SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

In the process suka gane ba mutumin arziki bane, sannan ga sana’oin sa.
Anan yazeed ya san ummah tayi aikin strip club tun kafin ma yaji daga bakin ssa danjumA.
Toh aranar da suka hadu da shi,.aranar yaji sauran sirrin saratu da ummah don kuwa yayi playing cards din sa sosai akan ssa danjuma har ya samu jin Tun daga farkon haduwar sa da ummah
Da duk wani taimakon da ya mata a rayuwa ita da sahura
Sai dai iyakan sa daya hada ta ogan sa bai san ya suka kare ba….
Shima yazeed anan ya dakata da jin labarin nasa sabida jin ance ai alhj abdul azeez ya mutu
Samun wani information akan sa kuma zaiyi wuya
Tunda har shikansa Ssa danjuma bai sani ba…
So, yanzu yana da masaniyar duk wani rayuwar ashah da zubewar mutuncin da ummah tayi akan sarahtu
He just concluded dat tunda har ummah zata iya rawan kan karfe a club ana bata kudi..
To tabbas kwana take yi da alhj abdul azeez
shine ya bata dukiyar da take juyawa yanzu..
Its so clear to him,
Kenan shiyasa ummah ta samu share akan gidan gona da gidan kaji,kenan ummah karuwa ce?
Abun na matukar shakin kwakwalwar sa
Yana jin Tunda aka haifesa bai taba jin yanayin mamaki da tsanstar nazari kamar na yanzu ba
A ko wani dare sai ya yi tunani daban daban akan su..
Sai dai bai kyautata tunanin sa akan su ba ko kadan
Musamman rayuwar ummah na baya..
Ya dauki lokaci mai tsawo yana shirya kansa da plan dinsa wanda daga shi sai zuciyan sa suka sani.
Sai dai wani abu na damun sa,sosai yake jin kamar zuciyan sa tana tsananin kewa da son sarah..
Wani bin idan ya kawo tunanin haka sai ya sha giya akai ya fice hankalin sa Yayi ta dariyar da shi kadai yasan ma’anan ta
Yana nan agarin kano abokan sa kuma suna sane da hakan amma ba wanda ya sani bayan su
A yanzu haka ma shiri yake na tarban su ranar juma’ah ya gayyace su akan Zasu zo masa weeknd Dukan su.
Faisal ne mafi kusanci da shi, dan gidan senator ne
Shine kuma yafi comunicating da sarah
Akan bacewar yazeed din
Sai yaji nata sai yaje ya fada ma yazeed din abayan idanun ta….sometimes har rercoding zaiyi ya tura masa yaji suna dariya..
Sukan su sun sha masa tanbayar ko dagaske yake akan maganan sarah..
Amma har yau yaki fitowa fili ya gaya ma kowa mai yake tsakanin sa da sarah na asali
Bare kuma nufin sa.
Bayan azuciyan sa shikansa fighting yake da yanayin rayuwar sa da sarah amma yaki ya fuskance gaskiyan hakan
Labarin sarah dayaji abun al’ajabi ne kuma abun tausayawa ne,.but sai yaji babu hakan aransa.
Bai san zafin abun ba sabida a labari kawai yaji,bai san me ake nufi da qaddara ba sabida mummunan qaddara bai taba rabar shi ba bare iyayen sa..
Bai san me ake nufi da bakar talauci da cin zarafin mutunci ba sabida rayuwar sa tun da ya taso acikin girmamawa da karamci ya ke ganin sa
Sai ya kasa bada rayuwar sarah da ummah wannan uzuri..
Gani yake suna da laifi akan dukan abunda ya faru da su
Infact su suka so hakan ya same su…
But how cud he be this judgemntal
Hmmm duniya kenan,dama bature yana cewa” ppl only judge you from their own point of view ” ba haushe kuma yace
Yadda mutum yake kallon kansa haka zai kalle wani..
Toh ranar friday da su faisal suka zo kano wajen yazeed.
Shikansa yaji dadi sosai sabida tunanin sarah ba wai yana barin sa bane,.amma kullum acikin shan giya yake din ya karya ta cewa ya kamo da son yar karuwa.
Daga nan kuma tana nan tana fama da zaren son sa dake ninkuwa bayan kowa ni jan numfashin ta a duniya.
Hotun sa ne gaban screen din wayar ta
Cikin dare kullum sai ta karance chats din su tsaff ta bi tana karanta tex messge dinsu tana yi tana hawaye tana murmushi alokaci guda cike da kaunar sa..
Yau yana neman cika wata guda da sati..
Zaman su faisal anan suka kusan sauke gidan da surutu da kide kide da shaye shaye…
Anan ana shan shishan nan hayaki da warin giya ya gauraye su ana ihu ana surutu
Wasu na buga game ana ta shagali.
Faisal ne ya Kawo zancen sarah,sabida sun gama lura da yazeed a dame yake amma sai yana boye wa da buguwar giyan daya sha.
Don su sa shi dole yayi magana suka haura masa dukan su da tsiya
Mai ban haushi
Cewar javeed soyayyar sarah ya sa zaki buya abun mmaki
Abun tun yana wasa har ya fara dawowa na bacin rai
Sai Ya musu bayanin shi ba wata sarah a zuciyan sa amma sai tunzira shi suke yi
Musamman faisal da ya sake ya na bayyana wa gaban kowa don suji maganganun da sukeyi da sarah a wayah cikim kwanakin nan
Sai ya zamto sun maida shi kamar mahaukaci
Ransa yayi matukar baci da suka daura masa cewa lallai soyayya suke da sarah bai fito fili ya gaya musu ba..
Haka ya sa ya sa makudan kudi har kimanin millliyon 20 akan bet mai taken
“Game of love”
Sun sha mamakin da sai da ya sa suka yi shiru suna jin sa..
Yace” nan da sati biyu game din zai kare
Zai gwada musu abun mamakin da su kansu bazasu taba tsammanin sa.
He wll become a lion in the eyes of all ladies
Idan haka bai faru ba ya basu kudin daya sa yanzun duka.
Jin haka ya sa suka amince, amma sunsha mamaki…
Kowa kuma sai ya shige kogin tunanin me zai faru?
Good or bad?
Me zai yi ma sarah..
whats is the suprise worth 20million
A haka suka bar kano da zullumi gashi ko faisal da ya same shi in private sukayi magana
Yaki sanar da shi me yake shirin nuna musu akan sarah..
Su dama damuwar su kawai su san gaskiyar sa amma Basu da wani nufin na daban..
Haka dai suka rabu ya kuma sanar da su ranar dawowar sa lagos..
Anan bangaren sarah kuwa,ba laifi sai da raman rashin sa ya nuna
She became quiet and cold
In kaga tana magana toh hapsy ce ta zo ta same ta..
Agidan ma ummah sam ta dena gane mata
Ita kanta sai da ta soma tunanin rage haddarin son yazeed daya addabe ta don ta samu nitsuwa
Ya mata wahalan sosai wajen yanke wannan hukuncin amma dan dole ta bar komai ma ranta tana dada kawo wa cewa..
Hala akwai dalilin daya sa ya bace..alherin sa kawai take roka wajen uban gijin ta yanzu.
A ranar data soma sawa ranta zata cire yawan tunani
Ta fito cikin shirin ta mai kyau da tsari tana tafiya cikin sanyi da rigima
Dai dai kofar shigan ta office tana daga ido suka hada ido da shi……
Lokaci guda ta tsaya”Ji tayi kamar zata sulale kasa tafada don mamaki
Lokaci guda jikin ta ya fara rawa da kansa
Ta kure shi da idanun ta tana sauke faffadan murmushi
Sai ta rasa Murna zatayi ko kuka
Ihu zata tsala ko dariya zata yi?
Shima tsimewa yayi yana duban ta,shikam sai da ya sa hannu ya share dan guntun hawayen sa..
Basu da wani nisa sosai
Amma bugun da kirjin ta take yi bai hana shi gane wa
ba wanda ya tanka tsakanin su sai aukin murmushin da suke aikowa juna…,
ta dade da sumewa cikin idanun sa tana kallon murmushin sa mai cike da kalamai da yawa
Shikuma yana duban yadda gabobin ta suka taso gaba daya cikin tsananin farin cikin ganin sa.
A take ta rugo aguje tayi kansa tare da sake wasu zafafan hawaye.
Ko da ta fada jikin sa taji ya rungume ta sam sai ta fashe masa da kuka mai shiga zuciya…
*To waye wannan din?*
*Official cat*[2/2, 22:31] SURAYYAHMS????: *????BRILLlANT WRITERS ASSO????*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™jan2019
????????
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
????????
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*