SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Haka kawai ta hatsala ta soma tanbayar sa meyasa zaiyi referring dinta as friend bayan ba haka bane tsakanin su?
Tace ko ka daina so na ne mahfud?
Ya yi shiru yana kallon ta cos She was becoming more emotional and serious
…
Baice tanka ba Har ta gama bambamin ta sannan ya juyo ya dube ta…
Yace sarah mubar wannan maganan please tell me meke damun ki?mmmm ? Haka kawai zaki soma min masifa ni me nayi miki..
Haushi hakan ma ya dada bata, she’s actually annoyed and chocked up da tunanin kar ta rasa shi sai taga kamar shikam ma bai damu ba..
Sai ta hada haushin gaba daya ta sauke ma dan laifin cewa ita abokiyar sa dayayi idanun ta gaba daya suka rine tana neman taro ruwa..
Yaki ya nuna ya fahince ta har sai da tayi sanyi
…yace toh kiyi hakuri im sorry sarah bance haka da wani nufi ba abunda naga ya dace kawai na fada.
Arent we just friends? Ko dai wani abu daban ke bata miki rai pls tell me mana
Ta dube sa cikin shakurewan kuka tace ni ban sani ba we are not, im not your friend shima nafasa…sai ta bude motar ta fice ta barsa anan”
This is serious yafada a kasan makoshin sa
Hankali adan tashe ya biyo ta duk dama bayan ta bashi amma ya san kuka take yi…
Cikin damuwa da sanyin jiki yace sarah dan Allah ki bari ,pleass tell me whats hapening wai meye matsalar ne,.. ko dan nace miki friend dina shikenan nayi laifi?
Ya dan dafa ta a hankali sai ta juyo a dan birkice cos she can no longer hold back,…
Cikim kuka ta furta Mahfud kayi hakuri im sorryyy,i know i hurt you many times dan Allah ka yafe min dont purnish me for that pls,kukan take yi kamar me rokon ma rayuwar ta “pls i dont wanna be ur friend anymore i love you…ta karashe cikin shessheka
Dan Lumshe idanun sa yayi ya riko hannun t zuwa nashi, cikin rarrashi yace its ok sarah wannan maganan baiya wucewa awajen ki ko?
Tace toh ai kaine kake ce min wani friend asif we are just nothing to each oda.
Sakarcin nata sai ya basa dariya amma bai iya fitarwa ba Ya dada riko ta jikin sa kadan..
Yace its ok bana karawa…toh yanzu fada min me kike so nayi miki?
Ta dago suka hade ido cikim saltaccen shagwaba tace baka so na ko? …ka dena so na ko mahfud? No wonder mana…ka ki kace muyi auren again, ive been in ur place for 1month now amma sai kake share ni ..
Ya dan ja kadan cikin serious tune yace sarah pls stop this..kar muje nan wajen
Wai Baki ganin condition din ki ko?and u want me to say all this things to you
Yaushe kika gama warkewa daga haukar wancan wawar yaron are you even sure if u are over him yet?
idan da yana nan da zaki so ki mance da shi ki fada min haka…what change now?Ko dan kina gani na ne kike tunanin kin mance da shi…
Zatayi magana ya dajatar da ita dacewa
Sarah pleass relax ..im tired of aching my heart u have no idea what i went tro a wancan lokaci i wanted to die…I love you sooo much sarah i will wait for you to see that…. ya dan marairace yana cuping face dinsa da hannun sa
Kuka ta sake fashewa da shi don taso ace yaga zaquwar ta na son kasancewa da shi har abada ayau din
Yace Sarah “You must be thinking ure ok but i know ure not..kinji?
“Ta dago cikin ido tana kallon sa gaba daya ta wanke fuskan ta da hawaye, muryan ta har na rawa tace mmm toh shikenan mahfud,kenan
I must have to wait right?
But Mahfud if u love me as you said now dan Allah muyi auren mu..
I swear i want to be with you, i love youuu…. tafada tare da fadawa kan kirjin sa a hnkali..
Hankalin sa ya tashi sosai musamman daya ji yadda take zuba masa sautin kukan nata da gaske.
Amma har cikin ransa tsoro yake ya sake dauko wani serious issure tsakanin su, kwata kwata wata daya da dan satikai ne da faruwan komai amma sarah tana tunanin ta mance komai
Shi dai yasan she is not sure abunda ke ranta kawai take gaya mata kawai takeso
But he wont riskit this time dole sai sun bada juna lokaci su gane asalin me suke ji aransu musamman ma ita..
She needs time for her self shes still depressed.
Da haka yayi kokarin convincing dinta akan su tsaya matsayin friends for now duk dama da kyar da rigima ta amince masa…
Hakan ya sa basu isa gida da wuri ba sai daff ana neman kirar ishai”.
Sauri yake ya ajiye ta ya shige masjid…
Suka hade ido da granny….she was out on the yard gaba daya hankalin ta ya tsahi data dawo bata ga sarahn ba kuma anty warda bata san da fitar nasu ba.
Yana ganin yadda ya hade rai ta zuba musu ido ya sa shi saukowa tare da sarahn..
Wance itama ta dan razana da ganin granny..
Suna isowa tana kare mata kallo,daf ta dan rusuna tace barka Da yamma granny
Granny ta kalle ta tana shiru bata amsa ba..
Ta juya ta kalle sa tace ina kuka fito haka har dare mahfud? i asked ur mum and. …ya tsare ta da cewa granny abokina ne fa ya zo shine muka tafi da sarah su gaisah…
Why did i have to anounce if am going out haba granny
Cikin bambamin masifa tace akan me bazaka fada ba toh?
Wai gani kake kai ka girma ko,?shikenan ka girma mahfud,sai ka rika yawo kai kadai amma ba kana daukar mace ba kana kaiwa wannan time din da ita waje ba.
Ce maka akayi tana zaman kanta ne da zaka rikaa yawo da ita?
Granny pls ya fada adan saukake yana so ya bar wajen amma haka ta rika surutu har sai da ya dan nuna bacin rai akan face dinsa kafin ta kyale sa ya wuce..
As usual daya bar wajen sai ta matso kusa da sarahn fuska ba yabo ba fallasa tace
Ni ba zan hana ku fita ba saratu,amma yakamata ki rika sanar da matan gidan ko?ko zaman kanki kema kike so kiyi ne sarah?
Ta sunkuyar da kai a hankali tana so tayi magana amma fargaban granny ya hanata
Shiga ciki ki sauya wannan kayan duk ya matse ki …grnny
tafada batare
data kalle ta ba ta juya
Sum sum ta wuce ta shiga bata jin dadi aranta..
Bayan ta shige site din ta wanka tafada ta kimtsa kanta tsaf kafin ta sauya zuwa simple silk vest and short na nitie ta fada kan gado..
A duk lokacin da ta sauke nunfashi ba abunda take tunowa sai maganganun da sukayi da zu da mahfud..
Haka kawai ta shiga blaming kanta tana tunowa da duk abubuwan da suka faru tun ranar da yace zai aure ta a india..
What a curse, meyasa ban amince masa tuntuni ba? Sirrin da nake gudu kar ya shiga tsakani na da shi someone just prove to me that i cant even protect it.
Kuma yayi amfani da shi ta hanyar da bai dace ba he ruined all my hardwork and my mothers effort a lokaci guda ya samu a kwandon shara..
Im now nothing i lost everything
,rayuwata,ummah na and now mahfud is….sai ta kasa karashewa sabida zafin da kirjin ta yake mata
Wasu zafafan hawaye ne suke rushing kansu daya bayan daya daga idanun ta,
Sosai take jin zafi idan ta tuno da abubuwan ban haushi da wauta da tayi da rayuwar ta a baya..
She just wished she was better amma wani bangaren zuciyan ta ya ki ta yadda cewa ummah ta rasu har yau…she cant think straight tun tana kwance har ta tashi ta zauna kan gado rungume da piliw ta cigaba da shero kuka kamar zata cire ranta..
Wani bin idan ta tuno abubuwan data rasa
Sai taji kamar a mafarki
Amma babban abunda yanzu yake razana ta shine kar ta rasa mahfud”why must he hesitate to marry her now..
Yanzu ne ai nafi bukatar sa
Cikin wannan tsumayin har anty warda ta shigo bata hankara ba..
Tausayin ta ne ya kama ta sosai sabida tana dan jin abunda take fada cikin shessheka,