SARAN BOYE 77

No. 77

…………Kai Jay ya jinjina masa zuciyarsa a matuƙar raunane ya dubi Yoohan da kansa ke a duƙe yana hawaye. Nu’aymah kanta kuka take hakama Umar. Cikin ɗacin murya da soyewar zuciya Jay yace, “Goshpower nama rasa abin faɗa a gareka. Dan kaine mutum na biyu da bazan taɓa yafemawa ba da mantawa da shi, bayan gagarumin

zalincin da akaima rayuwata da barmin tabo a shekarun baya. Ka cika azzalumi na gasken gaske. Ni nan da kake ganina nine yayan wannan mata ta ɗan uwanka Anum. Mune mukaje har Italy muka taho da ita, tabbas inaji a raina UBANGIJI ya lulluɓe idanunmu daga garekane saboda wannan shine rubutacciyar ƙaddarar Yoohan, wannan wata hikimace daga hikimomin UBANGIJI, ya kuma fimu sanin dalilin yin hakan, kamar yanda ban isa goge abinda aka zana daga zuciya ba, haka ma ban isa canja abinda ya zama rubutacciyar ƙaddara ba domin ALLAH shine kaɗai masanin gaibu, sai yaso mu sani, sai yaso mu gani, sai yaso muji”.

       A kallo ɗaya zaka fahimci a tsananin firgice Papa yake, dan jikinsa har ɓari yake ya dubi Jay, bakinsa ma rawa yake amma ya kasa cewa komai. Hakama Yoohan da Nu’aymah wani irin kallo mai firgitarwa sukema Jay ɗin. Ya furzar da huci mai azabar zafi da ɗauke kansa. Dan ji yake kamar yay fata fata da goshpower kawai kozai samu sassauci a ransa. Lallai yanaji a ransa idan ya cigaba da zama a gidan nan babu abinda zai hanashi huhhuda jikin Goshpower da bullets, dan haka ya miƙe da sauri ya fice hawaye na ziraro masa a saman kumatu. Komai dawo masa yake sabo a rai da zuciya. Gawar Anum da mijinta ne ke dawo masa cikin ido tamkar yanzu komai ya faru. Zafi da raɗɗi da ruɗanin da suka shiga da mutincin mahaifin Anum da ya taɓu a idon danginsa da al’umarsa a wancan karon na dawo masa a zuciya. Aƙidar larabawa ce wannan gudun zubewar mutuncin dangi. Idan kuwa aka samu kuskure wani abu ya auku na zubewar mutunci ga ɗayanku sai ya shafi kusan duk zuri’arku. To hakance ta faru ga zuri’ar Anum, dan sanadin wannan al’amarin mahaifinta yabar duniya, ƴan uwanta kuwa sai da suka bar ƙasar saudia. Tsakanin rasuwar Abban Anum da Ummu kuwa baifi watanni bakwai ba. Kuma hakan nada alaƙa itama da kasa goguwar tabon da aka ringa jifan Anum da mijinta da shi na safarar ƙwayoyi. Duk da su sunsan ba haka baneba, amma tayaya zasu fahimtarma duniya ba haka ɗin bane?. wannan ciwon shine ya tarwatsasu zaman cikin saudiya ya gagaresu duk da kasancewarsu manyan mutane.

       A hankali Yoohan ya miƙe yabi bayan Jay kansa na juya masa, da ƙyar yake iya ganin wajen taka ƙafarsa. Jay na tsaye jikin mota ya kifa kansa kawai yana hawaye yaji an rungumesa ta baya. Kamar dama wannan damar Yoohan ya ke jira sai kawai ya fashe da kuka. Duk mai imani ya gansu a wannan yanayin sai yaji rauni ya ƙara riskarsa. Juyowa Jawaad yayi ya rungume Yoohan ɗin, hakanne ya sakashi sake fashewa da sabon kuka dan yama manta shi namijine a yau. 

     Jay dake murmushi yana bubbuga bayansa yasa hannu ya ɗauke nasa sabbin hawayen da suke sake zubowa yana kallon su Aliyu dake fitowa da Goshpower da yaransa daga cikin gidan. Basu Jabeer ba, hatta da papa kansa sai da zuciyarsa tai masa nauyi. Sai da aka gama tasa ƙeyarsu cikin motocin sannan Aliyu yazo inda Jay da Yoohan suke. Cikin lallashi yayma abokin nasu kuma ɗan uwan nasu magana akan ya kamata su wuce lokaci na tafiya.

       Kai kawai Jay ya jinjina masa. Sannan ya ɗago Yoohan daga jikinsa, hannu yasa yana share masa hawayen daketa zuba babu ƙaƙƙautawa. Ya ɗanyi murmushi da faɗin, “Yarona bazai kasance rago mai kuka a gaban matarsa da jikana ba ai na sani”. Murmushi ya suɓucema Yoohan da sabbin hawaye a lokaci ɗaya, sai yay saurin sake faɗawa jikin Jay ɗin kuma.

          Suma su Naser dake sharar hawaye duk ƴar dariya sukayi saboda yanda Yoohan ɗin yayi. Jay ya yafito Nu’aymah dake goye da Deen tana ta faman kuka itama. “Zo nan my daughter ki lallashi mijin nan naki naga da gaske ɗan shagwaɓa ne”. Ƙarasowa Nu’aymah tayi tana murmushi da hawaye. Jay ya sake ɗago Yoohan yana faɗin, “Kai dama ashe likitoci ragwagene ban saniba ni Muhammadu?”.

        Cikin dariyar ƙarfin hali Jabeer yace, “Boss da alama kam, dan gashi Son ya tabbatar mana”. Duk sukai ƴar dariyar ƙarfin hali data rage musu nauyin zukata. Daga haka suka shiga motoci, dan an bincike gidan babu komai a cikinsa. Sabone ma da alama suma su papan jiya suka shigesa. Su Yoohan mota ɗaya suka shiga da Jay. Umar yaja motar, Jay na gefensa, Nu’aymah da Yoohan a baya. Su Abdallah kuma suka koma a motar da sukazo suma. Waya Jay ya ɗauka ya turama Baba malam text message dan hankalinsu ya kwanta, kafin ya juyo ya kalli su Yoohan dake taimakama Nu’aymah ta sakko da Deen daya sake farkawa daga barci.

     “Abuja zan wuce da ku, zanyi magana da malam insha ALLAH”.

     Sun amsa masa da girmamawa, dan shi kansa Yoohan baya buƙatar yin nesa da Uncle ɗin nasa sam.

      Su Abdallah sun wuce gida kamar yanda Jay ya basu umarni, su kuma suka wuce airport domin komawa abuja, fatansu suyi sallar asubahi acan insha ALLAHU.

_____★

        Idan nace muku wani babba mai hankali a gidan su Nu’aymah ya rintsa  a wannan dare nayi ƙarya. Kamar yanda su Ahmad suka kwana zaune tare dasu Papa haka suma su baba malam suka kwana zaune cike da tashin hankali. Duk da ma Abdallah yayi ƙoƙarin kiran wani a gidan ya sanar masa anga su Yoohan ɗin amma network yayta basa wahala. Dole ya haƙura kawai musamman da labarin da papa ke basu ya ɗauke masa hankali da tunani.

          Motar su na shiga cikin gidan duk su baba malam suka firfito da yakema asuba tayi. Ganin babu su Aymah tare da su ya saka jikinsu ƙarayin sanyi kuma. Sai dai kuma Murmushin kwantar da hankali da Naseer yayi ya saka zuciyarsu samun sassaucin bugawar da takeyi. Su Abdallah suka ƙarasa garesu jikkunansu duk a sanyaye, dan gaskiya ba ƙaramin tausayin Yoohan zukatansu suke a ciki ba.

       Kafinma wani a cikin su baba malam yay magana malam ƙarami yace, “Abba ku kwantar da hankulanku duk an gansu, sai dai sun wuce abuja yanzu haka tare da Uncle Jay, harma da masu laifin”.

   Kusan a tare suka shiga sauke ajiyar zukata, dan baba malam baiga text message ɗin Jawaad ɗinba dama. Jin haka yasa baba malam cewa, “Alhamdulillahi ala’kullihalin, inaga sai muje kowa yay haramar salla dan lokaci yayi”.

      Ina idar da salla kuwa kowa dole ya nema gado ramuwar barcin daya gagaresu. Musamman ma Umm da jininta ya hau ita da Hajjo.

★★★

        Ƴan Abuja ma dai suna sauka wucewa akai da su Papa station, madam Chioma natama mutane kukan iskanci wai Yoohan ya taimaketa kar sonshi ya kasheta. Wannan kalma ta daki zuciyar papa. Ya bita da kallon tsoro da firgici sai dai babu bakin magana dan shi koma tafiya baya iyayi saboda duka ƙafafun sunsha harbi.

       Ganin yanda Deen ke numfashi da ƙyarne yasa Yoohan bayan sunje gida sun sauke Nu’aymah su kuma suka koma massallaci. Suna idar da salla yace zaije ya samowa Deen magani dan an ɗibar masa sanyi. Jikin yaronma zazzaɓine.

1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button