sam.

Yunwa ta hana baba babaji zama don haka ya fito yana bin jeji ko zai samu ya dan dauki ko da masara ne a gona ya gasa ya ci

Anan ne sageer din ke masa tijara da zage zage, kamar bai san shi ba.

Har sai da ya tara masa jama’a makil akan sa yana tsine masa

Da kyar yaya hamza ya shiga tsakain rigimar ya kora kowa ya barsu anan su uki

Anan ya shiga musu fada, cewar sa ya lura tun da sarahtu ta bar garin wani mummuman Tashin hankali ke wanzuwa a tsakanin su
Har yau absu shirya ba

Cikin taurin zuciya da bacin rai sageer yace”
Yo ai tsakanin na da wannan bakin azzAlumi sai gaban Allah..

Anan ya shiga sake tonu maganan yadda ya wulakanta sa da uban sa akan filin gida duk akan haka yasa shi ya ma sarahtu sharri ranar ba don san ransa ba..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button