HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Ranta yayi matukar baci da shi…duk da hakan bai damu ba don Shi da zuciyan sa ne kawai ya san irin halin da yake ciki amma dolen sa ya nuna mata nadaman sa da tsantsar kaunar dake addaaban sa akan sarah

badon komai ba don yana son ita tafada masa asalin abunda bai sani ba akan su..

Anan ta bashi labari gamsashu ta kuma hada masa da fada mai dauke da nasiha..

Don batayi tsammanin duk wanda yaji kan labarin ummah da sarah zaiso ya tozarta su ba..

Hakan ya sake sa shi wani halin nadama dama ashe bada son ran ummah tayi duk wannan abun ba?
Ashe ma alhj abdul azeez bai taba kwana da ita ba instead ma taimakon ta yayi,kuma ssa danjuma raping din ta yayi? Wayannan abubuwan ne bai sani ba

He tots a yadda ssa danjuma ya gaya masa ya kwana da ummah don ya taimake ta da kudin maganin saratu a asibiti ya dauka son zucuya yasa ta aikata hakan,duk laifin ssa danjuma ne bai fada min asalin zancen yadda zan gane ba..

But how dos it make sense now? dama bada niyyar alheri na ke son naji ba”
Hala shiyasa na amince da duk wani zancensa ba tare da dogon bincike ba..

A duk lokacin da ya tuno wayannnan abubuwan sai yaji zuciyan sa na zafi kamar zai tsage..

Sarah has gone trou so much to achieve her dreams which he use fake and delusionary love to destroy..

Yasan yayi mata illah a zuciya amma bai dame sa kamar rashin adalcin dayayi ma qaddarar rayuwar su ba..

Daga nan ya koma gida cike da tunanin mafita

..cikin ransa sai ya dauki alwashin sai ya goge ma sarah duk wani bakin paintyn daya kwaba ma sunan ta ita da mahaifiyar ta

Yasan Ko da bata fito sun hade ba sai ya warware abunda ya kulla da hannun sa…

Tun daga wannan rana
Ya fara neman hanya yana hade plan dinsa..
ya dauke sa sati guda da gama tsara su,..

Sai dai abu daya ne yake damunsa a kowani dare baya iya bacci
Wani bin yakanyi kukan idan ya tuno da yadda sarah ta bude masa zuciyan ta abaya ta yarda dashi fiye da misali…
Ta kuma tausaya masa beyonds oll odds…

Yau yasan Indai har haka matsayin sadaukarwan ummah yake da girma wajen sarah amma syill ta zabi ta saba mata sau dayaawa dan tafaran ta masa rai..

Toh lallai yasan sarah ta so shi da gaskiya,amma menayi?

Idan ya kawo wannan tunani dan dolen sa yake kurban giya idan bai samu ba haka zaiyi hawaye har bacci ya dauke sa cike da bakin cikiin kansa

Soyyayr sarah dake bin jinin sa tamkar wutar azaba ce, kullum da salon nadaman da take tuno masa da shi..

Farkon abunda ya soma yi shine sai ya shirya meeting tare da amina dagani yar jaridan daya kira don ta fara watsa labarin sarah da ummah na batanci..

Har yau Tana son tayi suna amma wannan karon yazeed yazo mata da labarin daya sata halin nadama itama..

He use his ways well ya nuna mata dole ne su hada hannu su fitar da gaskiyan sarah sabida basu mata adalci ba

A take Shi ya amince da kuskuren sa amma sai yake ganin idan yaje yayi confsssing kai tsaye yasan ba zai yi tasiri ba dole a wayar da kan jamma’a a kuma hankarar da manyan su na nan cewa ga asalin labarin sarah ba yadda aka fitar ba..

Aiki ne mai wuya ma dukan su amma haka amina dagani ta sa aranta zatayi sabida itama mace ce,data ji labarin she just tot of her self in thier place

dadin karawa yadda taga nadaman boroboro a idanun yazeed ya sa ta dada karaya da case din
Jikin ta sai yayi sanyi

Sai ta shirya musu cewa
Zasu sa tallar program din mai taken foundation din sarah data tafi ta bari

Idan mutane sukayi votiing za ayi live programme na debates akan tarihin ta kowa ya gani..

Ammma kashhh ko da akasa bai samu wannan daman ba

Sakamakon yanzu kowa ya danyi sanyi da hidimar whar tunda su hajiya asma suka dauki mulkin sai ya cire ma mutane interest..

Yanzu Yazeed baida wani mafita da ya wuce buga short memos da open diaries ana watsawa a social media houses
Facebook instagram da BB chaneels whatsaps tweets

Yadda yayi shine yana bada labarin zak zak abunda ya same su baya kama suna amma yana sa tanbarin foudation din ta”

A wani point din da ya san dole yaja hankalin mutane su so suji kuma su tabbatar wacece ake magana akai sai ya tsaya..

Wasa wasa sai gashi ya dawo topic of discussion….
Ana sharing ana reposting jama’a suna fadan ra’ayin su

Da haka suka fara samun votes na tv programe din daya ke so ayi live don maganan ya zama mai kargo ako ina.

Anan bangaren su mahfud kuwa kishi da fitina tsakanin shabnam da sarah sai bunkasa yake.

Tun mahfud baiya ganewa har ya soma lura da su
,.
Ga grannyn na kan bakanta na tunanin ma mahfud din aure.

Amma acikin kwanakin yadda shabnam ta zafafa bayyana son da take masa a fili ya sa grany ta shiga halin tausayin ta ..

Yanzu shabnam tasan sarah ba baya bace, sabida duk abunda tayi mata gorin iyawar sa sai taga tayi saurin koya ta kuma jajirce akai

Sarah ta dena yin sanyi itama yanzun nunawa take zata iya yin komai don ta kare masoyin ta.

Haushin shab bai wuce da sarah take kin biye mata suyi hayaniya ba a ko da yaushe fadan su awasa yake karewa duk dama na ciki na ciki..

Bayan wata guda da hutun mahfud ya koma bakin aikin sa…

Bangaren anty warda tunda ta lura granny ta sa tausayin shabnam aranta yasa ta ke dada jan sarah ajiki tana nuna mata hanya..

Cikin haka take shirya ta a hankali ta yadda zata amshi sabon rayuwar zama da namiji nan gaba,wani bin sarahn ke cewa anty wai meye anfanin wannan ne ?

Amma bazata taba fada mata ba sai dai tayi murmushi tace” ke dai kisha zai yi miki amfani ajikin ki. .Kamata yayi ya mace ta zauna ta ciki kasaitacciya ba a waje kurum ba..
Sai suyi murmushi” antyn ma takan sha wasu wasu tana amfanin da su sarahn tana gani tana koya..

Da shike ma ba dayawa take bata ba Wani bin sai tayi kamar ta dago kan zancen amma wani bin kuma sai ta waske..

Yanzu sarah tana izun ta na biyar kullum sai tayi bita, kamar mayya wata rana ko dan tabada shabnam haushi zata nace da karatun..

Gashi mahfud baya ce ma sarahn A’a a ko wani hali ne,sai ka lura da soyayyar nasu yanzu ya kai wani matsayin da bazai taba karye wa ba..

Ranar duka suna zaune a falo,shab tana kusa da granny ta langwame sabida taji maganan iyayen ta zasu dawo nan da kwana hudu su dauke ta..

Tun adaki take kukan ma granny cewa bata so ta tafi ita kuwa granny so take shabnam ta kaucar da wasa da kwane kwane for once ta fada nata asalin abunda take ji akan mahfud..

Anan sai ga waya yayi kara,…
Mahaifin mahfud ne ya kira anty warda Hankali tashe yake sanar da ita cewa yana tare da mahfud a asibiti ya samu minor car accident ya buga kansa,….

Innalihhi wa enanna ilaihi rajiun ta fada tare da lumshe ido wanda ya sa duka suka dubeta.

Granny ce ta mike tsaye tace warda?meke faruwa

Anty wardan bata amsa ba ta shika tanbayar mijin ta ko yaya yake yanzu?

Anan duka suka mike kirjin sarah sai da yayi bugun tara ayayin da ta karaso kusa da antyn tare da granny..
tana ajiye wayar ta kalle su tace mahfud ne yana asibiti…

A rude sarahn tace what?anty meye same shi is he alrrrrigt? Ina yake yqnzu muje mu duba sa.
Grannyn ma hakan take fada cike da damuwa.

Ba wanda ya lura da shock din da shabnam ta shiga ciki..

Ita dai tana jin tanbayoyin su sarahn ne amma ta dade da shiiga halin damuwa da bugun zuciya kwana biyun da suke gwabza kishi da sarah akansa haka kawai kaunar sa ya dada zafafa aranta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button