HAUSA NOVELSAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

SAMARIN SHAHO Complete Hausa Novel

Mahfud Bai dawo da wuri
Ba sai chan ana neman bakwai saura.

Anan ma yana shigowa ta taso da fara’ar ta ta koma jikin sa suna gaisawa cikin tarairaya kamar ba arms dinsa tayi bacci ba…

Ko da ya taho yana tambayar ta yazeed din bata ce eh ko a’ah ba ta tsura masa ido irin ni ban sani ba din nan..

Sai ya taho kusa da shi ya daga sa..ya tambaye sa ya jikin

cike da kulawa ya sa shi ya kimtsa yayi sallah shida kansa ya gyara masa gadon ya sake zaunar da shi..

Ko daga ido bata yi,she just wonder wannan wani irin ciwo ne haka da bazai warke ba.. Bayan ta tambaye sa mai zai ci
Anan mahfud ya matso kusa da ita yace babe baki ce ma bro komai ba fa”
Ta dan noke kadan ta dago ta dube sa tace ,sannu ya jiki….

Da kyar ya murmusa ya furta da sauki daganan tayi shuru abun ta..

Shidai mahfud sai yaga kamar sarah bata damu da wayannan famlyn nasa ba amma this is just the first time sai yace hala zasu fahimci juna anjima.

Sai ya sa ta hado musu shayi kamar yadda yazeed din yake bukata ba musu ta shiga hadawa suna hira kadan kadan da shi duk idanun sa da hankalin sa na kanta..

bayan ta gama 2cups kawai ta kawo nan mahfud ya dauki daya ya mika ma yazeed ita kuwa sai ta koma gefe ta zauna..

yace malama bazaki sha bane? Bata kula ba ta gyada kai a hankali…yace akan me comn taso ki xo nan kisha…haka sam taki sai ya shiga lallaba ta shi dai yazeed shikadai yasan yadda shagwaban nata yake konasa hakan ya sa ya kasa shan shayin sai ya rike a hannun ya na jin su…

chan da mahfud ya juyo suka hade ido yace kaima bazaka sha bane?
Yayi shuru sabida yasan yana wani kyakwan motsi hawayen kishin zai zubo kasa.

sai mahfud ya karbe cup din da niyyar basa abaki a hujajan ta taso ta rike hannun nasa da wani irin kallo wanda ya sa ya sake mata cup din bazata.

tana karba ta zauna kusa da yazeed suna fuskntar mahfud din tare ,,..nan ta juya fuska ba yabo ba fallasa tace ma yazeed kaga rike shayin ka ka sha da kanka…

ai bro din ka bai iya jinya ba sam in ta shine bazaka warke ba komai sai ya maka anan kamar jariri..am sure ko da mum ne bazata so ka rika sake jikin ka ba emmmmm..

duka sukayi murmushi

Musamman yazeed don baiyi tsammanin zata yi magana mai tsayi da shi haka ba..

Hakan ya sa yadan ji dama dama har da cewa sure!! gaskiya ne i wll just try now…

Bata sake kallon sa ba ya shiga shan shayin a hankali yana satan kallon ta..

mahfud yaji dadi yace toh shikenan ai kema sai ki dauka kisha wannan ni zan hada nawa tace noooo hero bari kawai,zo nan ka zauna ta dan jawo sa…

yana zama ta shiga lallaba sa tana petting dinsa cikin salo”cewar ta ita ta isa tana kusa yaje ya hade shayi da kansa?..anan sai ta jawo tea cup din ta sa tea spoon dan dai dai ta soma bashi a baki kamar bata san da mutum agefen ta ba..

Cikin kulawa take bashi kamar jinjirin da ake kafafa kafa da shi shiko mahfud ya sakankance abun sa sai karba yake yana mata surutu.

tsaban takaicin su ya sa yazeed ya sake rike shayin yayi shiru ji yake kamar wuta ake hurawa akirjin sa..

haka suka kammala duka zauna hira kadan kadan ake wanda yake dada sa yazeed wani hali kiris ya rage yayi bursting as early as 7.40 sai ga sallamr hjiy billy

daga gefen sarahn mahfud ya mike tsaye ya taro ta da murmushi
ta amsa shi kam amma hankalin ta nakan sarah ganin bata ko kalle ta ba ya sa ta maida kallon wajen danta taga ya yake ciki..

bayan sun gaisa dukan su,…tace ma mahfud yaje wajen doctor ya jiyo mata kan maganan ciwon

Taasan doc baizo ba tukunna amma tana mugun son ta samu lokacin da sata ma sarahn magana akan yazeed..

yana tashi zai fita itama sarahn ta mike zata bishi…

haushi ne ya turke hjy billy amma sai ta rufe da murnushi tace “ina zakije kuma yata ,comn dawo nan ai yanzu zai dawo ko?

tana shirin kawo bori ya dan zare mata ido yayi mata alaman ta zauna yana zuwa..

Yana fita ta dan ja tsuka cikin ciki…ko zama batayi ba hjiy billy ta hatsaka ta hada da haushin kininibin data ke musu tun jiyan tace sannun ki gimbiya hamshakiya burin ki ya cika kin wargaza min yaya na hankalin ki ya kwanta ” toh ta Allah ba naki ba ba abunda kika isa kiyi wanda Allah bai yi ba…

shikam yazeed lumshe idanun sa yayi baya son mum dinsa ta rika overacting amma sam bata ji..

wani irin sanyin kallo sarah tabita da shi mai shake da hararar sama da kasa..tace ohh mumy dama kin sanni ne?uffff Ai ban sani ba..

Hjy billy Tace com shut up sarah..don na nuna bamu sanki ba dosnt mean anything in gaya mikii….kema kinsan sabida yazeed zan sararar wallhy da tuni kinsan kin shiga rayuwar yayan bilkisu,yau da sai na nuna miki ni uwace ma mahfud din dakike gadara da shi nonsense..

“ko alaman damuwa bata nuna ba sai ma ta nemi waje ta zauna kafin tace “to ni ina ruwa na,

dan baki san ni ba ai ke kika dama wannan duk ke ta shafa mum..u don’t know me i just dont care huhh..!!

“Ni dama Ba damuwa ta nazo inda kike ba inan nan ne kawai dan shi…so suck it up kuji dakan ku naji da nawa ni bana son hayaniya pls..

baki abude hjy billy tace “Iyyye ,sarah bukar mani kike fadi ma hakan how dare you?
Ta daka mata tsawa cikin haushiN rainin ta

abun ya ishe sarahn duk dama batayi tsammanin jin haka da gare ta ba..amma its seems like hajy billy ta gama rufe idanun ta sosai danta kawai ta ke ji

“nan sarahn ta mike tsaye tace”ohh mum pls duk abunda kikayi da rayuwar ki anan damuwar ki ne idan kina ganin akwai abunda zaki iya min sai kijira mijina ya shigo kiyi agaban sa

kasa kasa tace Wannan ai munafunci da ruwan ciki har ana ikirarin da ashe ma tsoron sa ake ji..to ni bana tsoron kowa sai Allah.

A zuciye ta hatsala ta sake daka tsawar …sarah bukar….!!!

Da Dagon murya sarahn ta maida tace mata and… Lingard mum…dont you eva forget that.. kaiwa nan ta fice tare da bankade musu kofar dakin sautin tsakin ta ya gauraye su duka

mamaki da haushi gaba daya ya sa ta shaking ta juto zatayo magana yazeed ya ce mum pls stop it..

u just overacted meyasa zaki daura mata wani laifin kuma bayan yafiyatta nake nema mum i was the one who offended sarah why are you insulting her

A hatsale Tace an zage ta ita din waye”duk ta dalilin ta ka shiga wannan halin wai shin baka ganin kanka ne..u almost die here i just cant stand her anymore ita ta jawo duk wannan masifan ..

yace enough mum i love her idan kina fadan haka bana jin dadi pls relax ki rika lallaba ta kinji mum,bana so kina takura mata she might just get upset bana son ranta ya baci dani again.

tsaki hajiya billy ta ja cike da jin haushi tana bambami,
Daurewa yayo ya sauko ya shiga lallabata da cewar ta yo hakuri akan sarah..yace “insha Allah ma yau zamu koma gida achan zanfi samun daman gaya mata abunda ke raina emm..

Cikin haka sai gasu sun dawo tare wani uban hararar kasa kasa suka sauke ma juna da hjy billyn.

Zaman lokaci kadan yayi yana musu bayani abunda likita yace nan sarahn ta tada masa hankali sai dai yakaita ta ci abinci ita yunwa take ji.

Gaba daya sai da ta kular da su hjiya billy ji take kamar ta kashe sarah ta huta.

itAko sarahn asali bata da niyyar shiga damuwar su amma ganin take taken hjy billy yasa ta daura dammaran cewa bata isa ta sake shiga rayuwar ta ba…

haka suka fice daga asibitin tun safiyar bata bar sa kuma ya dawo ba sai chn yamma..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button