SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

in har Goguwar munafurcin babaji yafi karfin kowa nasan karyan shi ya ja da Allah don
Shi ne gata na dani dake..
nayi miki miki alkwari saratu bazan taba barin ki a wani hali ba har na mutu ina tare da ke yata sai na karbe miki rayuwar ki daga bakin qaddara dayake so ya jona miki..
Na sake sauke hawaye na rungume ummmah ina kuka bata fasa rarrashi na ba ta cigaba da cewa
kiyi shiru abunki,ko duk duniya sun guje mu ni dai nasan babu mai raba ni da ke har abada sai mutuwa.
Nace Nagode ummah, na gode da kika fahimce ni, nayi miki alkwarin biyayya duk rintsi duk wuya ba mai raba ni dake ummah ummah Allah zai saka miki Allah zai tona asirin kowa zasu ji kunya wata rana..
..Cikin shshesehka nake fitar da maganan da kyar
Ummah bata ce komai ta shiga share hawayen ta tana kan bubbuga gadon baya na a hankali
A hakan muke zauna cikin bakar kunci da jiran abinda zai faru nan gaba gidan sarki.. abincin ma na gaban mu amma bamu wani masa cin kirki ba.
Yau ne ummah bata fita neman babaji ba don tasan duk yadda akayi ya gama shirya mana tijarar da zaiyi agaban sarki anjima.
Wajen karfe 3 saura aka aiko sako cewa bayan lasar ake so mu hallara acahn.
Sosai Gaba na yayi mummunan faduwa amma hakan na yi ta lazimi ina rokon Allah ya saukaka mana lamarin.
3.45pm Makil da manyan dattujan gari a kofar gidan mai girma shugaban kurwala..
Ladiyo, laure hansato da maman dukku da kishiyon ta rabi da hassana sai dukan kishiyoyi ummah da dangin miji watoh baba babaji da mata guda uku sune a gefe akan tabar ma duk suma babaji ya sa aka kira su domin shari’ar ..
Hmm jahilci baiyi ba , ashe idan abu ya kasance na cin mutunci baza a yi shi a sirri ba sai an taro jama’an gari?
“Hakan Ni kadai ya dama amma ummah na kam tun agida na lura da babu fuskan imani a tattare da ita sosai ta dauke fuskan rahma ta bushe zuciyan ta
Kamar wasu barayi haka aka gurfanar da mu biyun a tsakiyan fada kan tabar ma..
Sarki ya soma jawabi da jan hankalin mata da dai daikun matasan dake wajen akan illahn safaran miyagun kwayoyi acikin gari da sauran garuruwan makwabta,
Yace ” na kira ku ne badon komai ba sai don na yi hukunci ma wannan baiwar Allah bisa laofin data aikata ma yankin nan ..yadda kowa in yaga ni zai san bada wasa muke yi,
Ummah tasha mamain wanna furucin A zuciyan ta tace Kenan sarki ya amince da maganan su har ya laka min hukunci? Tayi shiru dai tana sauraro
Anan ya sa maga takardan fadan sa ya gaya musu duk abunda ya faru da umma na ni kuwa nasha mamakin yadda aka juya kan zancen aka laka ma ummah komai a take hawaye suka wanke fuska ta .
Bayan angama Tuni dattijai suka hau zagi da bakar magana
Ana Allah ya wadar da ummah wasu suna cewa ashe duk halayen ta da aka santa da shi na nagarta da chan na munafurci ne?
Ni da umma bamu ce komai ba muna shiru
Sarki ne ya dakatar da surutun da ake cikin raderaden,
Yace”
Ya isa haka , ya kamata muyi abunda ya kawo mu..
Yace”A matsayin na na mai gari na bada dama wa duk wanda ya san wani abu mai alaka da lamarin wannan baiwar Allah muna sauraro kafin a fadi hukunci ta.
Ah’a ranka shi dade ayi mata hukuncin ta kawai..ga gaskiya boro boro me za ajirah?
babban aminin baba babji wato dan masani ya fada a zafafe
“Tuni wasu suka bi bayan sa nan ma har da mata kishiyoyin ummah ne kawai basu tanka ba
Nan ma sarki ya tsawatar ,
Yace tunda haka ne baria shi mijin ta babaji kawai ya fada mana ta bakin sa muji,kar kuma wani ya sake tsoma mana baki
Shiru ne ya dan ratsa wajen.
Sannan sarki ya dubi baba babaji yace yayi magana”
Har da gyaran muryan sa ya mike tsaye kamar mumuni
Farko ya fara da fada ma jaama’a wai ya auri umma ne sabida ya na mata kallon kuruciya zai biye mata hakkin ta amma halayen dayaje ya tarar da ita sun dade suna sashi mamaki,
Ana shiru ana jin sa.anan ya dada bata ma ummah na suna ya nuna a idon jama’a cewa bata da tarbiya,fitsarariya ce.
Nikuma Anan raina ya soma baci..
ummma kam na shiru ta dago tana duban sa cikin wani murmushi mai dauke da sarkakkiya.
“Yace ni bani da abun da zance tunda sarki da al’umman sa masu adalci masu girma sun kama ta da laifi dumu dumu kawai ayi mata hukuncin da ya dace da laifin ta…
nima ayafe ni domin da haka nake neman shaidar mutane da yan uwa cewa na saki gambo saki uku..bazan iya zaman aure da ita ba
“A take Ummah ta rangwada guda mai kauri mai sauti tayi wani irin dariya mai cike da jin dadin wanda ya nuna alama ko ajikin ta.
” Surutun da ake yi kasa kasa ya faadada aka cigaba da cece kuce matan nan kamar zasu tashi su buge ta kowa na zagin ta,
“Raina yayi mummunan baci da irin yadda ake nunawa ummah na ita barauniya ce kuma karuwa uwa uba marar tarbiya.
Jiri ne ya soma dauka na sai naji bazan iya daukar maganan ba cikin wani irin hatsalallen fushi da ihu na ce “ku dakata…!!!
Kowa ya dakata….
Tsit waje yayi da mamakin jin haka nasan wasu sun sha ko aljanu ne dani
anan na mike gaban sarki kamar mara hankali
Na tsaya
Cikin kuka Nace” hammma, kai sarki mai adalci ne ka dada dubawa ummah na bata da laifi akan abunda ake tuhumar ta ..
Ni Nasan gaskiyar abunda ya faru in ka bani dama zan fada maka.
Kowa sai yayi shiru
Baba babaji yau a munafukin sa ya fito Sai ya sauya kama ya zauna abokin sa ne ya tashi a zafafe zai kama ni da duka wai nayi rashin kunya da katsalandan a maganan manya anan Aka riko sa.
Sarki yace” kowa ya nitsu ..kar wani ya sake motsowa idan bajaka duk abunda nayi masa shi yaso..yace saratu ina jin ki mai gaskiyar da kika sani akan wannan lamarin.
Anan nayi ajiyan zuciya kukan dake so yaci karfi na ma na tukare shi
Nan na soma zuba labari A- Z yanayin zaman mu da ummah a hannun baba babaji har rakube da nake yi a gidajen mutane na fadi daliili na,
Kukan da nake yi anan yasa ummah na kuka itama
Har cikin ranta bataso na fadi abunda ya faru dani na fyade da cikim shegen ba.
Shiru ne ya ratsa wajen tabbas zuciyan wasu ya girgiza da jin oda side of story na dana umma dana bayar ..
Cikin magiya da kuka nace in har akwai karya acikin abunda na fada Allah ya wulakanta ni a cikin wutar sa…dan Allah ka bi mana hakkin mu bamu da kowa sai Kai sai Allah
Shikan sa sarki zuciyan sa ya girgiza amma sai ya daure ya juya yace ena babaji ?
A dan rude baba babaji yace ranka shi dade gani
Sarki ya dube sa cikin wani irin yanayin damuwa yace ka fadi tsakanin ka da Allah me kasani akan wannnan maganar ?
Nikam tuni ummah ta riko ni tana kuka tana lallabani yanzu kam duk masu bakin zagi sun dan rusuna ana dai kan sauraro
Anan baba babaji yace” uhmm ai daman ni nasan za’ayi haka ranka shi dade shiyasa ma nazo da shaiduna ga su nan.
Yayo nuni da manyan munafukan sa abokan sa aciki naga har da sageer.
Yace ma sarki “wallhy wayannnan da kake gani sunyi nisa wajen makirci da munafurci amma ni bazan yi dogon magana ba gaskiya ta ita ne zata fidda ni.
Ya juya kamar da gaske yace ma ummah wallhy gambo ba dai naji kunya ba sai dai ke kiji kunya yau sai na tona asirin ki.
Umma ta dube sa ta kar kada kai tana shiru .
*WATTPAD VOTE AND FOLLOW @SURAYYAHMS*
*OFFICIALCATTY????*
[2/23, 22:43] +234 802 646 5734: *????BRILLIANT WRITERS ASSO????*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }