SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Kukan take yi rungume da pillow har sai da anty warda ta dafa ta kafin ta dago..
Fuska ba yabo ba fallasa Tace sarah meya faru ne kam?
Tayi shiru ta sunkuyar da kai zata yi rufa rufa antyn tace dont lie to me tunda har naga hawayen ki nasan akwai abunda ake miki wanda bakijin dadin sa..ko ana takura miki agidan nan ne?
Pls tell me don bazamu ji dadi hakan yana faruwa ba..u r our own remember?..
Ta dago ta dan share hawayen ta cikin marairacewa da shagwaba tace anty,
Bawani abu bane nima ina so na iya dafa abincin ne irin wanda bazai sa shi purgin ba,
I really tried hard amma nakasa iya irin nata..anty da kika tafi ko granny tace ban iya girki ba..
thy always think is awful
Kukan Shagwaban nata sosai ya burge anty abun tausayi ne amma sai ta bata dariya sosai..
Cikin son ta kwantar mata da hankali tace haba sarah”
Wannan ai ba matsala bne da kin fada min tuntuni da zan dauki lokaci na ko shekara nawa na koya miki girki har sai kin gaji”
Waye ya miki karyan bazaki taba iya wa ba da kike damun kanki?.
Tayi shiru ta dauko tab din ta nuna ma anty abubuwan data ke koya
Sai tace amma idan nayi zaiyi kama da nasu amma sam babu dadi
Dariya anty tayi tace comn share hawayen ki, wannan ai shirme ne sarah.
U will only get the fancy name and looks ko suma basu yi yayi dadi wani lokaci..
Yanzu yaushe kike so ki iya girkin…
More than anything tace a shirye nake anty ni ko yaushe ne ina so..
Ta dan shafe mata sauran tears dinta cikin kula tace toh shikenan.
Only u and i zamu na koyan girki a site dina ba ma sai mun fito main kitchen ba..is taht ok?
Tayi murmushi cike da godiya ta rungume antyn tace yes maaam ure the best
Haka suka rabu tace mata ta shirya anjima sai ta zo
Anan bangaren mahfud kuwa fada ya ma shabnam akan kar ta sake fadan wani magana akan sa baya so..
Hakan ta makalkale tayi fuskan kynwa ta bashi hakuri..
Ya wuce ya fita aiki…
Nan shabnam ta zauna cike da jin dadi,tasan ta sa sarah a wani hali don kuwa ta fara ganin hakan sosai a idanun ta…
Sai wajen bayan azahar sarahn ta fito da niyyar fara lessons din ta wajen anty warda anan sukaci karo da shabnam..
Wani irin bugu kirjin ta yayi,amma sai ta daure ta karaso
Cike da annoying smile shabnam ta tsare ta, tana kallon ta sai dai batace komai ba..
cikin dauriya sarahn tace lpya kuwa?
Sai ta dan sace da dariya mai ban haushi…
abun ya bata ma sarah rai ganin ta cimma burin ta sai ta sake ta ce im sorry,.kawai na tuno wani abu ne yake bani dariya..
Ta dafa Sarahn,ko kinsan idan muna tare da mahfud yadda yake da fuskan sa kamar baby ko dole yake sa shi kara kyau.
a hankali sarah ta watsa mata harara
Bata damu ba Cikin rawan jiki ta jawo sarahn kamar bata san metake yi ba ta nuna amata cartoon daga babban screen tace hey loook kamar wancan doli dolin…
Sai ta kwashe da dariiya .
Har sarahn ta kulu zata dakatar da ita dan sosai ranta ya baci what sort of nonsense is this..
amma sam shabnam bata hakura ba tace tsaya kiji ai ba anan abun ya kare ba,kinsan wani abu tunda yafara purging din nan sai nayi ta imagining how his cute face will be inside the toilet musamman idan yana nishi kinsan zawo baya jira ko.wani dariyar ta sake fashewa da shi loudly wanda ya sa tsakin da sarah take dannewa ya kufce.
A hatsale ta dan ja jikin ta zata bar wajen..
Murnan ganin bacin ran sarah ya dada sa shabnam ta daka tsalle ta dawo gaban ta tace haba sarahn wai har kinyi fushi nifa labari kawai nake baki..
Am just saying on a serious note, sai ta dan daure fuska” tace mahfud yana shan wahala a duk lokacin daya ci abincin nan naki, Uhhhggg i just wonder why he wont stop..
cike da haushi sarah tace sai ki je ki tambaye shi ko ki fada masa abunda ya dace yayi please excuse me shabnam..
Tayi murmushi ta tabe baki tace ok,wuce…ni dai nasan mahfud bazai taba dawwama ahaka ba
Kwanan nan ma zai aure wacce zata na bashi abun da ya dace dashi and tht way he wont have to purge… kaiwa nan tayi gaba ta bar sarahn anan
Kallon ta bai ishe sarahn ba sabida sosai kirjin ta ya ke mata zafi sosai,.so yarinyar nan ma tunanin aure take tsakanin ta da mahfud ?..how dare she
Wani irin bakin kishi ne ya rufe ta, sai da ta dauki bottle water ta sha sannan taji dai dai..
Da kyar ta iya dauke maganganun shabnam din aranta don itama yanzu ta soma jin shaukin ta nuna mata iyakar ta akan mahfud duk dama tasan karamar yarinya ce ba sarar ta ba.
Ko da ta samu anty, anan site din ta sai ta shiga koya mata simple tricks kafin ma su shihe kitchen din ta zaunar da ita tana zana mata su a paper tana gani..
Sosai ta sa hankalin ta sabida hankalin ta ya matikar tashi, sai ta quduri niyyar sai ta bada kowa mamaki..
Haka ta bi anty kitchen din site din nata suka fara ba wanda ya sani..
Duk zumudi da son taga burin ta ya cika haka ta dannne ta yi kokarin kwantar da hankalin ta na koyan abunda antyn ke yi..
Ita kuwa shabnam data ga yanzu sarah ta dauke mata wuta sai ta dada jin dadin haka,.irin ai da bakin ciki na zaki mutu.
Ita kuwa tana nan tana koyan girkin ta shiru ba wanda ya sani sai ita da anty..
Bangeren yazeed kuwa, ..
tun alhj nafiu da hajiya billy basu gane ba har suka fara fahintar shaye shaye kawai yasa agaban sa tukurum
Abun yayi tsamarin da har ya dena baiwa komai muhimmanci a rayuwansa
Sai yayi sati biyi uku baije aiki ba yana gida yana kwance tashi tunanin sarah ne yayi masa zare a ransa a kowani jan numfashin sa sai ya karo..
Shikadai yake jin abunsa
Ga safeenah ta wanke sa da buhun zagi, kwanan nan ta ce bazata aure sa ba..
A cewar ta wulkancin sa ya ishe ta,kullum sai am sa rana bazai taba zuwa ba
Idan an tambaye shi dalili sai yace babu komai
Amma zahirin gaskiya shine mummunan soyyayr sarah ne ya masa dabaibaiyi a zuciyan sa.
Sai ya rika dura ma kansa giya ya fita hankalinsa ko zai mance da ita ya samu sukuni
Sai dai yanzu abun yayi worsts da safeenahn ta fita harkan sa…da dai idan ya sha giya yana dan samu ragamar
Amma yanzu haka ko ya sha sau nawa ne baya jin saukin abunda yake ji akan sarah…
He madly wish that zai san inda take yaje ya bata hakuri bai damu ba koma yaya ne…..
Amma duk iya bincikin sa bai samu ko da news guda akanta ba,..
hapsy kam ma tabar aikin anan nigeria da mijin ta don mrs ruth da hajiya asma bakaramin wulakntata suke yi ba ..
Yanzu haka suke ta ammalin su da organisation din ba aje ko ina ba mutane sun soma koduwa da rashin sarah.
Yanzu adalci yayi karanci none of them is willing to stand up for them
yawancin programe din da sarah ta kafa na taimako sai aka soma watsar da su
Ba a basu kulawar daya dace
Safeenah da iyayen ta kansu kawai suke ginawa
Suna tara kudi suna taka kan duk wanda ya shige musu gaba basu damu da damuwar kowa ba..
Anan ma mrs ruth ta yi ta haden haden ta ma safeeenahn da wani dan gidan senator,not knowing that faisal ne babban abokin yazeed.
Dukan su basu sani ba amma bakaramin zumudi sukeyi ba iyayen nasu gama daya suna ta shirin yadda abun zai kasance sai ahada su..
Bayan sati biyu,shabnam na nan tana dada zafafa game dinta don ta kara kular da sarah sai ta hana mahfud sakat ko bai sani ba takan san yadda zatayi ta nuna ma sarahn shes more closer to him now.