SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Sai tabi ta hada da haushin ai ance sarah ta zo ta koya abinci wajen ta sarahn ta ki gashi mahfud ya wani zo yana lallaba ta..
Bayan ta gama sai ta taho da shi ta samu granny na kan aikin kallon ta..
Tace granny yau nasan kinsha yunwa amma yafi da bakici abunda zai dame cikin ki ba…
Granny ta taso da kyar cikin muryan tsoffi tana cewa its ok shabnam maganan ya kare evryone makes mistakes itama nasan kufce mata kawai yayi
Ina ita sarahn?…ta tambaya tare da zama
Shiru shabnam ta danyi daga bisani tace ai tunda ta bar nan ta wuce daki ..she dint even stay to watch as u ask her..
Granny bata ce komai ba ta tabe baki..
Bayan tayi serving granny
Sai tasa aje a kira mata sarah da mahfud..
Shabnam Tace aihooo dama bai tafi bane na dauka ya fita..
Grnny tace no,inaga yana wani abu ne aciki tukunna..
Within 10 minutes maid ta dawo tace sarahn na bacci..
Shikuma mahfud yace ya koshi..sai da shabnam taji wani gullotun haushin sa amma sai ta share…
Ga yarinta na damun ta sosai,shes already concluding everything bata damu da sakamakon sa ba..
Bayan kamar awa daya Yana zaune yana waya sai gashi an buga knock a falon sa yake
Sai dai yana iya ganin mai shigowa da shike wall din gaba daya glasss ne ga haske ko ina..
Tana shigowa ta zauna kusa da chair dake fiskantar sa bai daure fuska ba har ya idar da call din ya dube ta a takaice yace lpya?
Sai ta dan sauke ajiyan zuciya ta fito da dan karamin qur’anin ta tace nazo ne kayi min bita tunda baka je ko ina ba…
Sakrcin ta sam baya burge sa amma sai ya daure yace” im busy.
Ta dan rolling idanun ta sigar normal phrase ai nasaba jin wannan.
Bata ce komai ba ta Tashi ta fice minti kadan sai gasu nan sun shigo ita da granny,
Kallo daya ya musu ya dauke kai,.ko zama granny batayi ba tace mahfud why arent you teaching her kullum yarinyar nan sai ta kawo min complain”
Batare da ya kalle ta ba ya daure fuska..murya ciki ciki yace granny na fada mata ” am not in the mood am busy..
Cike da damuwan daure fuskan dayayi granny tace busy doing what? Mahfud ko wani ya bata maka rai
Charaf shabnam ta karbe maganan”ehmm grnnny let him be,ai da ba hakan yake min ba now he’s alwys just angry at me musamman idan nayi magana akan ta
Ai kuma gaskiya na fada bata iya abinci ba ba ci zamuyi ba..ta murguda baki
Ya hatsala amma sai yayi calming kansa yace
Ohh realy?as what,ke kika haifeta ko ke kika sa ta tayi miki girkin?
If ure talking about someones fault here,i think u shud look at ur self..ko bakisan abunda kikayi ba dabian musulmi bane,Annabi SAW yace kar ka kushe abincin wani idan zaka ci kaci idan bai maka ba just quietly leave it.. how dare you critisise her like that,.? Sa ar ki ce..? Ya daka mata tsawa
Shiru granny tayi ta rike baki a tsakiyan su..
Lokacin shabnam ta matukar hawa sama, akan sarahn ne zaina mata tsawa haka for what?..
Ita sarahn wacece da ba za ayi critsing dinta ba..
Cikin fushi tace ohk naji nayi laifi,but granny u shud also tell him to preach annabi yace ma wancan yarinyar,sabida itama girman kanta yayi yawa “she cant even bring her self down to learn from me, amma bai ji haushin ta ba sai ni?
Maybe thats whay she wud neva learn ufff shes so arrogant and rude a haka zata kare..
Enough, granny ta daka musu tsawa duka..
Cikin masifa tace where is this coming from..lpyan ku kuwa ashe abun naku yafi karfin wasa? Sakarci zaku kawo min
Idanun shab gaba daya suka taro ruwa murya ta na rawa tace grnny ai kina gani shi ya fara,
Yace just shut up shab,ure just 17,just learn to be respectful,sarah ba mate din ki bane and then agidan nan dole za ki bata girman ta..thats all am saying here.
Granny tace enough
Mahfud meke damun ka ne kam.. bazaka bari nayi magana ba..ok kai zakiyi ta haura ma karamar yarinya da surutu ai nima nace ma sarahn ta koya wajen shabnam but she dint”
Amma ni ban bata rai ba sai kai zaka bata naka ran akan shabnam?
Pls dont take sides anymore…
maganan nan ya tsaya haka in kuma laifi kake nema both of them are at fault.
And you Shabnam sarah is just like ur elder sis agidan nan nasan tayi ba dai dai ba,but ai wannan tsakani na da ita ne u shudnt worry abt it ok?
he’s right next time idan bata iya abu ba dont critisise her like that,
Kema bazakiji dadi ayi maki hakan ba..
Respect each oda thats why we are family..
Hawaye ta somayi a hankali don bakaramin bakin ciki mai dauke da tsoro ne ya gauraye ranta ba..
tunda take da Mahfud a duniya bai taba mata haka ba sai yau,Who is sarah actually to him? Ta lura tunda ta zo gidan kamar Da ita kawai ya damu,
Ita fa?Ko dan bata fito fili tafada tana son shi ba ne amma gani take ai tunda granny ta na da clue ai shikenan..
Ta yaya za’ayi ta san relatiosp dinsu da sarah
Kuma a yanxu tasan ba wayon da zatayi ta san meye matsayin sarah musammann awajen mahfud..
Take sai ta hada plan,granny tana kan musu surutu ta dago cikin sanyin jiki tace im sorry mahfud, toh kayi hakuri bazan sake ba..ta shagwabe
Murmushi granny tayi ta dan jawo ta kusa ta share mata hawayen ta tace,dats my girl.. comn ya isa haka share hawayen ki shab,
Shima dole zai baki hakuri…
Ta dan kalle sa tace Comn my prince shes apologising,.. baice komai ba ya dauke kansa
anan shabnam ta dada fashewa da kuka cikin kukan take cewa ita zata koma wajen ammyn ta kawai bazata zauna anan din ba, making him feel like an ware ta agidan,…
Dan karamin ajiyan zuciya yayi yace its ok, am sorry too shikenan?
Ta gyada kai a hankali ajikin granny,
Tace to magana ya kare to yaushe zaka koya mata karatun,
Dai dai nan sarah ta hango su ayayin da ta ke karyo kwana tanan tana saukowa kusa
Yace sai na dawo ,yanzu zan fita ne.
Da sauri ta share guntun hawayen ta tace ohhh maybe bayan ishai ko?
Ta yi masa murmushi
Ya rasa wani irin saukin waarewa zuciyan shabnam ke da shi ,yayi ajiyan zuciya yace ok.
Nan suka fice tare da granny tare da masa sallama..
Ko da suke tafiyan su ita ita kadai ta hango sarahn tsaye, amma granny bata ganta ba..
Kasa kasa ta dube ta cikim ranta tace sai na rama abunda yake min akanki, i will surely show you that hes mine and am equally important to him ta dan ja tsaki..
Ita kuwa sarah idon ta nakan sa daganan bayan wucewar sa ta sauko ta same sa,
Cike da fara’a ta ce baka fita ba? Na dauka ka tafi office
Sai da ya koma kan cushion sannan ya dube ta a kasale yace no,im here wani abun ya rike ni
Ganin yanayin sa yasa ta karaso ta zauna daga da chair din dake kallon sa tace inche lpya? U look tense ko wani abu ya faru ne..
Ya dan dago kadan suka hade ido yace babu komai..let me get dress ko tare zamu tafi ne yau..
Ta mike tsaye tare da gwalo ido tace nooooo pls kaje abunka..
Yayi murmushi..a yangace tace take care of urslf hero.. ya mayar mata tare da cewa ohh,and you too heroine..
Nan ta fice ta bashi wuri. …
Bayan tafiyar sa daki ta koma ta kira catherine suka shiga hira
Ita kanta cath taga sauyawan sarah, yanzu ta dada yin hankali
And most importantly hankalin ta akwance yake tamkar ba abunda ke damun ta..
Haka tayi zaman shiru daga baya ta soma tunanin yadda zatayi ta iya girki, ta lura shabnab bata son ta shyasa bata so tace zata forcing kanta ta wajen ta bare ajisu agidan sam bata son ta jawo ma mahfud abun magana tunda don shi suka karbe ta agidan..