HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Sai sa ya sake tuno masa cewa shiyasa mahaifin sa ya yi karya akan saratu duk dama yasan burinsa ne ya aure ta.

Sageer sosai ya rike abun aransa yasan yayinma sarah butulci kuma ya cuce kansa matuka

Tuno da sarahn ya sa baba babaji sake shiga wani hali ga yunwa na mugun cin sa a lokacin..

Haka yaya hamza ya zaunar da su…

Yayi musu dogon nasiha mai shiga rai..

Daga bisani ya sanar da su maganganun sarah
Da dada bayyana musu cewa Sarahn da suje fada akai ma da ta zo

yace matar nam fa saratu ne da suka sani ba wata…

Rike rike aka soma yi da baba babaji zai fada kasa cikin tashin hankali cewarsa a kyale sa zai je wajen ta neman gafara ko Allah zai jikan sa .. Ya sassauta masa daga bakar rayuwar da yake ciki

Da kyar da wahala suka yi convincing dinsa …

Amma inabSai da ya turje anan suka bashi goyon bayan akan cewa zaije birni ya nemi gafarar saratu tunsa yanzu yasan inda take..

Gani yake idan ta yafe shi shikenan zaiji sauki

Sageer ma yace toh zai bisah sai suje tare.

Yaya hamza kuwa dama so yake su sassauta makan su yafe ma juna gaban shekaru da suke rike ma kansu.

Hakan Kuwa ya faru,yanzun kawai so suke suma su fuskance ta su fadi abun da ke ransu su huta..

Babu wanda ya san da maganan
Baba babaji da sageer suka yi shirin tafiyar lagos

Kwana biyu suka rafka a mota sannan suka iso garin lagos..
#surayyahmz

*Writers note*
_godiya ta musamman ma masoyan surayyahms a duk inda kuke …Acikin shafukan whatsap mafi akasari naji ana cewa this is the most anoying storyline surayyhams has writen sarah tana bada kowa haushi,well yes gaskiya nima zuciyata na min zafi da takaicin musamman ni da nasan kan labarin gaba daya” amma let me make it clear to you dearies…sometimes we must face the bitter truth to learn the most important lessons in life,this story has already happen in reality arond 2012,..99.9% of our girls are going throu so much in hands of this cassinovas,heartgamblers,deceivers,sai nake ganin wanda yawancin suke korafin sakarcin sarah inda da qaddarar ta zai sauka akan wata sai taga tayi abunda yafi nata sabida samarin shaho fa sunyi kama ne amma ba dai dai yake da mayaudari ba,shi baiya aikin sa da garaje dole sai ya gina foundation dinsa mai karfi a zuciyar mace inda bazata taba gane kalar sa ba,most of the men appear so smart and perfect yadda komin ilimi, tarbiya,wayewa ,iko da kyaun mace da kyar take fita a tarkon su”so i urge my beautiful followers and readers to forget about who is right or wrong in this story my main motive is to let you know,so take the lessons analyse them into ur daily lives if possible.. daganan sai ka san yadda zaka sa kafan ka idan irin haka ta fado maka………writers note continued in next page27_

 

 

 

Ofical cat
[2/24, 07:17] ‪+234 802 646 5734‬: *????BRILLlANT WRITERS ASSO????*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™jan2019
????????
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
????????
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*

 

27

Daga isowar su suka neme wajen rabewa zuwa washe gari da safe
Don dukan su ji suke kamar basu taba ganin ta ba sai yau.

Sosai suke tuno da abubuwan da yafaru sau dayawa shikan sa baba babaji jikin sa ya bashi wani abu game da ita da ta zo din amma ya kasa ganewa .

Amma kuma bai taba kawowa saratu har zata rayu ta zamto hamshakiyar ya mace kamar sarah ba.

Cikin nan zaman nasu sageer ya nemo musu adreshin da zai kai su kai tsaye babban branch din su inda suke.

Ko da washe gari yayi sai suka shirya tsaf suka nufi nan organisation da niyyar su same ta.

Sam sun kasa hakura dukan su sun sanya aransu hala idan suka yi baki da baki da ita Allah zai rage musu wani abun.

Sai dai kashhh tun safe take cikin comittee na wani muhimmin meeting
Wanda ya dauke su dogon lokaci basu fito ba

Yau saura sati biyu wata gudan da suka bayar don su fara karban mutanen da suka yi registered don basu kulawa…

Su baba babaji Gaba daya a motsare suke kauyen ci da tambarin talauci da wahala shine ke haskawa a fuskokikn su da suturan su..

Anan ma da kyar masu gadi suka amince auka shigo harabar org din

Don duk wanda yaci karo da su bazai dauka ko ba roko ya kawo su ba…

Anan suka kai ciki suka tarar da securities.
Tun kafin suce wani abu,
Aka tsare su da tambayar ina zasu je anan,kuma meye kawo su?

Har bakin su na rawa suka bayyana wajen saratu suka zo..

Anan ma ba irin juya kansu da ba’ayi ba sabida wasu cewa suke basu san wata saratu anan ba

Babu irin bayanin da basu yi ba amma sai wasa da hankalin su ake.

Sosai ran sageer ya baci, cewar sa itace ta zo kauyen su fa kwanan nan..
Wasu daga nan sun gane ta amma don sun raina shigar nasu da yanayin nasu sai suke enjoying wasa da hankalin nasu.

Cikin haka, aka sake yin baki manya daga kasar waje.
Gefe su baba babaji suka rabe suna kallon ikon Allah.
Ba don ya danyi bokon nan ba da sai yace halan ma ba kasar nigeria yake ba.

Ko ena cike yake da gwarjinin wayayyaun jami’ai da kwararrun ma’aikata

Suna tsaye anan ba wanda ya sake tanka musu,sai dai ayi ta wuce su ana zaga su.

Ransu yayi matukar baci meyasa ko kadan basu da daraja a idanun mutane?…
Sun dauka ko a kauyen su ne kawai ake musu kallon haka ashe ko ina ma zai iya faruwa.

Bakin ciki ke cin kowannen su ga fargaban ganin yadda abubuwa suke tafiya anan.

Chan wajen karfe 12 rana abu yaki ci yaki karewa
Wata mata ce ma’aikaciya ta amsa su da cewa suje kawai su dawo yau sarah bata da Time….

Kuka baba babaji ya fashe da shi na takaici, ga shi tulin lokacin da suka dauka anan ba wanda ya basu ko kyakywan tarba bare wajen zama.

Ga azaban yunwa nacin cikin su duka,..

Abun da ya fi ci masa rai ma shine yana ji yana ganin wasu daban suna zuwa ana amsa musu a mutunce amma su ba wanda yake basa kulawar sa akan su

Hawayen sa sun ki tsayawa cikin tunani yace rayuwa kenan Wai har ni babaji ake wulakantawa akan saratu?

Ganin yadda sageer yake bashi baki akan suje su dawo goben ya sa security ya tunkaro su tare da ce musu su fita kar su jawo musu hankalin mutane….

Bakin ciki sosai ya ishe sa,..abun dai ya musu zafi sosai

Cikin bacin rai,baba babaji yace”
Da Allah tafi chan, bayan kun gama wulakanta mu? Mutanen banza mutanen wofi,inche dai nan wajen offishin saratu ce?
Kasan ni waye ma saratu kuwa?….sageer ne ya riko sa don sosai ya balle yana maganan cikin radadin zafin rai da bakar yunwa

Dariya aka fara masa musamman da suka ji yace ko ansan shi waye ma saratu?

Kowa yasan mahaifin saratu ya rasu,so what?
Wannan din bai wuce yace makabcin su bane a kauye,

Securityn kansa sai dariyar yadda mutane suke fassara bacin ran baba babaji suke cikin tsokana da raha..

“zo mu tafi baba babaji,wayannan ba su san me ya kawo mu ba?
Amma na tabbata idan saratu ta fito zasu san mu waye ne.

Lokacin idanun baba babaji sunyi jajir, yana bambami securityn na kan ce musu su fita kawai..har yakai su bakin gate….

Anan waje suka dakata yana share hawayen sa ,
Shikan sa sageer baiyi tsammanin ran baba babaji ya baci haka matuka ba.
Yace tashi mu tafi mu nemi wani abu muci,inyaso gobe ma dawo kamar yadda suka ce..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button