SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

“Sai dai kashhh rashin lpya yana sanda na a hankali ,
nonowa ne sai zurr zurrr suke yi ta ciki sun kumbura duk ban kula ba kuma ban damu ba sai hidima na nake yi..
A ranar da ka kawo ummah gidan sarkin kurwala Chan da yamma akayi kiran baba babaji a gidan maigari
Anan aka soma magana gaban ummah da shi baba babaji da dogarai guda uku akan lamarin.
Umma na tun anan ta soma gane waye babaji
..don sosai ya bayyana cewa bai san da tafiyar ta bama,shima ai nemen ta yake yi…babu irin karya da cin zarafin da baiyi ma umma anan ba . .ummah na rantsuwa shima yana yi.
Ganin kamar ba za gane asalin kan gaskiyan zancen ba
Yasa Sarkin kurwala yace bazai saurare maganan shi kadai ba suje gida nan da kwana uku zai tara mutane ayi sharia tare sa kashe di don a koma ja kunnen masu hali irin na ummah na.
Ran sarki ya baci sosai yace bazai lamunci mace marar tarbiya da mutunci agarin sa ba..
Wasikar hakuri shima ya rubuta ya aika ma sarki hammayo ya kuma tabbatar zasu dauki matakai nan gaba akan haka..
Ummah taji haushi musamman da ta fahimci dukan su wajen sunfi daukar maganar baba babaji akan nata
Da kuka ummahn ta iso gida ,..ta ma kasa hakuri don zuciya ya debe ta sosai tun daga bakin hanya suka shiga cece kuce da baba babaji abunda ba asan ta da shi ba kenan Tsawon zaman ta agarin nan..
Gashi dama mahaifin ta ne kawai gatan ta wato marigayi hamma aliyu mahaifin ta wanda tun bayar zuwan su garin da mahaifiyar ta ta rasu shike tsaya mata…
Yanzu bata da kowa sai ita da Allahn ta din hakan yau babu wanda ya shiga ma umma fadan ita kadai take neman kwace makan ta yanci…
Baba babaji kuwa dadi yaji ganin ya cunkusa mata bakin ciki ya gulla mata sarkaken tarko….
gashi ya sa yau ta kasa hakuri suna tahowa tana masa debar albarka akan Muzanta ta dayayi da karyan da ya hada mata awajen sarki..
Ko ajikin sa don shikam Dadi abun yake masa tana hauka a idon jama’a ana dada bata rashin gaskiyan lamarin
Cikin ransa Ba abunda yake sai Dariyar mugun ta har suka shigo gida
“Churrrrr akayi akan su kishiyoyi da yayan su don an cika gidan tam dama ana shirin bikin Sauran yayu na..
Anan a tsakiyar gida Kowa saida ya gaya
Ma ummah bakaken maganganu da habaici iri iri akayi mummanan sa’insa face face,
tun umma na kuka har ta bushe idanun ta tana amsa ko wacce
Shegiya a cikin su ba kunya ba kawaici.
Ina makaranta a lokacin zazzabin dake sanda na shike sani yawan bacci da shegen tsitt da yawu Yau ma har aka tashi ban samu na dafa na iso gida ba Sai da na dan huta da kyar dai na tarkata kaina na kamo hanya..
A Lokacin da ake ci ma umma mutunci a tsakar gida baba babaji ya sabule yayi waje ya barta da matan gida kowa saida ya gaji ummah bata gaji ba. .
anan na zo na same ta
Ban tsaya jin wani hayaniya ba na taho muna hada ido da ummahn da hanzari na zo na fada jikin ta ina fashe da ruddaden Kuka.
Anan ne itama ta dawo hayyacin ta ta kamo ni nan take jikin ta ya soma rawa tana neman yin sanyi….
Kallo ta bini da shi kamar wacce bata taba jin Nayi irin Wannan kukan ba sai yau.
Tace saratu? Kar ki bari ki ji abunda suke fada karya ake min saratu
Cikin kuka nace kar ki damu ummah bazan taba yarda da hakan ba
Wani wawan Shewa aka buga a tsakar gida baba ladidi da group din ta sai dariya suke kamar suna kallon wasan kwaikwayo,
“Suka ce Kwarya tabi kwarya ana jan wuyar rakumin dawa a gari sai ga dansa ya shigo A ka kwashe da dariya ….
Ja na daki umma tayi bata kula su ba ni kuwa tsaban zuciya
Ban tsagaita kuka na ba tsawon lokaci har saida ta rufe ni da fada mai dauke da tashin hankali da firgici…
Tashin hankalin da ummah ke ciki yasa gaba daya sai naji nauyin gaya mata abun da ya Faru tsakani na da baba babaji..
gashi dama abunda nake shaukin gaya mata ke nan amma duk sanda na dauko hanyar fada sai na tarar da ita cikin tsananin jimami
don kuwa a cikin dan kwana ukun da sarki ya bayar hatta makaranta banje ba, kullum sai anyi fada da hargitsi da ita kamar gidan zai dage haka ake masifa da mu..
Wani bin tsaban haushin wani maganan idan ya gulle ta sai ta fita neman baba babaji
Gashi ya buya ya dena nuna kansa ma kwata kwata a waje anan ne ma ta san cewa dagaske inna wuro na raye tana kuma family house dinsa tare da sauran matan sa
A nan ma sai da aka tada zaune tsaye sa ummah ta sake maimaita abunda ya faru ko da zasu fahimce ta amma hakan bai faru ba
Karshe ma a hannu a hannu aka dawo da ummah kamar mahaukaciya tana surutu.
Sanadiyar kokarin bin gaskiyar ta ya sa Duk garin sai aka daura mata laifi aka ce itace batada mutunci..
bata da gaskiya ai baba babaji baice komai ba itake tada hankalin jama’a..
Babu wanda Ya taba tsaya mata in ana zagin ta ana cin zarafin ta amma kowa yana bada muhimmaci sosai akan reaction din ta da zatayi don ta kare kanta..
Ranar da kwana uku suka cika da asubahi da azabbaben amai na tashi kamar zan cire hanjin cikina na..
Sosai hankalin umma ya tashi sosai don ita ta zo kaina..
sai yanzu ne ma take kallo na da kyau take
Gane yanayi na
Don dama Sosai jikin ta ya dan bata kamar ena dauke da juna biyu amma dai tayi saurin dannewa tana tayani kintsa kaina..
Kaina na kasa ina kan Jin Abubuwa da dama na ci na a rai nan na fashe da kuka mai radadi
“Ummah Tana dago ni na shiga kukan da dan sauti ina rawan dari gaban ta..
Tace Saratu? Me ke damin ki dama baki da lpya ne ? Cewar Umma tana kure ni da ido cikin dauriya.
Ina sane da yan labe dake jin mu amma haka na cire komai araina na mata bayanin komi daga tushen sa ban boye mata abunda ya faru ba koda na miskala zarratin daga abubuwan danake fuskan taba har yanzu
Umma ta rike ni gammm amma bai hanani jin karkarwawa da tsuman da take yi ba.,
Magana take so tayi amma muryan ta ya sarkafe yana fidda i i na tsaban bacin Rai ji kawai nake tana” b..aaa. .baji,
Dum umm..a ta yanke jiki ta fada gaba na summamiya..
tun kafin Na tsala ihu aka yo chaaaa akan mu jikin umma na fada ena bata hakuri ena kuka..
Ruwa aka dan yauyafa mata kafin ta farfado a kasale Ta kalle ni gaban ta duk na gama fita hayyaci na kuma ban fasa ba..
Ido tabi kowa da shi batace uffan Ba tayi yunkuri ta tashi ta kamo hannun na muka shige daki…
Munaji ana rade raden maganan ana raba gulma a tsakar gida..
A kan gado ta zauna Hawaye kawai take yi agaba na ta riko hannu na sai sheshheka nake tace”Allah sarkii diyata ki yafe ni, kaico na saratu, ni nayi silar shigar da ni dake cikin wannan mugun rayuwa kar ki sake daura makanki laifi ni na jawo mana fitina arayuwan mu dana auri babaji,.
Gashi ya lalata na nawa ya lalata naki tace sarahtu Inaga fa babaji kamar ciki yayi miki.
Cikin wani irin bugun zuciya Na dada kame hannun umma na fashe da kuka mai tsumayin radadi da
Tashin hankali..
Wayyo Allah na imma na shiga uku Ciki fa kikace ummah?
na daura hannu na akai hawayen na har turririn zafi suke fiddawa ena kan kuka ina cewa na shiga uku…
Tausayi yasa Umma ta jawo ni jikin ta amma
Shiru ne ya ratsa wajen
Aka rasa wanda zai dakata da nashi kukan kuncin da kyar ummah ta dago ni ” idanun ta sunyi jajir tausayin ta tuni ya gauraya zuciyata naji inama ace mutuwa mutum ne da nace ta dauke mu baki daya mu huta da duniya…
Ummah ta shiga shafa fuska na cikin kulawa ” yace kiyi hakuri saratu, duk da ni jahila ce yau nasan mutum ne kawai bai wuce qaddarar sa, kin kare kanki a bayan ido na ,nasan da alokacin ma ko kin gaya min ba shi zai hana ya sake fito da wani mummunan hanyar cimma burin sa ba, nima nan kinga abunda ya min ban aikata komai ba amma yanzu na dauka abubuwa da dama akaina…