SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Sai wannann yarinyar shabnam don ta nace sai ta bisu granny kuwa ta goya mata baya har da cewa agidan su zata zauna kafin iyayen ta su dawo
Cewa take ma malamin mai suna sheik suleiman ,akan ya ma mahfud magana ya rika koya mata karatu yana mata bita agida.
Theres no daubt that she’s his student don da girmamawa take kiran sunan sa.
Mahfud bai amsa ba, sai granny tace kar ki damu zai koya miki if hes less busy…
Tayi murmushi..
Anan anty warda ta sanar da su lokaci ya tafi su kawai ake jira..
Jikin sarah duk asanyaye yake da son ta sake jin wa’azin irin wannan masu bada mutum hope da karfin gwiwa
dan catalog din dake hannun ta ta rike tana duba channels din su mana social media..
Sam bata damu da surutun su shabnam da granny ba har suka isa gida..
Kowa agajiye yake din haka yawanci dakin su suka nufa straight..
Washe gari da safe sarahn bayan ta kimtsa ta shiga rubutu su tana sawa a searching…
Duka chanells din suka bayyana anan take gani videos da clips anan ma har da wasu malaman na daban wanda bata san su..
Ko wani video da title dinsa mai dauke hankali
Kamar zaga ka ance 70major sins
Ko 3 first to enter hell
Ko”ways to completly wipe ur sins…da sabanin haka masu sa sauki da jin hope ma zuciya
Abubuwa da yawa masu jan hankali da tunani ta gani..
A very Easy steps to know ur religion haka ta sa hankali akai tana bi its pure english so tana fahimtar komai ..
Kowanne daya taji sai ya dada bata shaukin sake jin wani
..da haka ta kalle 10 video clips wasu sun tsinka mata zuciya wasu sun sa ta hawaye da nadama..
Sai jikin ta yayi sanyi sosai,..
Cikin haka sai aka aika ta sauko kasa.
Its was 10 am satuday morning kowa na kan dinning table
Tana saukowa cikin nitsuwa ya dan daga ido ya kalle ta,haka ma granny da shabnam da dama take so ta san waye ita
A ladabce ta dan rusuna tace ina kwana granny ..
Cike da murmushi tace lpya lau sarah…jiya an gaji ko? Oya comn sit food is ready
Tayi murmushi ta zaga ta gaida anty warda sannan suka gaisa da mahfud..
Idon sa na kan ta amma ba wanda ya lura sai shabnam dake jira sarahn ta gaishe ta amma sai ta bita da slight friendly smiles bata ce mata komai ba..
Adan sakalce shannam Tace granny Bari na sa ma kowa nashi, sai ta mike ta fara kokarin serving din su
Cewar ta tunda yanzu nazo gida ni zan na kulawa da ke little
Kowa yayi dariya…
Sai ta taho daf zata zuba masa a hankali tace and you kitty.
Ya dan harare ta ya maida mata murmushi…
Kau da kai sarahn tayi kadan tana maida dan karamin nishi ciki
Kowa na ci sai granny tace gaskiya abincin yayi dadi..am sooo proud of you my princess.dariyar jin dadi ta mayar ma granny ta dan jingina da ita..
Tace kinga warda ko magana bata yi…
…tun kafin anty warda ta amsa ma joke din
Shbnam Ta dago cike da jin dadi tace ai ba ita kadai bane loook
Tayi nuni da mahfud dake ci a nitse “cikin shauki tace hesso enjoying it…
Kowa yayi murmushi
Shikam Tabe baki yayi ya dago ya dube ta, tace ko ba haka bane? Yayi maka dadi ko kitty.
If u want gobe da safe ma ni zan maka wanda yafishi dadi…
A lokacin Sosai sarah ta dago da kalle ta cikim wani irin yanayi,ita kuwa ko ajikin ta sai wani murmushi take ba kunya
granny tayi murmushi ta kau da kai… .
anty warda ce ta katse ta jokingly tace kai shabnam pls let him eat..
Yayi gyaran murya fuska ba yabo ba fallasa ya tashi ya sha drink dinsa ya ce to nikam ma na koshi…
Ya firta Excuse me…ya tashi yana shirin zamewa daga kan table din
Tace granny wai don nace yaji dadin abincin shine yace ya koshi..ta dan turo baki cikin sakalci….
A cikin ranta Ta tsani tayi magana yaki amsawa ko ya amsa ta half.
Granny ta dube sa abincin yayi dadi mana right ?
Sai ya dube su duka yace
Of cous,
Sai ya sauka ya fita..
Anan sarah ke lura tunda mahfud ya bar nan shabnam ta rage surutu granny ne kawai ke maganan ta ba kamar dazun da mahfud yaje zaune ba..
Tabe baki tayi azuciyan ta tana bin yarinyar da kallo tafara gane wani abu game da ita amma bata so ta kawo insecurities ma zuciyan ta sai ta share..
Ko kafin a tashi anan shabnam ta kasa zama sai tayi excusing dinsu itama tabi bayan sa ba wanda ya lura..
Anan bayan sun gama
Sarah ke ma anty warda hirar jiya cikin nitsuwa suke tadin su..
Granny najin yadda sarahn taje bayyana intrest din ta sosai akan haka..
Bata bayyana ba amma cikin ranta yayi mata dadi..
Anan ta barsu ta haura sama..
…chan sai sukaji noise din rikici da dan surutu
Muryan shabnam ne da granny, tana mata shagwavan mahfud yaki kulata bayan ance ya rika koya mata karatu..
Duk yadda granny tayi da shi sai yace hes busy sai anjima
Far daya anty warda tabsoma lura da chnge of mood a fuskan sarah amma sai ta kaucar mata shi da maganan abubuwan da ta sa agaban ta yanzu…
Haka har suka yi sati guda…
Sarah da shabnam basu taba maganan da ya wuce gaisuwa ba…
Kowa na soo ya gane nufin kowa..
Yadda mahfud ke yawo da idon sa akan sarah kuma yake nuna kula yasa shabnam ta soma dan jin haushin ta…
A kullum sai ta yi maganan ta ma granny duk dama granny ta dauka kishin yarinta ke damun ta..
Ita kuwa shabnam tun daga lokacin sai ta dau alwashi nuna ma sarah akwai wani abu tsakanin ta da mahfud azuciyar ta..
Tunda ta zo sai take Gani kamar hankalin sa na kan sarah..
Sarahn kuwa bata komai yanzu illah bin wayannan cahnnels din tana gyara imanin ta..
She became addicted Wani bin har abincin bata so ta sauko ta ci..
Shi mahfud idan yaga haka sai ya damu sosai yayi ta takurawa akan ta sauko din
Gani yake kamar damuwa ke sata yawan kebe kanta..
Amma azahirin gaskiya zuciyan ta take ginawa da imani da tsoron Allah…
Yanzu har ta kan bata lokacin ta sosai wajen yin chat na tambayoyi da duk abunda ya shige mata duhu da malamai online ana amsa mata su tana fahinta..
In just 2 weeks ta soma yin sallah akan lokacin sa cike da tsoron Allah..
Sometimes idan ta rude sai ta je wajen anty warda su biyun su suyi magana itake kara mata haske akan abubuwa dayawa babu wanda ya san da hakan…
Lokacin da abun ya shige ta sosai idan tayi sallah tunda ga raka atanl fajr zata soma ciko nafilan ta har ishai bata missing..
Sannan within the hours da rana ko da yamma da shike bata taba komai agidan sai take using tana karanta littafn aduoi da hisnul muslim tana koya dakanta…
The same naciya da turjiyan datake yi a da chan baya don career ta shi take applyng dinsa anan ma
Ko ma ace yafi don bangaren rayuwa ne mai muhimmnci wanda tayi nadaman yarda shi sosai.
Sai ta kaurace ma sauko wa tsakar gidan sosai Besides shabnam takan ruda ko ina da surutu kullum tana sa kanta girki da sauran abubuwa
Damuwar ta shine kowa ya san da gaske take yi akan mahfud
Idan ta takura sai ya mata bitan karatun ta basu karewa sai da fushi amma hakan take nacewa sai dai bata gansa na zaune ba
Sosai take zagewa ta bauta ma granny with the hope that za ace ita ce better macht dinsa…
Shikam damuwar sa bai wuce ya san meya sa sarah ta dan sauya akwana biyun ba…
Amma tafiye tafiye da aiki ya kan sha masa kai sosai sometime wajen ci abinci kawai suke haduwa..
Wasa wasa tsakanin sarah da shabnam sai kallo,maganan tsakanin su sai ya fara rauni sai ayi kwana uku kwana biyu basu tanka ba.
Gwara ma sarahn ta kan mata murmushi normal a wuce