HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Da kyar ta tashi ta shiga wanka ta kimysa kanta jiki a sanyaye,
Anan ne da ta fito take ganin letter da ak aiko mata

Bayan ta karanta she just made up her mind to face her reality

Simple kaya ta sa riga da skirt da mayafi dan karami akan ta ta nufi offishin hajiya billy.

Anan ma da kyar mutane suka barta ta shiga lpya kowa na so yaji ta bakin ta amma bata ce komai ba har ta kai gaban su

Kallon tara saura suke binta da shi, dama alhj ne kadai yake sassautawa to baya nan

Anan ma take sanin cewa yazeed fa ashe tintuni suka shirya da safeeenh tana nan daga gefen sa bata sani ba..

Hajiya billy ce kadai tayi magana”sai dai har ila yanzu a bacin rai take mata da tsawa

Ita kuwa sarah bata ko nuna bacin rai ba sai ma shiru datayi tana jin ta

Bayan ta mata bayanin suspension dakwace matsayin ta,..

Sai ta kara da cewa zata yi duk abun da zatayi don taga sarah ta nisanta daga qurbata musu suna da mutuncin su

Har suka gama banbamin su bata tanka ba..sai da tayi waje sai ga wayannan matan societyn sun tunkaro ta da rally stick akan basu son ta,baza su lamunci fuska biyu ba..

Da kyar security suka tsare sarah daga hayaniyan su…

Wasu sun zage suna cewa ai irin su sarah ne ke fakewa da taimakon mutane daga bayan fage suna lalata su..

Tasha mamakin dan adam..ashe haka zuciyar mutane yake?

Tun a mota take kuka
Tana tuki gaba daya sai taji rayuwar tayi mata zafi

Ko Parking batayi ba aka kira ta cewa ta zo gidan gonar mahaifiyar ta naci da wuta

Tasan dama ummah bata nan tafito sai ta juya kan mota ta wuce nan gidan gonar ummahn

Da mamakin ta taje ta samo fire burget Da
Ambulance suna kan zageye gashi bangare daya naci da wuta sosai..

Tana sauke kafan ta kasa sai ga yan jariida rututu sun yo kanta..

Cewar babban su, mrs sarah ko zaki iya gaya mana dalilin daya sa mahaifiyar ki ta kashe kanta?

Wani irin dum dum taji tuni kanta ya fara sarawa
Tayi cikin su hargitse suna biye da ita..

A rude kuma cikin razana Ta shiga tanbayar su anan ina ummahn ta?

Ba wanda ya amsa mata ya sa ta danna ihu a firgice tana dube dube tana kiran ummah”gwanin tausayi.

Wani maiakacin ne ya ke ce ma sarahn ,ai wanda suka ga faruwa abun sunce ummah dakanta ta shiga wutar din ta kashe kanta.

Kenan ana so alaka mata da cewa bakin cikin abunda ya faru da ita jiya yasa tayi comiting suicide.

Kan Sarah kamar zai kunce ta ce karya ne”
Ummah na bazata taba tunanin Kashe kanta akan dan wannan abun ba karya ne…

Duk sai aka maida ta mahaukaciya anan,
Wasu har karkada kai suke irin abun Tausayin nan..

Sam taki yarda ummah na cikin wutar sai ta zube kasa tana kuka tana kiran sunan ta da karfi..

Yadda ta birkice ya hana yan jaridar karosowa kusa da ita..

Amma sai suka sa a fagen labari cewa mahaifiyar sarah ta kashe kanta sabida abun Kunyar da ya bayyana daga halayen ta da yarta..

Wasu kuma suka buga cewa ai ummahn ce da bakin fa tace gwara ta mutu da ta zauna tana kawo ci baya ma rayuwar yarta..

Anan gaban wutan saraj take xaune akasa tana kukan fitan rai da rudewar runanin har dare yayi bata motsa ba

tunani take ko zata yadda da ummahn ta na cikin wutan nan ko kuwa ummhn ta zata fito su tafi gida..

Daga nan ma polisawa ne suka yi nasaran daga ta anan zuwa asibiti

Wasa wasa tayi kwanciyar kwana biyu in shock bata farka ba.

Kuma gashi babu ummah babu asalin labarin ta..

Ko da ta tashi duk hidiman hirar su akeyi a media ana shan mamaki,…

A kwana na ukun ne yan uwan ta daga kauye suka taho aciki har da baba babaji nan suka mata ta’aziyar da jimantawa akan abun da ya faru..
Don labari ya iske su

Bata cikin hankalin ta don bata amince ummah ta rasu ba tukuna,..

gashi duk inda ta juya sai ace sabida ita mahaifiyar ta ta kashe kanta..

Ko da ta mayar ma yayun ta da dangin ta abunda ya faru sai suka qudiri niyyar mata gangamin addua a nan wajen malamai akan lamarin ta….

A cewar su iya taimakon da zasu mata kenan har ta sallame su suka tafi ba wanda ya lura

Kwanan ta biyar kullum tana cikin rashin lpya sa kuncin rashin mahaifiyar ta”gashi taki sam ta amince da komai a ranta amma day by day take ganin hakan ne.. hala ummahn ta mutu ne…

amma tasan bazai taba yuwa ta mutu sabida ita ba
Gashi ko waya bata yi da kowa anan take kwana ta wuni wani bin bata cin komai sai kuka

Randa ta cika sati guda da safe ta mike tsaye ta kalle kanta jikin mirror tsawon lokaci tana tuno da rayuwan ta da tsawon lokaci da ta dauka ana fooling din ta da duk abunda suka kawo ta wannan lokaci….

sosai ta birkice ta hargitse kanta gaba daya a wajen sai ta fashe da wani irin kuka mai zafi da cin rai..

Sake muryan ta tayi kamar yarinya karama Yi take kamar Allah ne ya aiko ta har sai da taji bata sauti..

A kasa ta kwanta rungume da kafadarta
Tana tunanin ta ina zata fara fuskantar duniya babu ummahn ta..

Duk sai ta daura ma kanta laifin komai.

Da haka ta yanke shawaran barin nigeria gaba daya ko zata samu nitsuwa na dan lokaci..

Daga time din taje tayi booking ticket ta shirya komin ta Cikin dare ta bar nigeria zuwa kasar florida anan yankin america..

Ta tabbata anan kawai zata samu catherine shiyasa ba tantama ta wuce….

Ko da ta isa a wani hotel take zama har Allah ya sa ta same number ta ya shiga,

don tasan cath bata san meke faruwa da ita ba…
Sai da suka hadu ranar take fada mata komai..

Wanda hakan ya sake jefa ta cikin wani sabon jimamin a take sai da aka sake kaita asibiti..
sabida nunfashin ta na yawan yankewa musamman idan ta tuno da part din ta da yazeed

Ita kanta cath ta girgiza
Da jin duk abunda ya faru da sarahn kamar a mafarki haka ta dauke sa.

Ciwon kamar da wasa sarah tayi wani 2days tana kwance har ila yau nunfashin Tan ne bai zama stable ba..

A germany kuwa tun ranar da mahfud ya koma… aiki ne yayi ma sa yawa baiko samu daman jinyar zuciyan sa ba

gashi tun da su anty warda suka lura da hakan sai suke kokarin hana sa samun lokacin da zai sa damuwa wa ransa….

kullum acikin daga sa suke akan suje hidiman yawo da grannyn sa dake mugun son ziyartan masallacin taiwan don jin live programs na manyan islamic scholers da philosopers..

Da shike hidima ne na addini da qaruwa sai idan ya zauna baya son tashi wa’azi ake mai shiga zuciya da tsatssafo da imani da tsoron Allah..

Tun zuwan sarah washe gari cath take shirin nema ma sarahn mafita..

A yau da doc yace ma ta sun sa ran jikin sarahn zaiyi sauki fiye da kullum,a ranar ta nemi layin mahfud ta sanar da shi duk abunda ya faru.

He was heartbroken kamar an tsaga zuciyan sa haka yaji,
Sai yafara blaming kansa da bai tsaya ba,had he know that hakan zai faru da ita da bai bar nigeria ba ranar .

A lokacin ne bai iya boyewa ma famyln sa ba ya gaya musu duk abunda ya faru da sarah da ummahn nata cikin kwana kin.
Duka sun fahimci abun sosai…

Sai dai grannyn sa ce kawai ta san farkon labarin da duk wani fadi tashi da yayi akan sarahn har ila yau..

A hakan ma don tayi masa fin karfi ne taji komai don baya iya boye mata damuwar sa wata rana..

Shiyasa tafi kowa tausayin sa da bashi shawaran ya sassauta makan sa..

Daya dawo daga nigeria ranar Daya daga cikin dalilin da ya sa take tafiya dashi kenan masallaci don akwai yar makwabciyar su shabnam dake mugun son shi amma baisan da hakan ba amma granny tana sane..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button