SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

™/SUN6th/ 2019????
????????
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
????????
_A TRUE SENSATIONAL STORY_
~_Story written by_~
*SURAYYAHMS*????
*OFFICIALCATTY????*
*_WATTPAD_ @SURAYYAHMS_*
@ IG:Surriem-sule_
*#Lovestory2018/19*
*#romance#purefiction*
*#Destiny at fault..*
*Any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence”i give no permission for any comparison All my stories are strickly mine,beware copycats!.*
_this page is For_
_Xinnie nie_
_siyamah ta_
_and_
_hafsat Ay_
_PAGE4_
Shiru wajen ya dauka
Anan baba babaji ya yayi nuni da inna wuro yace baba kinji ai wai nace kin mutu?…
Sai ki tashi kiyi bayani ma sarki yaji da bakin sa ko hakan ne, Kema haka zuwaira sai ki kawo mana wayar naki a duba a gani ko da gaske ke kika kira ni ki kace min inna wuro ta rasu da har ni zan tura gambo taje gaisuwar rasuwa…
Tun kafin ya gama maganar sa Inna wuro ta soma tashi Ta bude ido a hargitse ‘”tace ni dai ban mutu ba gani da rai na kuma babaji bai taba cewa na mutu ba…nan ta fashe da kukan su na tsoffi, “ni da babaji ya kawo ni nan gari yana kulawa dani ace har shi zai laka min mutuwa? Kai Allah ya isa munafuki baiji dadi ba..halan ma so ake na mutu ake wani nokewa da karyan banza
toh ta Allah banaku ba.
Nan Zuwaira ta cafke da buhun zagi tana tsiwa a dole ranta ya baci tace “wayyoh Allah na shiga uku da sharrin duniya kowa anan dai ya san ban taba rike wayar salula ba tun da aka haife ni,..in banda raini da neman araba ni da miji na sai arasa wanda za a sa acikin zancen karya da makircin da ake so adaura masa sai ni? , tace duk karyan mutum sai an gano sa ai dama mu mun sani mutum bazai yi gudu dansa yayi rarrafe ba,
hmm watoh anje an shirya ma yarinya maganan karya da makirci ta zo tana zuba tana kukan munafurci toh wallhy nikam na fi karfin ku munafukai..
Allah kuma sai ya saka min sharrin da aka min bazan yafe ba
ta fashe da kuka,
Sarki yace ya isa hakan.
Nan baba babaji ya sake cewa toh,sauran maganan cewa na bata ma gambo suna,ranka shi dade ina ganin wannan kazafin ita kadai tasan da su don kai ma shaida nane ba ataba kama ni da wani abu ba bare miyagun kwaya,
hasali ma kai ka bani shugaban comiten zauren lura da zaman takewan matasan garin nan da tarbiyan su ko ba haka bane?
Kowa ya ce haka ne kam.
Yayi shiru kamar wani abu nacin sa arai yace Sai kuma maganan saratu “ya juya ya kalle ni yace saraatu Allah ya tsine miki albarka…
Nan waje ya kaure ana cewa “Ahhh ahhhhh haba wa babaji babaji kar ka tsine mata
Ayi dai hakuri mutane suka shiga bashi baki,
“Anan ya dada borewa Ya hau tafasa ku barni natsine mata dan uban ta”kuka ya fashe da shi yana kumfar bakin ya nuna ransa yayi mummunan baci,yana cigaba da tsine min.
Saratu dan ni ba uban ki bako?toh Amma Allah ya isa tsakani na dake meye ban miki ba a duniya da zaki laka min sharri don ki zubar min da mutunci na,..
A lokacin Ana rirrike sa kamar zai buge ni sarki ya tsime yana duban ikon Allah
Yace”Yar iska kawai duk abunda nake yi akan ki baki gani saida kika tona min asiri kika dauko cikin shegee? Sau nawa ina kama ki ina rufa miki asiri saratu yanzu ni na zamu miki abun tozartawa…
Anan ya shiga kwalla kira “Kai sageeru ena sageer nan waje yayi tsit aka juya ana dubawa ta ina sagirrr zai fito..
Sum sum ya fito gwanin tausayi a Gaban sarki ya hantsala sagir din kamar barawo yace zakayi magana ko sau na ci uban ka…ka fadi kowa yaji…marasa mutunci kawai..
Hankalin kowa ya tashi..ummma ta dada riko hannun na duka muna kukan zuci.
Ban san me naui ma sageer ba amma nasha mamakin Yadda ya hada labarin karya ya bayar akan neman mu.
Baba babaji yace” ka fadi meyake faruwa tsakanin ka da saratu agarin
Sau nawa kuma ena kama ku turmi da ta barya a dakin ka?
Sageer Yayi shiru cahn da dogari suka soma yunkurin zasu daka shi ya dago da kyar yace ” ayi hakuri sau dayawa..
wani irin kuka na fashe da shi ina kallon sa cikin razana
“Lahhhh ha ilah ha illahu la hawla wala kuwaata illa billhi
Hau hau hau aka soma tambade de da maganganu ana tabe baki..
wasu suna cewa dama chan sun sani wasu suna cewa tabbass sun sha gani sa tare da ni ashe abunda muke yi kenan?
Sarki ya daga hannu, ya mike tsaye ya ce sagirru ” kana nufi kenan cikin jikin saratu naka ne?
Nan ma yayi shiru jikin sa ne ke rawa sosai alaman ba da son ransa yake wannan shariar ba sai da sarki ya daka masa tsawa
Ba bata lokaci ya amsa da i..ina yace”eh kamar nawa ne
Anan ma aka sake kaurewa da salati wato tsabagen iya karuwan cin saratu ba ma da tabbacin waya bata ciki..?
Anan fa Kishiyon ummah na suka soma na su surutun cewa an zubar musu da mutuncin dangin su
Fada ne mummanna ya so ya kaure akayi chaaaaa Ana zagi na ta uwa ta uba sharrin da labarin da ban taba ji ba anan yau sai da aka fade shi kowa sai da tsine min Albarka iya isar ta.
Lokacin ummma ta mike tsaye dani ta bie ni abayan ta daga ni har ita kuka muke yi, babu bakin amsa maganan kowa..
Da kyar sarki yayi controling dattijai da matasa da matan garin da suke wajen
kowa yayi cirko cirko yana nina bacin ransa akan mu.
Musamman ma magana da ya zo da cewa kawai na so ne na bakan ta baba babaji na zubar masa da mutuncin sa.
Aka ce wannan ai cin Zarafi ne dan haka dole adauki mataki mai zafi akan mu ko ayi mana luli zaman garin nan sai ya gagare mu..
Da sarki ya sa aka dan rusuna akayi shiru sautin kuka na kawai ke tashi nan umma na ta daure ta tare numfashin sa …
‘tace ya mai girma Hamma kasani Bani da wani abun cewa anan…
domin kuwa gaskiya kamar hasken rana take idan har ta fito babu wanda ya isa ya sa hannu ya kare ta Allah shi zai isar mana da ni da diyata…
Ina kuma yi muku tuni da Allah bazai barku ba dana fada da ban fada ba zai biye mana haddin mu..kuje da gaskiur ku na rike rashin gaskiya ta da na diyata ayi mana hukunci.
Waje na so ya kaure da sharhi ,sarki yace a dakata masa.
Nan yayi dogon magana mai cike da bacin rai rashin jin dadi da masifa yayi Allah wadar da ni da ummah..
Ya kuma ce zai hukun ta sageer duk dama ba a tabbatar da nashi bane shikan sa kokunto yake.
Anan Aka taru aka bada baba babaji hakuri
Aka bashi baki sosai .aka danne sa kamar da gaske.
Sai sarki ya juya ya kalle mu rai abace yace ke kuma saratu kafin na dawo kanki ki rusuna gaban babanki yanzu anan gaban kowa ki bashi hakuri cin zarafi da bata sunan da kike so kiyi masa.
Jiki na har karkarwa yake yi tsaban kuka da takaici amma haka na shiga yunkurin sabulewa daga jikin ummah zanje gaban baba babaji na bashi hakuri…
Dam dam na ji umma ta riko hannaye ne..
Idanun ta ne suka kuma kafewa Alaman ta bushe zuciyar ta, tace”
Babu wanda zaki bashi hakuri anan saratu..hukunci kawai na roka mana.
mamakin abun da tace yasa aka soma tabe taben baki ana salleme wa.
A umarnin sarkin?
Kai wai me ake jira da gambo ne ba aci uban ta ba..
sarki ya ce adakata…
Gambo?
Umma tace naamm hammayo
“Ki kace bazata ba kowa hakuri ba..
ummah tayi shiru daga bisani tace in har ma kashe mu za’ayi ayi gaggawar yin haka sabida yata dai bazata taba bawa babaji hakuri ba..
kuje da gaskiyar ku Duniya ta ishe kowa riga da wando.
sai tassss umma taji saukar mari afuskan ta daga hannun babban aminin sarki..