SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Da ya dago ya kalle sagir din sai ya fashe da Kuka yace saratu fa yata ce,amma ganin ta kawai sai na wulakanta wannan wani irin rayuwa ce?
Kaga shiyasa na nace zan zo nan ko zata yafe ni wani abun ya ragu da ga cikin bakin qaddarar dana jefa kaina aciki.
Sosai sagesr yaji tausayin sa gashi kuka yake har jikin sa na rawa shikadai..
Duk suna wannnan yanayin yazeed da tuni ya hango su sai ya tsaya lura da me suke ciki
Musamman da ya dago fuskan baba Babaji,ai ya ma taba alkawarin zai sa akawo sa offishin sarah amma bai samu daman yin haka ba
Cikin ransa sai ya fara tunanin kar dai yaji shiru ne ya sa ya zo dakan sa?
Kai amma ban kyauta masa ba..is not easy mutum yayi rayuwar sa cikin ciwo nadama da tsangwamar mutane..
Gashi ni da na masa alkwarin samun sauki ban kula ba..
Da haka ya sa ya sauko cikin azama yayi kansu,
Sosai yaji wani irin gani su anan din.
Yana isowa suka mike tsaye, zasu gaishe sa sai shi ya riga tanbayar su da cewa yaushe suka zo?
Shikam sageer bai gane sa ba amma baba babaji ya so ya fahimci fuskan sa.
Yaxeed Yace” kamance dani ko?
Nine nazo wani lokaci nace zan sa akawo ka offishin sarah,
Murmushin bazata baba babaji ya sake Yace Allah na gode maka,nan ya gaya masa cewa ai saratun da kanta ta zo amma abunda yafi bata masa rai yanzun wulakancin da aka musu ne akan ganin ta.
Yazeed ya dauka ko duk kauyanci ya sa suke refering dinta as saratu,
Sai ya ga kuma sun nace suna magana akan haduwar su da ita,yanzu haka ma rokon sa suke yi ya taimaka su ganta..
Basu damu da yunwa ko gajiyar da ke damun su ba muddin zasu hada ido da ita..
Tuni wani abu ya basa maybe is a personal issure… amma sosai yake so yaji don ya sha mamaki kuma kansa ya daure matuka”
Me hadin sarah da wayannan? How did thy know her,ko tayi musu alkawarin wani abu ne? To meye wannan din..
yasan dole sai ya yaudare su kafin ya san kan zancen,sai yace kuyi hakuri tukunna kunga yau sarah tana da manyan baki bazai yuwu ku ganta ba,
Amma ni zan je daku ku huta ku ci abinci gobe da kaina zan sa sarah ta saurare ku..
Murna akan murna baba babaji har da rusunawa kasa wajen sa ma yazeed albarka mai cike da godiya da karamcin nasa
Haka ya sa su a motar sa ya kaisu wani karamar hotel, anan ya odering musu abinci mai shegen dadi da tsada kaji ne nasha nasha mai qamshin dadi ga abubuwan jika magwogro.
Yana daga gefen su suka haura kai ham ham kamar dan wuta yaga gasashen nama,
Baba babaji naci hr zufa na saukowa akan nasa kamar wanda ke cikin Shower..
Duk yana kallon su, sai hiran santin suke
Time to time yana sa musu baki
Cikin salo yazeed din yace amma da cahn kasan sarah ne ko?
Anan ba wanda yake zuwa ganin Ta kai tsaye sai akan lokacin da ta basa…
Baba babaji ya dago a sanyaye ya dube yazeed yace “nasan ta sosai..shiyasa ma kaga na zo don na same ta.
Saratu ai yata ce…
Sageeer yace haka ne, yar sa sace ,ai wannan daka ke gani oga, shine mijin mahaifiyar saratu
Bayan mahaifin ta ya rasu,
Cikin tsananin mamaki yazeed yace ohhhhhhhh
Kenan kai mijin maman sarah ne? Amma ai mahaifiyar ta bata da wani miji a yanzu haka..
Ban fahimce ka ba.
Baba babaji Yace ai mun rabu ne,
Yazeed yace ohhh ayyah..
Toh meya faru ko zaka iya fada min,?
Kar ka damu aiki na ne taimako zan taimaka muku..
Su kan sun yarda da yanayin yazeed beside shekaru aru aru kenan babu wanda ya dube su da idon rahma har ya kashe kudin sa akansu ya basu muhalli da abinci sai yau..
Gashi har ya na cewa zai taimake su…rabon baba babaji yaji wani mutum na daban haka kawai yace zai taimake sa ai ya mance.
Sai abun ya taba zuciyan sa anan ya taso ya zauna shi da sageer..
Nn Suka shiga bada yazeed labarin saratu da ummahn ta in è best way thy can..
Sai dai cikin nuna nadaman su da neman yafiya suke bayanan nasu,
Sannan suka tabbatar masa da cewa lallai sarah itace saratun su.
Mamaki da rudani ya hana yazeed magana,sai baki yake basu yana gwada masu babu komai shi xai taimaka
Amma cikin ransa is full of questions .
Musamman fannin ta ya akayi sarah ta kufce ma wannan mummunan qaddara ta har ta zamto haka?
How did she make it? Yasan dai a waje tayi karatu kuma mum din ta na da sana’ar ta da kudin ta but how did thy make it?
Amma ace a haka suka taso?Toh ya akayi suka samu duk wannnan rayuwar?Sata sukayi ko karuwanci?
ai yasan cewa ummahn sarah har yau bata sake aure ba bare ace arxikin mijin ta ne,but how?
Kenan akwai boyayyen sirrin sarah da ba wanda ya sani sai ita..
Ya dade yana kawo tots daga bisani yace ma su baba babaji,
Kar su daga hnkalin su,
Shi yasan yadda zai yi suga sarah amma su daure su bashi zuwa gobe,
Godiya sukayi ta masa sai dai hankalin sa bai ya wajen su,
Tunanin kawai yake yi kala kala akan sirrin rayuwar saratu daya dan ji yqnzu…
Now he knows where her abject inspiration to help the needy is coming from.
Babu shakkka jajircewar saratu ya samo asali ne daga ciwon qaddarar ta dake makale a zuciyan ta..
But this is not the end yana so yaji ya akayi ta cimma burin ta har tayi,ilimi da kudi haka..
according to baba babaji cewa yayi da ya fara nadama ya shiga neman su a da chan ance masa sun tafi birni a motar kano.
Kenan a kano saratu da ummah suka yi kudi?a kauyan cin nasu??,damn but they r oll women…thy r suppose to be weak,inma ba haka ba ai zai yi wuya ace mace ta shiga wannan halin sannan ta mance da shi so easily har ta tashi ta daga rayuwar ta..
Sai ya sa aransa dole sai yaji sauran kwaf kwaf din sannan ya samu nitsuwa
A daren daya koma gida sai ya tura makudan kudi ma wani mai suna zulkhi cewar sa ya hau jirgi ya taho su hadu gobe a gidan sa.
Anan su baba babaji suka kwana,
Washe gari da sassafe yazeed ya kawo wani agents dinsa ya hada su tare yace akai su ga saratu..
Daga nan shi kuma ya wuce wajen zulkhi bai bari ma sarah ta san da shi ba..
Anan ta karbe su ba yabo ba fallsa ta kaisu wani wajen daban suka samu zama.
Kamar a mafarki suke ganin realityn su,ita kuwa bata boye musu ba ta fada musu itace din,..
Duk dama ta sha mamakin ganin su amma sai bata nuna ba,..
Anan duk suka dada warware mata duk munafurcin Da suka mata cike da nadama da neman yafiya
Suka roke ta don ta yafe musu..
Dukan su kuka suke yi har da ita don Tasan za’ayi hakan ya sa ta sa suka bar office din gaba daya suka je wani waje.
Bayan sun fahince juna ta kaisu gida har wajen ummah,anan ma suka nemi gafarar ta.
Dan itakam ummah addini yanzu ya shige ta sosai halayen ta ko da ba ace ba kasan imani ya ratsa zuciyan ta ya mamaye shi..
Duk da bata iya hade baqi ba,takan zauna ta kunna karatun qur’ani tana ji yana mata dadi sosai.
Tsaban naci har ta haddace wasu surorin cikin sauki ta haka.
Kuma zata iya daukar fiye da awa 4 tana kallon wa’azin malaman nan bata gaji ba.
Gashi dama da saratu ta samu cin gaban rayuwa sai ta rage mata zuwa aikin ta, yanzu haka managers din ta ke lura mata da gidan gonan ta da gidan kajin ta.
Su baba babaji A duk yadda suke ganin saratu tayi musu karamci bai kai yadda suka ga ni wajen ummah ba,don sosai ta mance da komai sai ma nasiha mai shiga rai data yi musu..
Haduwan su da ummah ya dada zafafa zafin nadaman da baba babaji keji aran sa….lallai ya kasance hasararre ya kaskatar da rayuwar gambo amma Allah ya nuna masa cewa gambo ce mai nasara tun a duniya.