SARAN BOYE 76

“Ni da shi twins ne. Muna tsananin kamanni har takai jama’a basa iya banbantamu inba mahaifiyarmu ta faɗa ba. Duk da itama wani lokacin rikicewa takeyi. Suna ɗaya iyayenmu suka saka mana wato Goshpower. Takai inhar ka kira ɗaya a cikinmu sai mu amsa maka mu duka. Mamanmu ta taɓa faɗa mana kaifin basira da muke da shi da farar fata tasa har ana dangatamu da wasu sunaye. Wasuko na tsoronmu da faɗin mama debora ta haifi waɗanda ba mayu. Wannan ba sabon a bu bane daga hallayar mutanen ƙabilarmu da yankinmu wajen danganta mutum mai fari da ƙyawun jiki da suna na tsoro. Mutane basu fara samun basirar banbantamu ba sai da muka fara girma halayenmu suka fara banbanta tsakanina da ɗan uwana. Mu duka munada kaifin basira da wayo, sai dai kowa da yanda yake gudanar da tashi. Duk inda gaskiya take zaka samu ɗan uwana a wajen, niko saɓanin haka shine zaɓi na. Kullum cikin takalo rikici nake wa iyayenmu, ɗan uwana kuma bai gajiya da bayyana gaskiya idan an tambayesa. A duk lokacin kuma da nai niyyar cutar da shi akan wannan abu da yakemin sai bana samun nasa. Dan ko faɗa zamuyi yafi ƙarfina. A haka dai muka kammala primary, akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninmu, amma bamu cika zaman lafiya ba da zama waje ɗaya na dogon lokaci. Bayan secondary skull muka wuce jami’a, inda anan mabanbantan halayenmu suka sake bayyana. Duk da mu duka muna karatu ni a koda yaushe hankalina nakan mata, sannan duk wani abokin banza zaka samu nawane. Hakan na ɓatama ɗan uwana rai, tun yanamin nasiha da faɗamin gaskiya har yayi zuciya ya daina, daga ƙarshema muka raba ɗakin kwana, dama ba department ɗinmu ɗaya ba. Haka dai muka cigaba da tafiya, kafin mu kammala jami’a na zama riƙaƙen mara jin magana dan har harkar ƙwaya na fara, sannan na shiga cikin ƴan Cult. Mun kammala degree ɗinmu na farko, ta hanyar ogan babanmu muka samu taimakon tafiya ƙasar Italy ƙaro karatu. Daga nan ne labarin canjawar komai ya fara. Dan watanninmu biyar kacal a makarantar na sake canjawa daga duk yanda aka sanni. Idanuna sun sake buɗewa sosai harna fara harkar cocaine. Ta hanyar wanda na fara harkar Cocaine ne idanuna suka sake bushewa. Ya kutsa dani cikin manyan mutane konace tantirai dake juya duk wani iya shege na duniya. Nasha wahala ba kaɗanba wajen karɓar horo daga garesu har takai makaranta ma na daina shiga duk da yawan damuwa da kirana da ɗan uwana keyi, tare da yawan ƙoƙarin son sanin abokan mu’amulata. Muna shekarar ƙarshe daya kamata mu kammala degree ɗinmu na biyu ɗan uwana ya haɗu da matashiyar Balarabiyar saudia mai suna Anum. Itama karatu tazoyi, wannan kuma shine zangonta na farko. Sun fara rayuwa kamar abokai a hankali suka rikiɗe zuwa masoya. Sam bansan da wannan soyayya tasu ba sai da tai nisa, muna ma gab da kammalawa. ko nace ɗan uwana na gab da kammalawa. Danni tuni na yaye kaina daga zuwa makaranta. Sai dai nakan shigo lokaci-lokaci saboda harƙallar dake tsakanina da ɗalibai ta kayan shaye-shaye. A wani shiga da nai cikin makarantar ne na haɗu da Anum, wadda ina cikin tafiyata tazo tasha gabana, a zatonta ɗan uwana ne. Da farko na harzuƙa matuƙa, sai dai ƙyawunta yayma idanuna barazana da danne fushina. Cike da tsokana take kallona tana dariyar wai yaushe nasai kayan jikina?, ita dai basu mata ba. Naji haushin kalamanta amma saina fuske na barta akan ɗan uwan nawa ne. Kiran wayata da ogana yayine yana min neman gaggawa yasa na sulale nabar Anum da nufin zan dawo gareta. Daga haka bansan yanda ta ƙareba bayan taga ɗan uwana. Shin ya warware mata mu ƴan biyu ne, kokuwa ya karɓa mata matsayin shine ni?. Kwana biyu da yin haka na dawo cikin skull neman Anum sai dai na samu labarin cewa sun wuce saudia ita da ɗan uwana. Samakon zuwa da yayunta biyu sukai suka ganta da ɗan uwana daba musulmi ba”.
“Duk da bana shiri da shi hankalina ya tashi matuƙa, dan kodai babu komai shiɗin ɗan uwanane ai. Duk zatona ko zasu cutar da shi ne? Naso binsu duk da bansan ina suka nufaba sai kuma wani aiki ya sake taso mana zuwa ƙasar Germany. Haka na tafi al’amarin ɗan uwana na damuna a cikin rai. Kamar wasa sai ga wannan tafiya ta jani tsahon wata huɗu, lokacin da muka dawo ƙasar Italy saina samu munyi graduation, course mate ɗina duk sun kama gabansu har ɗan uwana. Na bincika Anum sai na samu wai itama tabar makarantar. Daga jin haka sai kawai na nufi Nigeria, a zatona ɗan uwana ya koma gida. Amma kash sai na iske saɓanin tunani. An dai tabbatar min yazo wata biyu da suka gabata wajen rasuwar mahaifinmu, nima anta nemana amma ba’a sameniba. Ko damuwa banyi da mutuwar babanmu ba, sai dai jin ogan babanmu ya bama ɗan uwana maƙudan kuɗin aikin da mahaifinmu yay aiki a ƙarƙashinsa dan yaje ya juya hankalina ya tashi na bukaci sanin ina ɗan uwana yake?. Mamanmu bata saniba, abinda kawai ta sanarmin shine ya sake barin ƙasar, bakuma susan ainahin ƙasar daya tafi ba. Yadai bar musu kuɗin da zasu ishesu, tare da musu alƙawarin nanda shekara guda zai dawo musu da daddaɗan labari. Nayi ƙwafa kawai bance komaiba. Daga haka na tattara kayana zan koma. Sai dai kafin na wuce na haɗa harƙalla da abokaina akan zanke turo musu kaya insha ALLAHU suna saidawa su tura min kuɗin. Sunko amince tare da min alƙawarin bazasu bani kunyaba. Daga haka na tattara na koma inda na fito, babu wani zancen nasarar da naci a karatuna dana zauna naima mahaifiyarmu. dan koma ban faɗaba nasan ɗan uwana ya gama tona mata dukkan zance a kaina”.
“Ban sake sanin ina ɗan uwana yakeba, ba kuma mu sake haɗuwa ba sai bayan kusan shekara, ana gab da zai cika alƙawarin daya ɗaukama iyayenmu na komawa garesu da daddaɗan albishir. A lokacin naje kai kaya ƙasar Syria ne. Kwatsam zamu shiga wani shopping mail ni da abokin tafiyata sai ga twin Brother ɗina tare da balarabiyar yarinya dana taɓa haɗuwa da ita a Italy a bazata. Da gani har shi babu wanda baima ɗan uwansa kallon mamaki ba. Hakama mafi yawan jama’ar wajen kallon mamaki suke mana da al’ajabi. A zahiri dai gashi muna tsananin kamanni, amma a shigar sutura da yanayi bama muyi kama da ƴan yanki ɗaya ba. Ni na fara sakin murmushi ina kallon jaririn dake rungume a kafaɗarsa, sannan na kalli Anum na sake kallonsa. Goshpower kaine anan kuma?”.
“Shima Murmushin ya saki a karo na farko yana girgiza min kai, yace my twin bro, wannan suna yanzu na bar maka. A yanzu sunana IBRAHEEM ne, wannan matatace Anum, ga yarona Abdul-Maleek. Woow!! Na faɗa ina dariya da tafa hannu, kafin na miƙa hannun ya ɗoramin jinjiri Abdul-maleek. Yaro ƙyaƙyƙyawa mai tsananin kama da mahaifiyarsa, sai dai ya kwaso kamannina nima ni da ɗan uwana kaɗan. Ganin dai da gaske munsan juna abokin tafiyata ya barni tare da su yana faɗin mu gaisa shi zaije ya kai kayan zuwa anjima saimu haɗu. Na amsa masa da jin daɗi, dan koba komai ina buƙatar keɓancewa dama da ɗan uwana dan naji yaya batun kuɗin daya amso a Nigeria suke. Dan ko kaɗan banji wani damuwa da fahimtar ya koma musulmi ba. Kamar ya shiga raina kuwa. Sai ya buƙaci mizai hana muje gidansa kawai, ashe nan yake da zama yanzun. Mun shiga danƙareriyar motarsa dani da ke wahalar nema da shiga haɗarin rayuwa ko wadda bata kamitaba bani da ita. Wannan abu ya sosamin rai, amma sai ban nunaba muka shiga, suna gaba shida matarsa niko ina baya tare da jaririnsu a hannu. Al’amari bai kuma tadamin hankaliba sai da muka isa ƙaton gida da yaji kayan more rayuwa a matsayin wai nashine. Lallai nasha kallo, cikin mintuna kalilan kuma matarsa ta gama cika gabanmu da kayan ciye-ciye. Sai bayan munci mun ƙoshi mukai gaisuwa da tambayar bayan rabuwa. Bai ɓoye min komaiba daya shafesa bayan rabuwarmu”.
Yace, (Ɗan uwana kamar yanda na sanar maka wannan itace matata, mun haɗu a jami’ar Italy dakaƙi nutsuwa ka ƙarasa. Da farko tsakanina da ita abota ce, sai daga baya muka fahimci muna son juna. Sai dai ta tabbatarmin babu yanda aure zai kasance a tsakaninmu saboda addinimu ba ɗaya baneba. Hankalina ya tashi domin ina tsananin ƙaunarta. Nai alƙawarin inhar zata yarda mu zama ma’aurata zan koma addininta. Ta sake tabbatarmin indai saboda aurenta ko soyayyar da nake matane zan zama musulmi wannan bazaisa ta yarda ta aureniba. Na musulinta kawai domin ALLAH badan tarayyarmu ba. A hakanma na yarda na amince, a randa muke shirin zan karbi shahada aranar ƴan uwanta biyu sukazo dubata. Sun nuna mata tsantsar ɓacin rai nayin tarayya dani, harma yanda ake musalta musu a cikin makarantar mun zama tamkar wasu miji da mata. Dagani har ita hankalinmu ya tashi muma. Dan tunda nake da ita ko maganar banza bata taɓa shiga tsakanina da itaba. Bata taɓa yarda ko zama gab da juna munyiba balle akai ga aikata wani abu mara ƙyau. Ni bamma taɓa kawo wani mummunan al’amari tsakanina da itaba kamar yanda nasan itama hakanne daga gareta. Kawai dai ALLAH ya haɗa jininmune kawai, kuma ina koya mata karatu. Duk yanda mukaso su sauraremu sunki, daga karshe ma suka tattarata wai zasu wuce da ita. Banyi ƙasa a gwiwa ba wajen tattara duk abinda nake da shi na bisu batare da sun saniba. Sai da muka dira ƙasar saudi-arebia suka fahimci jirgi ɗaya ma muka shiga da su. Sun nuna jin zafin binsu da nayi, amma sai basu hanani na bisu har gidansu ba. Koda muka isa gidansu sunma iyayensu bayani akan dukkan alaƙar dake tsakanina da Anum. Maimakon nai zaton za’a koreni sai naga saɓanin hakan, dan kuwa sun yarda da bukatata ta zama mai salla. Amma babu zancen aurena da Anum, dan suncemin yarinyarsu karatu takeyi. Duk da na shiga tashin hankali saina amince a hakan zan musilinta ɗin. A take kuma na amshi shahada. Komawata musulmi ya sake canja komai, dan kuwa sunmin gagarumar ƙyauta maiban mamaki ta maƙudan kuɗaɗe wai na riƙe kaina, tare da haɗani da wani malami dazan dinga ɗaukar ilimi a hannunsa a ƙasar Italy. Satina biyu a saudia na dawo saboda karatuna. Amma daka ganni kasan bana cikin hayyacina saboda rabani da akai da masoyiyata. Duk na rame na fita hayyacina, amma hakan baisa nayi sakaci da karatuna ba. Na cigaba da neman ilimin addini da zana jarabawar ƙarshe data rage mana na tsahon watanni biyar. Har muka kammala jarabawa banji labarin kaba. Na bincika ance bakaje Nigeria ba. Hankalina ya tashi matuƙa. Amma yaya zanyi. Bayan yin graduation ɗinmu na tattara zan koma gida ƙasata. Amma maimakon nayi 9ja direct saina kasa haƙuri na nufi Saudia wajen Anum. Nayi mamakin tarbar dana samu daga iyayen Anum da ita Anum ɗin kanta daya kasance tazo hutu, dan lokacin karatunta ya dawo nan ƙasar Syria. Albishir na farko da suka faramin shine bani auren Anum, ashe dama sun gwadanine dan suga da gaske nakeson komawa addinin islama kokuwa dan son ƴarsu?. Shiyyasa suka haɗani da malamin dake koyar dani batare da nasan bayanai yake basu ba a kaina. Nayi farin ciki nayi kuka dan daɗi. Sai dai da aka nema na gabatar da iyayena na fito fili na tabbatar musu akwai matsala. Dan nasan kaf danginmu babu wanda zai amshi canjawata matsayin musulmi balle kuma auren musulma kai tsaye. Naji tsoron Anum zata sake kuɓucemin sai gashi ba hakaba. Dan duk da abinda na sanar musu sai gashi sun amince sun bani aurenta. Bayan ɗaurin aurena da Anum an bamu wajen zama kafin ta koma makaranta. Watanmu ɗaya da tarewa ta koma makaranta, ni kuma naje gida Nigeria, sai dai kowa ya tambayeni ina kake sainace kanacan baka ƙarasa naka karatunba sai next year. Na tarar jikin babanmu yayi tsamari, amma sunki kaisa asibiti. Inada kuɗaɗe masu nauyi a accaunt dana samu saboda musilintar da nayi, dan haka nai amfani dasu wajen kaisa babban asibiti aka fara bashi kulawa. Sai dai kash, kwanakinsa huɗu a asibiti ya rasu. Bayan rasuwarsa da kusan sati biyu nace musu zan koma domin yin kasuwanci. Ananne ogan daddy ya bani kuɗaɗen daddy, wai yace a bamu idan munzo, tunda mune manyan ƴaƴansa maza. Na amsa kuɗi na basu wanda zasu wadacesu na koma saudia. Mahaifin Anum shine ya ɗaurani akan harkar kasuwanci acan ƙasar Syria, ya bani shawarar na koma can kusa da matata ina kasuwancina tana karatunta. Naji daɗin wannan shawara kuwa. Tafiyata Syria ta zama tushen nasarata, dan ina zuwa na iske matata na laulayin ciki. Nayi farin ciki matuƙa, harma bansan yaya zan musalta makaba. Haka na zauna kulawa da ita tare da fara kasuwancina. Cikin amincin ALLAH sai gashi dan danan na haɓaka. Saboda na farane da kuɗaɗe masu nauyi. sannan kuma ta hannun babban mutum irin mahaifin Anum. A haka cikin Anum ya shiga watan haihuwa, tana gab da haihuwa na sayi wannan gidan da nake ciki, tare da motar hawa. Sannan na zauna na banbance dukiyar da take matsayin mallakina, na kuma fidda wadda ta kasance ta mahaifinmu. Kwanaki uku da yin haka Anum ta haihu namiji, wanda yaci suna Abdul-malik. bansan yaya zan bayyana maka ɗunbin farin cikinaba ɗan uwana. Amma babu abinda zancema ALLAH sai godiya. A yanzu haka watan Abdul-maleek uku a duniya, muna shirin zuwa Saudia ne domin nunasa ga dangin Anum dan babu wanda ya taɓa ganinsa sai mahaifinta da yazo mana nan sanadin harkar kasuwarsa. Daga Saudia kuma zamu wuce Nigeria na nunata ga dangina, na kuma sanar musu na zama musulmi duk da a tsorace zuciyata take. Dan yanzu haka maganar da nake makama nayi cinikin wani gida a Lagos, idan munje can zamu ɗan zauna kafin hutun Anum na ƙarshen shekara ya ƙare. Waɗanan takardun sune takardun shaidar company na dana mallaka da dukiyata. Insha ALLAHU kuma zan mallakashi ga Abdul-maleek ne. Dan haka kaima inason ka zama shaida, kaimin signing anan wajen, a duk lokacin da yakai shekaru talatin na girma zan mallaka masa shi. Wannan kuma sune takardun dukiyar mahaifinmu, idan nazo Nigeria mu dukanmu zamu haɗu mu saka hannu alamar tabbatarwa da banawa bane ni kaɗai).
“Rungumesa nai a lokacin, na nuna masa tsantsar jin daɗina da wannan ƙoƙari nashi, tare da bashi goyen baya akan zamansa mai sallah. Yaji daɗin yanda na bashi goyon, hakama matarsa. Sai dai ni a cikin zuciyata ƙulla ta yanda zan kwashe waɗanan takardun nakeyi, tare da damfare duk wata dukiya da yake fankamar ya tara. Banbar gidanba sai dare, na tafi da ƙudiri kala-kala a cikin raina da zuciyata”.
“Washe gari ma naje na samesu, shine ya ɗaukeni ya zagaya da ni duk inda companys ɗin suke guda biyu. Na ƙara girgiza da wannan al’amari, dan dukiyace bata wasaba ɗan uwana ya tara. Tofa sai tunanina ya ƙara faɗi da girmama. Dan koda nabar wajensu a ranar kasa barci nayi, har takai na fito na bayyanama abokin tafiyata. Yace na bashi dama zaiyi tunanin ta yanda dukkan wannan dukiya zata zama tawa, amma sai nan da kwana biyu mun gama abinda ya kawomu zai faɗamin hukuncin daya yanke. Naji daɗi, na kumayi murna. Sai dai wayewar garin ranar al’amari ya canja salo, dan bamusan yaya akaiba aka kama wanda muka kawoma kayan cocaine. Har bincike yazo ta kanmu. Da farar safiya mukaji jiniyar motocin ƴan sandan ƙasar. Hankalina ya tashi matuƙa ni da abokin tafiyata, cikin zafin nama muka samu nasarar tserewa ta bayan gidan kafin ƴan sanda su gama shigowa gidan. Muna barin gidan muka rabu nida abokina, domin wannan gudune na ceton rai, kuma hakan abune da kowa ya sani daga tsagera. Idan bala’i ya tunkaro kowa takansa yakeyi. Ba’a sauraren dukiyar da aka tara balle abokantaka. Cikin kiɗima na nufi gidan ɗan uwana, dan duk da wannan bala’i da nake a ciki ban manta da batun takardu ba. Ina isa na samesu a tsakar gida suna hutawarsu cikin kwalliya. Dakewa nai daga ruɗanin da nake ciki na amshi jaririnsu, tare da faɗama matarsa nifa inajin yunwa. Dariyar tsokana suka dinga min, ɗan uwana na faɗin to nazo nayi aure, yafimin wannan gararin, danshi sofa yake na dawonan tare da shi mu haɗa ƙarfi wajen kula da kasuwancinmu. Murmushi kawai nayi, na shiga daga ciki ɗauke da yaron. Matar ta shigo ta bani abinci. Tana kammala haɗamin komai ɗan uwana ya shigo, kallonta yay cike da so da kauna, yace tunda ga bro yazo kizo muje muyi shopping ɗin nan da bamuyiba jiya, sai mubar Maleek tare da shi dan harmu dawo da wahala ya farka. A take ta amince da shawararsa. Yayinda ni kuma kaina ya kawomin wuta a take. Jacket ɗin jikina na cire jin yana faɗin bara ya karo riga a saman kayansa. Nace bro indai rigace ga wanann ka saka nasan zata maka ƙyau, dan yanzun nan dazan fito na ganta a wani shago na siya. Nama tambayi biyu akace babu. Cike dajin daɗi ya amsa, dan shi mutumne mai saukin kai. Sannan bashi da saurin zargi. A gabana matarsa ta taimaka masa ya saka suna dariya da yaba ƙyan da rigar tai masa. Murmushi nayi ina dubansa na ajiye yaronsu na tashi ina gyara masa rigar, cikin dabara na saka masa wayata da wallet ɗina a aljihu, na zare tasa wayar da wallet ni kuma. Sunmin sallama sun wuce bayan sun tambayeni abinda nake buƙata a siyomin nima, dan yace idan ya dawo zamuyi magana akan zamana a gidan. Suna fita na kulle ƙofar falon, na bar yaron anan na shiga cikin ɗakinsu binciken takardu dama duk wani abu mai amfani. Duk kuwa da a raina ina addu’a da fatan tarkon dana ɗana musu ya zama sanadin tafiyarsu har abadan. Komai na gansa, dan haka na tattare tsaf na hada a jikka, na fito falo inda yaron ke barci na ajiye tare da zaman jiran sakamako”.
“Mintuna talatin kuwa ban rufa da zamaba saiga babban labarin da nake jiran gani daga television. Ɗan jaridan dake bada rahoto ne ke magana cikin tsantsar sarƙewar harshe, akan samun nasarar kama mutane biyu da suka shigo daga ƙasar Italy da hodar ibilis. An samu nasarar cafke ɗaya a airport, ɗaya kuma daidai traffic light tare da matarsa. Sai dai bisa kuskuren guduwa da sukayi na gardamar su basusan komaiba ƴan sanda suka harbesu, wanda bisa tsautsayi suka matu har lahira. Sai ga gawar ɗan uwana an nuno tare da matarsa kwance cikin jini. Hannayensu riƙe dana juna. Ga ƴan sanda na lalube wallet din dana saka masa tare da wayata anata faman bincike. Ko ɗar banji a raina na nadamar yin hakanba, dan koba komai asirina ya rufu, zan fara sabuwar rayuwa. A take na ƙarasa haɗa duk wani abu mai muhimmanci dake gidan, tare da kayan yaron na shiga mota na fice a gidan. Na tabbatar yanzu bazan fuskanci kowacce irin matsalaba, musamman daya kasance hankalin jami’an tsaron ya koma gaba daya akan nasarar cafke masu laifi. Aiko banci karo da kowace matsalaba wajen barin ƙasar ta mota. Duk da naci uwar wahala ga yaro nata zubamin kuka ban damuba. Haka nai nasarar fita a ƙasar zuwa ƙasar dake maƙwaftaka da su, acan kuma nabi jirgin ruwa, inda anan ne na haɗu da Chioma, itama tsagerace ta kanta, dan kuwa kusan duk irin harkokina shi takeyi, sai dai ita oganta a Nigeria take. A dai takaice na samu nasarar komawa Italy tare da jariri da ɗunbin dukiya da takardun kaddarori da taimakon Chioma. Ogana yayi farin cikin ganina dajin labarin ta hanyar dana kuɓuta, dan haka yaymin alƙawarin taimakona ta hanyar tabbatar duk waɗannan kaddarori na ɗan uwana a tafin hannuna. Yanda Chioma ke taimakona da rainon jariri dana canjama suna da John ne yay sanadin ƙulluwar soyayya mai ƙarfi a tsakaninmu har mukaima juna alƙawarin aure. Ta matsa matuƙa muyi aure sannan mu koma 9ja dan haka na amince mata saboda nima ina sonta. Bayan aurenmu muka nufi ƙasar haihuwarmu cikin danginmu. Wanda zuwa yanzu labari ya gama zuwa kunnen danginmu na rasu ta hanyar kamani ina safarar hodar ibilis ni da wata, dan a haka labarin keta yawo. Kowa kuma yana ɗauka ni aka kashe, saboda kowa yasan halina. ni kuma nine ɗan uwana. Munzo Nigeria ne dama da shirin hutu mai dogon zango, dan ogana ya tabbatarmin dolene inyi nesa da shiga kowacce ƙasa. Inba hakaba kuwa babu makawa sai an bankaɗo ainahin gaskiyar nine mai laifi ba ɗan uwanaba. Nayi amfani da wannan shawara kuwa, dan haka na yada zango a Lagos gidan da ya sanarmin ya saya ta hanyar abokinsa. A labarin nanfa da nake baku kowa ya ɗauka dama nine aka kashe, dan ansan nine tsagera, ɗan uwana kuma shine ni. Dan haka na canja sosai wajen ɗaukar ƙyawawan halayyar ɗan uwana na yafama kaina akan dole. halena kuma na ɓoyesu, dagani sai matata muka sansu. Ban wani cika burin ɗan uwana ba na mallakama mamana da ƙannenmu dukiya ba, sai dai naja ƴan uwan nawa a jiki wajen sakasu cikin harƙallolina. Bansan yaya akai Godwin ya fahimci banine twin bro ɗina ba, sai kawai rana tsaka ya fuskanceni da wannan zance shi da Mike. Na matuƙar tsorata da firgita, amma sai Chioma ta bani dabarun maidasu a hankalinsu ta hanyar ƙara jansu jikina da rufe bakunansu da dukiya mai tsoka da kuɗaɗenta. Danni a lokacin bawani kudine da niba. Sunko bi sun tsuke bakunansu kuma, tun daga nan suka zama sunsan kowacce irin harƙallata, sun kuma san John ba ɗana baneba”.
“Abinda ya faru baisa na daina harƙallataba, sai harkokine suka sake buɗewa sabbi dan yanzun dukiyar Chioma muke juyawa, nazama jan wuya anan Nigeria, ta hanyar turomin da kaya da ogana yakeyi. Cikin shekara huɗu kacal na shahara, na kuma sakeyin kutse cikin addini har saida na zama Pastor a wata ƙaramar church duk da babu wani ilimi da nake da shi. Zuwa lokacin John ya fara wayo, yanada shekara huɗu, dan ko ina zuwa yake, ga surutu a bakinsa ba’a magana. Yanda yaron ya shiga ranmu muke tarairayarsa bazaka taɓa kawowa a ranka ba dɗanmu bane, dan soyayya ta gaske Chioma ke nuna masa. hakan yasa na ƙara sonta a raina, dukda kaf dangina basa sonta dan ta rainasu, su kuma gani suke ta ƙwaceni ta hanani taimaka musu bayan kuma dukiyarsuce tunda dai kallona suke a matsayin twin bro ɗina. Dukiyar ɗan uwana tazo hannuna, sai dai ba dukantaba, dan wata an tabbatar da dolene sai John ya girma sannan nasoba kuwa dole na haƙura, na cigaba da juya abinda ke hannuna ta hanyar harƙalla daban-daban. A wannan lokacin ne naje ƙasar France yin wani couse na watanni tara, dan rashin yawan ilimi nason min tangarɗa akan zamana pastor. inda acanne muka haɗu da Sooraj Hashim Jibiya. Bayan korarsa da akai a makaranta sanadin dukan da yaymin nai jiyya kusan ta watanni uku, da ƙyarma na kammala abinda ya kaini na dawo gida cike da alwashi kala-kala akan Sooraj dama yankin daya fito gaba ɗaya. Dan nayi alƙawarin sanadin abinda ya aikata mani saina tarwatsa duk danginsa da jama’ar yankinsa. Wannan shine dalilin farkon fara sato yara daga yankinsu ana kawomin ina cinikinsu. Sai dai na gaza lalubo a ina Sooraj yake? Dan ko’a wancan karon dama bansan taka-maimai shi ɗan ina bane, nadai san musilmine ɗan arewa. a zahiri kuma na lulluɓe True color dina da rigar addini, babu mai cewa ni shege ne. Cikin kanƙanin lokaci na shahara, dukiya da girma suka zauna saina tattaro na dawo Abuja. Wani halaye da John ya fara nuna mana na ƙyamar addini da wasu abubuwan namu duk da ƙanƙantar shekarunsa yasa hankalina tashi. Dan da alama yaron yanada wata baiwa dake nuna ya fahimci kamar muɗin ba iyayensa bane. Mike ne ya bani shawarar zuwa gidan boka a kulle tunanin Yoohan gaba ɗaya, koda ya girma bazai taɓa kawo a ransa muɗin ba iyayensa bane koda yaga rashin kamansa da Chioma. Naji daɗin wannan shawara, nakumayi amfani da ita. Bayan munje wajen boka ya amsa zai mana aiki, sai dai aikin zai zama sanadin saka ciwon rashin barci ga John lokaci-lokaci. A take kuwa muka amince, akai asiri John ya koma tafin hannunmu sosai. Duk abinda muka sakashi babu tantama yake mana, sai dai ban taɓa yarda yasan ɓoyayyar harƙallataba Mamana ma da sauran ƴan uwana nasa akai musu asirin da bazasu taɓa tunanin ko kawowa a ransu niɗin ba ɗan uwana bane. Ana haka Chioma ta haihu twins itama, Gebrail da Joy. Nayi farin ciki sosai da samuwar nawa ƴaƴan, amma samun nawa baisa naji tsanar Yoohan ba. Bayan su Joy Chioma bata sake yarda ta haihuba sai da John ya shiga jami’a ta sake haihuwar Victoria. Ta sake Abraham wanda cikinsa yazo mata babu shirin hakan, dan tace daga yaƴa uku ta gama. To ashe da rabon zuwan Abraham. Abinda yasa nasaka Solomon kullum yake tare da John tun bayan gama karatunsa, saboda tsoron kar wajen yawon ƙasashensa da aiki ya tilasta masa yin gamo da wani dangin mahaifiyarsa ƙwaɓata tayi ruwa. Shiyyasa dukkan motsinsa sai na sani ta hanyar Solomon”.
“Abu mafi ɗagamin hankali daya faru shine tarayyarsa da Sheikh Sooraj. Lokacin dana san wannan alaƙa hankalina yayi ƙololuwar tashi, na kumayi murna dan sanadin John maƙiyina dana ɗauki shekaru ina bulayin nema ya bayyana. har ƙauye naje mukai zaman meeting da sauran mutanena, dan saboda gudun irin haka yasa na cusa masa ƙiyayyarsu tun yana yaro, amma daga ƙarshe sai gashi abinda nake gudun ya auku. John ya xama musulmi kamar mahaifinsa. Ranar nayi tamkar mahaukaciya a gidan nan, harma na yanke hukuncin kashesa kawai na huta bayan na sakashi ya sakamin hannu a takardun da naketa a jiya tsahon shekaru, dan company ɗin yanata haɓaka zuwa yanzun, sai dai ina mamakin ta hanyar wa hakan ke faruwa?. Su Mike ne suka haɗu wajen bani shawarar mizaisa na damu da musilincinsa. Sun san dai babu ta yanda za’ai ya iya gano shiɗin wanene saboda asirin da ke a kansa. Sooraj kuwa amfani zamuyi da kusancinsa da John ɗin mu yashe masa asusunsa tsaf mubarsa da ɗimautar ƙwaƙwalwa da bugawar zuciya. Amma wai koda na tuntuɓi John akan mike alaƙarsu sai ya nunamin wani aiki yakeyi akan Sooraj ɗin. Nafa yarda da shi har cikin raina. Saboda nasan irin horon danai masa tun yana yaro akan wannan yanki. Har raina daɗi nakeji zai ɗaukamin fansa akan abinda Sooraj yaymin tsahon shekaru, dan duk da korar da akai masa a makaranta wancan karon baisa na huceba, na kuma daɗe ina addu’ar haɗuwarmu amma hakan bai yuwuba sai yanzun. Ban fahimci John folani yake a kwalayeba sai akan aurensa da ɗiyar Sooraj, idan nace zan bayyana muku halin dana shiga ni da matata dasu Mike a wannan tsakanin ɓata lokacine, da ƙyar Godwin ya kwantar min da hankali akan na amince da auren, bayan anyi mu kashe yarinyar yanda Sooraj zaiji ciwo sosai a ransa kafin kuma mu yashe masa asusunsa. Wannan shawarace ta kwantarmin da hankali na amince akai aure batare dana yarda na nunama Yoohan nasan ya musulintaba, sanann matata ma ban taɓa faɗa mata ya zama mai salla ba dan nasan tana son John sosai fiyema da ƴaƴanta, kodan shita fara samu matsayin ɗa ne kafin ta haifi nata oho. Shigowar ɗiyar Sooraj cikinmu ta sake ruguza komai na shirinmu, dan yarinyace hatsabibiya. takai ko ganinta nai sai naji matsanancin tsoro na shigata. Bala’in kwarjini takemin kamar ubanta, gata bata da tsoro. Ban sake tabbatar da yarinyarnan abar tsoro bace sai randa ta shigar min ɗaki, ta kuma nuna ba ita bace. Da gaske nima ɗin na yarda ba ita ɗin bace a lokacin, sai daga baya na gane itace ta hanyar cctv dake a falona wadda ko matata batasan da zamanta ba duk da kuwa harƙalla ɗaya mukeyi, kai hasalima na sakatane domin ita dan haka harkarmu take a kullum bama yarda da juna. Bawai ina tunanin itama zata cutar dani bane, dan ina tsananin ƙaunarta, na kuma yarda da ita. Ina tsoron kar dai cikin abokan harƙalla wani yay amfani da ita ya cutar dani ne dai. Sosai hankalina ya tashi da lamarin yarinyar, da kuma tunanin mahaifintane ya turota leƙen asirina. Sai kawai na shirya yanda Doctor ɗin da zasu mata aiki zasu kashe min ita ta cikin sauƙi kafin na dawo kan John ɗin shima. Naji daɗin abinda Gebrail yay mata, dan nasan nesa tazo kusa akan aiwatar da aikina a kanta, sai dai kash Dr Mateo ya lalatamin burina. Naji takaici, naji ciwo, na kuma yanke shawarar halaka John da yarinyar gaba ɗaya da zarar sun dawo ƙasar nan. Zan fara halakata ita da duka danginsu da ubanta kafin shi ma na juyo kansa. Amma taurin kai irin na John da bani da tantama wajen ubansa ya gada sai ya sake ruguzamin shirina. Ya koro Solomon, ya kuma ɗauketa daga Austria ya canja mata ƙasar da bani da damar shiga, dan tuni aka hanani lasisin shiga ƙasar U.S. Wamnan shine dalilin yimin katanga a garesu, na zauna dakon jiran dawowarsu ko zuwansu ƙasar a tare. A randa John ya dakarmin yaro wai ya shigar masa ɗaki naji kamar shima na halakashi da hannuna. Amma na taushi zuciyata dan nasan a tafin hannuna yake. Shina ƙanƙanin lokacine ya rage masa ai. Na tattara komai na ajiyeshine ban masa magana a kaiba dan banason ya zargi komai a kaina har sai randa ya sakamin hannu a waɗannan takardun, ya kuma kawomin shegiyar matarsa ƙasarnan. Dan nagama shiryawa tsaf akan yanda zan yashe asusun ubanta kaf na maidashi sifili. Wai kawai kwatsam rana tsaka saiga yarannan da ciki sunzomin gida. Lallai naga baƙar rana kuwa, dan da gaske ranar susucewa nasoyi gaba ɗaya. Randa na gama shirya ƙudirin aikata lahira suka baro Abuja batare da ko John ya sanar minba da yake shima tantirin ƙwallon shege ne. Nasa a biyota kanon, a daren da zasuzo bisa jagorancin Solomon kuma ƴan sanda suka ritsamin yaro a hanyarsa ta kawomin kaya daga ƙasar Cameroon. Da ƙyar yasha zuwa abuja, duk sun fasa masa jiki da bullets, amma sai yayi ƙoƙarin zuwa ya isarmin da saƙon na gudu, dan da gaske wanann tarkone babba aka ƙulla a kaina tsahon lokaci. wannan shine sanadin tserema ƴan sanda da nayi, sai da na bada ƙafa ta watanni biyu na dawo da baya saboda jin matar John ta haihu ta hanyar wani ɗan leƙen asirina. Na fahimci lokaci yayi da zai sakamin hannu a takardu, daga haka na kama gabana bayan na kasheaa shi da ɗan da matar tasa. Sooraj kuwa zan dawo masa da nasa shirin bayan ƙura ta kuma kwanciya…….”
Kallonsa kawai kowa keyi a falon kamar sun sami television. Dan shi kansa Jay makircin na Goshpower ya matuƙar rikitashi. Ashe shine sanadin halakar ƙanwarsa da mijinta. Iya bincike sunyi bayan faruwan wancan al’amarin amma suka gagara sanin gaskiya, dan sudai basusan mijin Anum da wani twin Brother ba. Ba komai yaja hakaba sai sakacin rashin bincike danginsa koda a ɓoyene, duk da dai shi yaso yayi binciken a lokacin mahaifin Anum ɗin yace a barsa darajar gaskiyar yaron, a bashi dama har ya bayyana mana danginsa suma ya bayyana musu mu. Tunda dai shi sun gwadashi ta hanyoyi da dama basu samesa da wani mummunan hali ba. A lokacin haushi shi Jay yaji yace ya cire hannunsa akan batun, dan ya rasa wane irin so sukema mijin Anum ɗin. Ganin yanda ya dage da harkar nema da neman ilimin addini yasa shima Jay din ɗaga masa ƙafa ya bashi lokaci zuwa sanda Anum zata haihu, dan yayi alƙawarin da zarar ta haihu kosu Ummu sun yarda ko basu yardaba dolene yasan dangin mijin Anum ta hanyar tasa ƙeyarsu har Nigeria aje tare da shi. Sai gashi a dai-dai gaɓar da take shirin kawo musu ribar auren nata su gani su kuma je ga dangin mijin nata wannan al’amari ya bayyana. Wanda ta sanadin haka suka rasa ƴar uwarsu da mijinta da ɗanta. Suka kuma rasa ainahin gaskiyar zance akan zargin da akema mijin nata. Haka suka haƙura badan zukatansu sunsoba, suka ɗauka wannan itace ƙaddararta kuma. Tare da mahaifinta sukaje suka amshi gawarsu wajen ƴan sanda bayan ansha gwagwamaya suka sallacesu aka kaisu makwancinsu. Sai dai basuga gawar yaronba, sai suka ɗauka wani ya ɗauke gawar a cikin wannan rubibi. Sai dai a binda ya ɗaure musu kai rasa muhimman takardun mijin Anum a gidansa. Bayan wasu watanni kuma akazo musu da batun an ƙwace duka kaddarorin nasa dake a ƙasar ta Syria. Basu da ikon nuna rashin yarda tunda sunsan hakan shine dokar ƙasar ga duk wanda aka kama da irin wannan laifin. Badan zukatansu sunso ba daga haka suka rufe babin Anum da duk abinda ya shafeta. Sai kuma gashi kwatsam bayan tsahon shekaru sunci karo da mai tsananin kamanni da ita a Nigeria, tare kuma da mai tsananin kamanni da mijinta matsayin ubansa. Wannan abu ya rikita Jay matuƙa, harma yaji a aransa inama Ummu da mahaifin Anum na raye su tayasa wannan al’ajabi…..
Ta ɓasan da Jabeer yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa daga tunanin daya tafi, Jabeer ya nuna masa agogo da faɗin, “Boss asuba fa na gab da shiga, muyi abinda ya dace kafin masu ƙarfin faɗa aji suce wani abu”………….