HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Ki dauka duk wannan ya faru ne a idon saurayin nan yaga sirrin su yasan me suke ciki da bakar qaddarar su, da yagama fahimtar rayuwar su
Sai yace zai aure yar matan nan.

A dayan bangaren kuma akwai wani shima kamar wancan saurayin ne, sai dai shi bai san komai akan su ba amma yana iya yin komai dan farin cikin su, sannan ya yarda da su..mind you bai san sirrin su ba..
Sai ya fito da cewa zai aure yar matan nan..

Toh acikin wayannan biyun
” wanne kiga yafi rufin asiri yar ta aura

shin wanda yake da hankali amma yasan sirrin su?
Ko wanda ya Ke da hankali amma baisan sirrin su ba?

Hawaye ne ya sauko mata sai ta share ta kalle hapsyn alaman tana jiran amsa

Shiru hapsy tayi tana lailaya gajeren labarin,ace mahaifiyar ki mayya barauniya marar tarbiya,?

Kai Tsakanin harshe da hakuri ma akwai sabani
Kaiiiiii anya wata rana bazai zama abun gori ba?what if aka zo aka samu misunderstanding? Soyayyar zai iya sauyawa ya zamto kiyayya kenan..

Nan hapsy ta dago tace inaga mai hankali wanda bai san sirrin su ba ya fi cancanta..don kazantar da ba ka gani ba ma tsaftace.

Sannan shi mutum tara yake bai cika goma ba..

Duka kansu da zasu dace da ita sabida dayan shi yasan ita wacece amma yana da hankali…future kawai ake tunani akan sa

Amma wannan kuma bai sani ba,zai iya yuwa kafin ya zo ya sani ansamu kyakywar fahimtar juna agaba.

Da kyar sarah tayi ajiyan zuciya tace nagode hapsy

Ashe hukuncin da na yanke na kan hanya kema kin fada..

cikin rashin fahinta hapsy tace kamar yafa? Ni kwata kwata ban gane me kike cewa ba.
Whats all this sarah?

Tace babu komai barinje gida wajen ummah na i will have to talk to you later pls ki kira min catherine itama zan mata magana anjima..

Batare da ta jira ba ta dauki jakar ta ta wuce gida.

Bangaren mahfud kuwa alhj nafiu ne ya dauke sa suka je humanataran service a wata kauye su biyu da sauran officials din su

Hankalin su gaba daya na chan ana ta hidiman jama’a is like alhj nafiu yana so yayi retire ne ya dawo politics abunsa.

Ita kuwa hajiya billy sam sai bata jin dadin zancen auren yazeed da sarah ba,
Yanzu ne take kawo wa ita dama safeenah ce,

Don hankalin ta zai fi kwanciya ta kowani fanni idan hakan ta faru.

Ai bata taba samin safeenah da boyauyen hali ba, gashi iyayen ta ma sannanu ne anan waje ta bata da fargaba akan su..

Abun ya dan dame ta sosai amma tasan dole su ma yazeed abunda yake so..

Isowar sarah gida ta ajiye motar ta ta hauro ciiki ta samu ummah ta idar da sallah kenan tana adduoi

Shiru tayi daga gefe tana tuno da wayar da sukayi da yazeed na cewa zata fada ma ummahn ta maganan auren su shima ya tabbatar mata da yana jiran amsar ta ko a gobe ne sai adaura musu auren domin su dada toshe kofan zargin tabewar tarbiya da iyayen sa suka fara nuna mata
Jiyan.

Cikin mamaki ummahn ta dube ta, tace lpya dai saratu ya naga kin dawo da tsakar rana haka?

Tayi shiri cahn anjima ta sauke ajiyan zuciya ta taho gaban ummah ta rusuna

Hawayen ta ne suka soma sauka ta bi ta sunkuyar da kai kamar me neman gafarar wani mummunan laifi

Lokaci guda ummah ta daga hankali tana tambayar ta meya faru?

Da kyar ta daure ta riko hannun ummahn ta shiga bata labarin,tun ranar da ta sha giya ta fada ma mahfud sirrin su.. Da duk abunda ke tafiya tsakanin su ayanzun

Toh data zo kan labarin yazeed ne aka samu mtsalan ta so tafada zak zak yadda komai ya faru amma ganin heartbreak da tashin hankalin da ya riga ya bayyana akan fuskan ummah ya sa ta rage gaskiyan nata akan yazeed sai ta fadi shawaran data yanke musu..

Jikib ummah yayi sanyi da jin duk wannnan labari..

Tabbasss ta so mahfud niyyar ta ko da sarah bata fidda shi a miji ba zata sa ta tayi mata biyayya ta aure sa..

Amma jin ya san sirrin su ya sa ta shiga halin rudani itama”

Amma ai ya dade da sani shine ya rike bai taba nuna wa ba?
Cikin wannan nazarin ta dago ta tanbaye sarah

Sarahn kuwa idanun ta sun riga sun rufe sai ta ke kawo ma ummah nata tunanin a ganin ta tasan tayi musu kuskure kuma wannan kuskure shi zai rabata da auren mahfud ..

Ta nun ama umma tana tsoro din bata san ya zai kasance wata rana idan ya aure ta ba..

Da wayannan reasons din ta cusa ma ummah fargaban abin da zaije ya dawo akan mahfud..

Ummah Tayi bakin ciki matuka kuma tayi ma sarahn masifa wanda bata taba mata ba, don sosai tayi kukan jin abubuwa dayawa kamar shan giyar da ta taba yi da kebewar da take yi da namiji da sunan soyayya.

But She was left with no choice kawai sai ta sa albarka ma auren su da yazeed din…
Itama don ta huta

Tun daga wannan lokaci ummah sai ta shiga wani halin bakin ciki,..
Da shiru shiru tunani dayawa suna zagowa aranta

Meyasa har yau bata ji kamar mahfud ba shi bane mijin saranh ta..

Ita kuwa sarag Bayan samun fahimtar juna da sukayi da ummah sai ta sanar masa da cewa a shirye suke da ayi auren..

Har da murnan sa da dada bata alkwarin sa cike da son ya kauce damuwar da yake ji a muryan ta..

Sai yace mata insha Allahu jibi zasu zo da iyayeyn sa ayi maganan auren.

Yanzu gaba daya tunanin ta yadda zata kare musu ne da mahfud

Amma tasan dole ne ta gaya masa a cikin daren nan kar ma wani abu ya rude ta ta sauya tunani

So tun yana shigowa gari inda netwk yayi karfi yake ganin sakon text din ta alaman ta neme sa bata same sa ba

Sam sai hankalin sa ya kasa kwanciiya yasan dole akwai dalilin daya sa sarah ta matsa su hadu yau..

Tunanin haka kuwa har ya bayyana akan fuskanr sa ,ga yamma yayi sosai har aNmna neman shiga ishai
sai ya ce ma aljh nafiu su karasa gidan akwai inda zaije

Yaso ya ce masa ah ‘a a ganin sun gaji sosai gashi dama yana so suyi maganan yazeed din gaba dayan su asan abun yi ..

Amma haka ya hakura ya barsa ya wuce gidan su sarah..

Da shike ma yau ummahn ta bata shiru a daki tana jimamin abubuwa dayawa sai wajen yayi empty

Sarahn Tana daga daki jingine da kan gado tana sauke numfashi tare da wayar ta a hnnun ta,

Sai yanzu ta sami wanda ta ki amincewa da zabin ta wato catherine”

A duk salon data fitar da labarin sai da ta nuna mata dacewar ta da mahfud fiye da kowa a duniya …
Sai sarah ta dauka jawai maybe cath just dont wanna see him hurting amma ya zamo dole su tsaya haka..
Gani take qaddarar daya sa ta sha giyan data sha
Shi ya mata katangar karfe da auren mahfud..

Dadin karawa ummah ta amince…duk da ma jikin ta ya bata ummahn na cikin damuwa sosai
Akan haka

Da kyar ta tara courage din ta Ganin kirar sa ya sa ta sauko sanye da hijabi ruwan kasa babu make up a fuskan ta.

Haka kawai yaji wani iri da yaga yadda take sanyi sanyi, bayan sun gaisa sai yace mata lpya kuwa kika kira ni?

Ina ummah kuma fatan tana lpya,kiyi hakuri naje wani kauyen ne da dad din shiyasa bakiji ni yau ba..

A hankali ta gyada kai,maimakon ta dago ta fuskance shi sai bugun zuciyar da ya dadu ya sa ta fara sauke hawaye silently batare da ya sani ba..

Shiru ne ya ratsa wajen har sai da ya sake tambayar ta meke faruwa

Sannan ta dan sake sautin kukan nata wanda ya sa shi matsowa kusa da ita sabida mamaki

Yace haba wa nasan ba lpya ba,toh meyake damun ki?

Tana shiru sai kukan ta keci a hankali..

Ya yi tambayar duniyan nan bata amsa ba, sai ya soma tunanin ko fadan daya mata jiya yasa take soo suyi maganan..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button