SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Haka ta shiga tunani wani bin idan ta kammala ibadun ta sai ta shiga food netwrk tana duban dishes da clips ammma is still not enough
Ba lallai bane ta iya yayi dadi kamar yadda take so ta nan..
A haka ta yanke hukunci zata na kokartawa tana yi a hankali ko ba zaiyi dadi ba amma she wll try..
Haka rayuwar su ta kasance,kwana biyu ne kawai da faruwan haka
Ammma sosai shabnam ta soma stalking dinsa
Ba dama kuma yace zaiyi magana sai ta soma nuna kamar maganan ranar ne bai wuce ba,
Haka ya danne zuciyar sa yana bari tana zuwa site dinsa yana koya mata karatun nata every day after ishai..
Fitina da kiriniya yasa bata barin shi sai wajen wani 9 ko 10 sannan zata kama karatun..
Kwata kwata ta sauya shikansa baya gane mata..
Ita kuwa sarah hakan take fama a kitchen but the more she try the more she gets dissapointed
Yanzu ba wanda yake cewa abincin baiyi ba amma shabnam dole sai tayi yadda granny zata fadi gazawar ta..
Kafin anty warda ta dawo gaba daya sarah ta shiga damuwa akan haka gani take kamar bazata taba iya girki mai dadi kamar na shabnam ba.
Gashi a dik lokciin da take tunanin zata ga mahfud sai ta gansu tare sa shabnam din ta takure ta katse ta tsare ko ina da sunan koyan karatu..
Lokaci guda damuwan ta da kishi suka fara shigan ta..she staterd feeling less again
Banda ma yanzu idan taji wani iri ta kanyi addua ko tayi ta azkar amma still tana bada kanta laifin duk wani abu dake faruwa da ita..
Ranar da anty warda ta dawo kamar ma ita akayi sosai ranta yayi dadi..
Ba kowa anan tsakar gidan sai ita don yau granny itama ta yafi cahn wajen mahaifin mahfud a sweden.
Tace sarah fatan kina lpya ko?
Ta gyada kai cike da murmushi tace lpya lau anty am soo happy that ure back..ta dan shafe gefen fuskanta tayi murmushi..
Tace ina sauran toh tunda na dawo banga kowa ba mahfud bai dawo bane…
Ta danyi shiru daga bisani tace inga yana site dinsa shabnam tana tare da shi yana koya mata abu
Anty tace ok,lets go an c them
Nan suka mike tare suka wuce site dinsa..
Shab Tana zaune daga gefe agaban sa sai narkewa take tana rigima baiya ko kallon ta amma bata fasa ba,
Tun da suka dosu nan sarah take jin wani irin bakar kishi na rufe mata ido,haka kawai shabnam ta soma bata haushi
Yana ganin anty ya mike tsaye yana cewa mum yaushe kika dawo?
Tayi murmushi ta amshi warm hug din da ta taho masa dashi tace sit down nima yanzu na dawo ina tare da sarah..
Suka maida juna murmushi,shabnam ta katse su tare cewa welcome mum, da faffadan murmushin ta tace shab sarkin karatu,
Hope ure doing great tayi dariya cike da jin dadi tace yes maamm
Mahfud is here alwys wannan karon inaga sai nafi kowa iya bita a makaranta.
Duka sukayi murmushi amma hakan ya ki bayyana kan fuskan sarah she’s just normal..
Yace mata toh tashi kije ki kwanta sai gobe zamu karasa tunda mum ta dawo,
Lokaci guda ta shagwabe ta marairace tace nooo, pls i want to finish it ai anjima zanje na musannam na gaida anty dan Allah ka karasa min… Ta wani langwasa masa wuya tana kirsa da ido
Ita kanta anty warda ta soma gane shabnam tana hakan ne sabida sarah,
Amma sai ta waske tace ok,shikenan za akarasa miki mukam bari muje mu kwanta gobe ma hadu..
Cike da jin dadi tayi murmushi sarahn bata ce komai ba suka fice da anty..
Suna tafiya tayi shiru har suka kai site din anty warda
Lokaci lokaci antyn ke tambayar ta abubuwan da suka gudana da yadda ta yi days din ta da bata nan
Sai dai sam hankalin ta baiya jikin ta sosai sama sama take amsawa
Duk anty na lura da ita sosai
a dan takaice ta kalle agogon hannun ta its 1o.30pm ta sauke ajiyan zuciya a boye
Anty tace lpya kuwa sarah
Tace lpya lau anty i think im sleepy zanje na kwanta..tayi murmushi tace bakomai kije sai gobe zamu karasa hirar namu ko?
Ta gyada kai sukayi sallama ta fita.
Sam sai ta kasa controling kanta she cant help it kwana biyu da shabnam din ke makalkale mahfud a inuwar ta ba wai baya sosa mata rai ba ne..
Sai ta den bi site din sa,
A rabe ta leka ta step kusan minti biyar sannan ta gano cewa har yanzu shabnam tana nan zaune da shi ..
Agogon ta sake kallo kishi ya sa ta sake furtawa ai da granny tace babu kyau na rika kebewa da shi
Just look now wannan yarinyar bazata taba barinsa ba tun karfe 8 har yanzu ai abun ya wuce koyan karatu kuma”
Tana juyawa suka hade ido da anty,.
Kirjin ta ne ya dan buga sai ta sauke kanta kasa
Tana jin kunya..
Anty tace sarah mekike yi anan?
A rude tace babu komai
Sai ta karaso ta leke itama don ta tabbatar ma sarahn ta fahimce ta..
Amma sai bata ce komai ba tace jeki kwanta its lts late..
Ta gyada kai a sanyaye ta wuce
Kallo anty ta bita da shi tayi murmushi daga nan ta wuce ta kado kan shabnam ta kaita room dinta..
Washe gari da safe kafin sarahn ta fito sai ta samu har shabnam ta gama hada abinci yau kala kala tayi masu dadi da dauke ido kamar wacce aka mata gori..
As always tana cikin zumudi..
Saukowar anty ne ya fargan da sarah daga tunanin kuncin data shiga na yaushe itama zata iya kamar wannan
Anan Suka agaisa tace muje ki karya,
Shabnam wheres mahfud ko ya har ya fice ne.
Bata ko amsa ba ta jiyo muryan sa ta baya yana cewa na isa na tafi banga mama na ba?
Suka maida ma juna murmushi ya sauke mata light peg agefen kuncin ta tare suka iso kan table din sarah na biye da su..
Suna zama ya dauki lokacin sa cikin nitsuwa ya sace moment yana duban radiant face din fa
Suna hade ido ta sauke wani kayataccen murmushi mai cike da kauna..yana kamewa da nashi
Shabnam ce kawai ta lura da hakan sabida itama din shi take kallo..
Anan ta tashi cikin surutun ta data saba ta soma fadan sunayen abincin da ta dafa cikin son ta yi ma sarah gwale take abun ta, har anty warda ta fahimce ta sosai..
Sarah kuwa na shiru..ita dai abunda yafi damun ta bai wuci yadda shabnam ke cewa ai kwana biyu da ba ita tayi girki agidan ba so mahfud yayi ta purging,
Gashi bai isa yayi musu ba she took the oputnity to make sarah feel like Kenan don ita kadai take tare da shi dole ta san duk abunda yake ciki..
Lokaci guda sarahn taji wani iri sai ta kasa sake kai abincin bakin ta tayi shiru..
Anty warda tace mahfud wai dagaske kayi ta purging wai wayake dafa abincin ne haka har da zai sa ciki tsurewa?
U shudnt have been eating it in yana damun ka bana son abunda zai jawo maka wani ciwo kasan mahaifin ka bazai ji dadi ba ko..
Yace its ok mum sau daya ne ,and im fine.
A hankali sarahn ta mike tare da cewa xcus me ta bar wajen a sanyaye..
Kallo duka suka bita da shi..
Shabnam ta dan murkuda baki gefe tayi dariya..
Nan ya kau da kansa ya cigaba da cin abinci slowly..
Shiru ne ya ratsa nan anty tana lura da kowa cahn sai ta kawo tunanin ko sarah ne shabnam take magana akai?
Yana mikewa yace ma shabnam ta biyo sa daki..
Duk dama tasan ba alheri bane amma sai ta tashi cikin rawar jiki ta biyo sa
Hakan ya dada tabbatar ma anty warda abunda take tunani sai ta tashi ta kama hanya zuwa site din sarah..
Akan gado tafada tana kuka a hankali..
Shikenan wata karamar yrinya zata raba ta da mahfud din ta…she just cant help it amma sosai kanta ya daure tana jin komai ya tsaya mata..
Ta yaya zan fara iya girki and then tana so ta kasance kullum a gefen sa amma a duk sanda ta tuna time dinsa gaba daya tare da shabnam yake spendings sai ta karajin ta karaya..