SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Kwana biyu suka yi anan gidan su saratu cike da goma na alheri suka koma gida…
Sarah ke tabbatar masa da cewa idan sati biyun ya cika zata sa a dawo da su a fara masa jinya…
Tsaban dadin yanayin da suka samu yafiya cikin sauki ya sa suka mance da yazeed don haka basu ko fada ma sarah cewar sun hadu da shi ba har aka rabu
Ita kam dama yanan nade a zuciyan ta amma kwana biyu data ga kamar ya share ta ya sa ta dan bada hankalin ta wajen ayyukan dake gaban ta
Amma yau da su baba babaji suka tafi
Tana Dawowa sai ta wuce straight offishin sa ko zata lallaba sa taji meye matsalan ,
Amma da mamakin ta sai ta ga offishin sa a
kulle
Ta sake kiran layin sa shiru shi ba off ba shi ba ringing ba.
Ko da ta tambaye farida secteryn sa ce mata akayi
Kwana biyu sukan su ba su gansa ba kuma basu san inda yake ba.
*Writers coments continued*
_samarin shaho is also to ladies that have everything in life but give less important to their god,sarah na daya daga cikin wanda suka mance da wani muhimmin bangare na rayuwa…misali, Ku dubi yadda sarah take mance da yin sallah akan lokaci idan suna tare da yazeed,ku fada min meyasa hakan bazai faru da ita ba?…yan mata ku tsaya ku kalle rayuwar sarah nan gaba… its very important….”kenan dan wani mummunan qaddara ya faru da kai arayuwa sai ka sa burinsa agaban ka fiye da komai har kula da ubangijn ka?toh wa zai taimake ka akan mugayen maza kamar samarin shaho?wayon ka ko ilimin ka?..,Kuma ina kira da kar kuyi ma labarin hanzari ku dan sassauta min i want to give more pages,nasan labarin baida dadi sosai amma sakon dake ciki is kind of more realistic than fictional#relax fans im also with you on this#sakallahu khairan,wah saka biljannat awaiting ur heartouching coments always????_
*Official cat*
[2/24, 08:55] +234 802 646 5734: *????RILLlANT WRITERS ASSO????*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™jan2019
????????
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
????????
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*
_28.._
Abun bai daga mata hankali sosai ba, sabida tasan maybe yar fushin nan Ne daya saba idan bata bashi attention dinsa ba,..
Hakan ya sa ta koma bakin aikin ta tana yi tana gwada layin sa amma babu wani sauyi,
Haka har ta tashi daga aiki ta koma gida bata ji shi ba.
A chan bangaren yazeed kowa haduwar su da zulkhi ya sa ya tambaye sa yadda za’ayi su samu tarihin sarah da mahaifiyar ta a garin kano shekaru da suka wuce.
Ya nuna masa hotunan sarah da na ummahn ta,
Sannan ya bashi dan detail din da ya samo daga binciken sa akan ummah da shekarun da ummah ta zo lagos.
Toh shi zulkhi shiya binciko musu cewa ai gidan kaji da gidan gonan da umma ta mallaka na shahararren Mai kudin nan ne alhaji abdul azeez shayal…
Daga nan yazeed ya sha dammara suka wuce kano ba bu wanda ya sani,suka shiga neman diddigin labarin ummah dana saratu..
Da kyar da wahala suke samun bayani daya sabida rayuwar su sunyi shi ne a cikin sirri wanda akalla sahura ce kawai ta san komai..
Amma da shike abubuwan mamaki da yawa sun faru, a ko yaushe idan wani sirrin ya fito sai ya dada sa ma yazeed din son yaji karshen bayanin..
Yanzu haka har kudi ya biya ana nema masa inda zaiji gaskiyan lamarin rayuwar su.
Anan kuma lagos sarah day by day tana shiga tashin hankalin rashin samun yazeed
Tunani dayawa ta kawo aranta nacewa ina zai je wanda har iyayen sa basa zu sani ba
Don ta tambayi kowa har gidan sa taje amma shiru babu shi ba labarin sa
Gashi yau ya cika wata guda chasss bai dawo ba.
Shikuwa da sannin sa yake yin haka ,so yake ya kwaba mata lissafi
Don shika dai yasan me ya ke shirya mata one big time…
Haka ta lalace da tunanin sa, bata iya cin abinci sosai bare bacci,
Saukin abun ma shine yanzu hapsy ta dawo nan branch din ta..
Ita kanta hapsy tausayin sarahn ke damun ta
A ko taushe da duba wayar ta sai taga dialled calls din yazeed yafi a kirga
Har ta gaji ta sa ta gaba tace,sarah dan Allah ki sassauta makan ki mana,
Ai inda ya damu dake bazai bace miki rana guda kiyi ta neman sa baki same sa ba..
Please this is getting too much baki ganin yadda kika dawo ko?
Abun na damun ta sosai duk dama kullum idan hapsy ta kawo magana bata tankawa yau kam sai taji dole ta sawwake ma zuciyan ta ko zata samu saukin zafin da yake mata.
Tace hapsy wallhy na kasa ne,kaina ya daure
I just cant hepl it na shaku da shi sosai…sai ta dan fara sauke hawaye..
Hapsy na shiru itama din tunani take yi,chan ta taso ta zo kusa da ita ta dafa ta
Sarah”?
Dago ki kalle ni,
A hankali ta dago.
Tace kina son yazeed ko?
Wasu hawayen ne suka taro mata lokaci guda tace eh hapsat ,ena son shi..kuma nasan shima yana so na
But we dint make it official
Hapsat tace ohhh crab .. now thats your problem,ya za’ayi ku rinka azabtar da kanku haka? Wai shin baku aminta da son dakuke ma wa juna bane ko yaudarar kanku kuke da bazaku furta shi ba?
Idan dukan baku bar wannan wasan banzan ba fa zaku yi illah ma zuciyoyin ku.
Cikin kuka ta ce to ni ya zanyi hapsy,nice zan ce ina son shi ya aure ni,ko shi zai fara fada min haka.?
I just dont get him…kinsan kuwa ranar da na vata masa rai ma haka nayi ta neman sa ban same sa sai daga baya ya zo yana gaya min wai bazai iya jure rashina kusa da shi ba ne”
I think don ban samu time dinsa sosai kwana biyun nan ba yasa ya tafi ya barni,this is tooo much for me
Yau kusan wata kenan Ban sake ganin sa..
Im feeling the pain i love him sooo much..
Kuka ta keyi sosai har da kife kanta akan teber gwanin tausayi..
Itakan ta hapsy yanzu tana cikin rudani
To wannan wani irin salon soyayya ne sarah ta dauka makanta..
Nan dai ta shiga rarrashin sarahn tana bata baki har ta nitsu tare da bata karfin gwiwar cewa tabbas akwai babban dalilin da yasa yazeeed yayi haka
Idan kuma ta yadda da yana son ta tayi hakuri ta bashi dama.
A cewar hapsyn maybe yana cahn yana shirya rayuwar su ne yadda idan ya dawo sai taga komai ya wuce..
da haka ta samu gwarun gwiwa
Amma sai dai kamar ko wani rana kara mata zafin son sa ake yi aranta
Kewar sa duk sun nakasa hanyoyin jinin ta,tunanin sa ya gauraye brain din ta..
Sometimes ji take kamar ta hadiyi ranta ta mutu
Da bakin cikin rashin sanin inda yake da dalilin sa na boye mata..
Haka rayuwar ta kasance
Hapsy ke jan ta da nasiha da shawarwari har ta samu tana sakewa
Kowa anan offishin sai da ya gane cewa rashin yazeed sosai ya taba walwalan sarah.
Wasu har tunanin yadda zasu faranta mara rai suke ganin yanzu sam bata samun peace of mind.
Shikuwa yazeed cikin wannan kwanakin suka bi hanya hanya har aka kaisu gidan sahura na da chan.
Anan aka basu labarin zuwan su da rayuwar su, hatta yadda akayi raping ummah agidan alhji sabo ya sani..sai dai suma cewa sukayi basu san inda suka koma ba
Har sai da suka hadu da wannan saurayin da da chan yake zuwa wajen sahura,
Shi ya basu labarin cewa ai ssa danjuma shi sukayi ma aiki
Yasan shi amma baisan inda yake ba yanzun
Daga nan su yazeed suka shiga neman adress da information akan ssa danjuma