HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Haka suka dunguma suka kai asibiti,
Lokacin an shigar da shi ana dubawa

Bugu ne kawai babu rauni amma sai yayi dogon suman da ya sa shi shiga complications dayawa alaman ya taba masa wani waje….sukan su likitocin yanzu suke so sugano

Kasa zama sarah tayi tayi nan tayi nan tana leke zuciyan ta cike da aduan kar wani abu ya same shi..

Sai yanzu granny ta lura da shab dake makale jikin cushion dake wajen ta sunkuyar da kanta kana ganin ta kasan tana cikin wani hali ..

tausayin ta ya sa granny ta zo daf da ita tace shab dear are you ok? Cikin nitsuwan da sanyin jiki ta girgiza kai tare da sauke hawaye…
Ta damu sosai kirjin ta har na mata zafi

Jawo ta granny tayi ta shiga rarrashin ta a hankali da kyarr ta sake kukan damuwa mai shake da son shi datake dannewa.

. ..anan duk sabida damuwar da shabnam ta nuna ya sa suka dan kaucar da nasu damuwar aka bada juna karfin gwiwa..

…after like 9 hrs mahfud bai farfado ba..

Nan anty warda ta taho kusa tare da dafe sarahn da har iyanzu bata zauna ba kanta kawai ta jingina da windown dakin dayake ciki ta bata shiru tana tinanin sa.

Tasan inda zata fitar da yadda take ji yanzun zata daga nusu hankali amma tana lazimin mahfud zai tashi ko dan ita..

Hannun ta anty warda ta jawo ta hada su waje daya da shabnam din ta zaunar da su..
Cikin dan masifa tace wato bazaku nitsu ku kwantar da hankalin ku ba ko?
Haba da Allah ,pls calm down he s going to be alright ok?

gyada kai sarahn tayi a sanyaye ,nan zaazafn hawayen ta suka sauko silently..

Granny ne ta rike hannun ta cike da tausayi tace sarah dont uhm uhm…
kamar wacce Tasan meke gudana aranta..so take tace an dauki dogon lokaci mahfud bai farfado ba..tsoro ne fall aran ta..amma bata furta ba

sai shabnam ta riga ta furta su afili cikin kuka. …
Cewa take to meyasa haryan zu bai tashi ba ?sai ta maida kukan ma granny dake faman saissaita hawayen sarah….

Anan ma wani sabin rarrashin akayi,cikin haka saiga doc ya fito tare da mahaifin sa.

Duka suka mike tsaye suna tanbaya nusamman granny dake so tayi panicking anan wajen cikin tashin hankali..

Doc ne ya ce mata ta kwantar da hankalin ta hes fine..wani jijiya ce ta dan bugu ta dan matse sai da suka jira ta warware kadan kafin ya samu ya farfado..

Amma zai bukaci hutu sosai batare sa yayi kykwan motsawa ba akalla na awa 26hrs..

Allah suka mika godiyan su,lokaci guda shab ta dawo murna ita kuwa sarah hawaye ne kadan akan fuskan ta har yanzu…

Cike da zumudi suka shige ciki dubasa yana kwance shiru

White shirt din suit dinsa ne kawai acikin sa an danyi releasing shirt din daga shorts din sa.

A hankali ya juya ya kalle su sai ya sake murmushin tsakona yadda ya ga damuwa boro boro afuskn su
cikin ransa yake cewa sai kace bazan mutu wata rana ba..

Granny tayi masa light peg agoshi tare da masa adduan sauki da larabaci while anty warda na rike da hannun sa tana comforting dinsa da motherly love smiles…

Alokacin Idon sa na kan masoyiyar sa da suka hade ido ” a hankali yayi mata kallon are u ok?

A shgwabe Ta gyada kai tace ya jiki? How are you feeling now, sai muryan ta yayi cracking alaman zata soma masa kuka ….

Sai ya rufe mata shi da murmushi ma sanyi yace da sauki. …

Shabnam na lura da duk conversation din da sukayi a zuciyan su anan da duk wani motsin da suke yi na reaction da idanun su

Tsaban haushin su ya sa ta boye nata gaisuwan sai ta tsaya daga gefe kamar tana jin kunya while bakin kishi ke bin hanyoyin jinin ta..

Grannyn ce ta lura da shirun nata ta jawo ta ita ke fada masa yanayin yadda ta damu da zu ta jawo ta kusa da shi..

Tace gashi nan ai ba abunda ya same sa ta shafa kanta cike da kulawa

Mood dinta kawai ya karaance yayi Murnushi ya dan riko hannun ta yace ok , Am fine now ki dena damun kanki ko…ta sake murmushi cike da blush ta gyada kai..

ita dai granny bata san ya zata fidda wannan case din ba..

Da cahn ta dauka zuciyan yarinta ke saka shabnam tunanin soyayya da auren mahfud

Amma yanzu tana kallon real true feelings a idanun ta

Anan aka sallame su suka koma gida

Dan maganar da sukayi asiibitin ya sa shabnam ta dawo da karfin gwiwar ta atleast ai yasan ta damu da shi sosai yanzu kam

Ahaka suka zauna site dinsa suna kula da shi har lokaci ya dan ja..

Shi dai idanun sa na kan sarahn da shike ma ya gama karantar halin da ta shiga ciki fiye da yadda kowa zai iya gani…..

Haka aka dauki kwana biyu ana jigilan kula da shi duk dama ya riga ya mike tarwal ba abunda ya nuna na ciwo ajikin sa..

Dad din sa ya sa ya dan hakura da fita amma sam yaki, zaije aiki kam amma baya dadewa zai dawo..

Anan kwana biyu su ka shiga ta amali wajen rige rigen zuwa masa gaisuwan ya jiki da safe..ko sarahn ta riga zuwa ko ta zo ta samo shabnam..

Yau ana saura kwana guda iyayen sahbnam su zo gaba daya da haushin kanta ta tashi bare aje ga kowa..

Tunda ta tashi akan gado bata fito ba bare tayi murmushi..

Granny tayi har ta gaji ta kyale ta..
Ta sani sarai akan maganan tafiyar ne take fushi amma shabnam bata fito fili ta fadi damuwar ta na asali ba bayadda ta iya.

Ita kuwa shabnam yau ta yanke hukuncin yin hakan amma tsoro fargaba da bugun zuciya ke damun ta ba akan komai ba sai akan yadda mahfud zai dauki maganan inyaji.

Indai akan sarah ne, gani take bata isa ta hana ta zama da wanda take kauna ba besides ahe ready to do anything don ta mallake mahfud da familyn sa.

Anan bayan ta kammala plan din ta sai ta fito yammah ne dab lokacin dawowar sa….

Daga saman bene dake hango parking space sarah ta hango sa ya sauko a mota,.. farin ciki ne ya mamaye ta sai tayi sauri ta dauko foam ballon rod dake wajen wanda take wasa da shi bayan ta kammala bitan ta,wato abun kumfa ne da ake hurowa sai yayi manyan balls yana sauka da kansa zuwa kasa kamar snow ball ko kumfar omo..

Tana tahowa ta tsaya daff inda zai bi daga sama ta huro su da yawa sukayi manya da kananan balls masu kyau
Cike da so da kauna Ta hure wajen sa
Tun daga saman suka yi flying all over the place bai hankara ba har gefen kuncin sa.

Dama yana taba abu zai fashe cike da mamaki ya dan shafe gefen cheek dinsa ya daga kai sai ya hango ta…

suna hade ido da abun a hannun ta take waving dinsa tana murmushi mai sace zuciya gaba daya balls din suka dada saukowa akansa beautifully…

” kallon ta yake cikin yanayin kauna Lokaci guda ta sake sace komai na shi,ji yake a duniya don shi kawai akayi ta.

Dan karamin murmushi yayi ya mata alaman i love you in 143 da yatsun sa da kuma shape din heart,itama tayi d same bata hankara ba sai taga yayi blowing kiss a iska tayi dan dariya ta cafke lokaci guda kuma ta boye fuskan sa ta juya masa baya tana dariya..

Abun yayi masa dadi He wass so in love and happy da sauri ya shigo don ya hauro ya same ta..

Shabnam da ke zaman jiran sa ganin bayan sa kawai tayi yana haurawA chan saman benen ta steps

Cikin mamaki Sai ta taho itama ta shiga bin bayan sa..

Itako sarah tana kan leken sa she tot da ta juya masa bayan yana nan wajen ne.
Har zata juyo sai suka ci karo da shi…
Mamakin ta ta ke boyewa da dan karamar Dariya ta danyi ta sunkuyar da kanta “yace ina abun yake nima abani na rama..

Cike da jin kunyar sa tace babu, ni ka je ka huta karatu zanyi…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button