SARAN BOYE 77

      Nu’aymah na shiga Miemaa ta fito ta shiga da ita ciki dan Jay ya kirata dama. Ganin yanda Deen keta kuka yasa ta amshesa ranta duk a jagule da ɗaukar alhakin yaron da akayi. Bata wani zauna jan zance ba tai ciki da shi, tare da cewa itama Nu’aymah ta biyota tazo tai wanka dan duk a galabaice take. Ruwa mai zafi ta haɗa mata, shima Deen tai masa wankan da ruwa mai ɗumi sosai. ta kuma gasa masa jikin da towel dan tasan mugayen can ba ɗaukar tausayi zasuma yaron ba. Aiko anayi yana uban kuka. ana kammalawa tunkan ta tsamesa a ruwan har yayi barci. Tausayin yaron ya kuma kamata. Goyashi tayi domin yin salla. bayan an idar ta nufi ɗakinta da Nu’aymah ke can. Har tayi wanka tama shirya cikin doguwar rigar data bata. kasancewar ba salla zatai ba tana zaune tana matsa ƙafarta da tun ciwon dataita mata da cikin Deen har yanzu data haihu bata gama saki da ƙyau ba. “Yauwa ɗiyata kin idar?”.

       Kan Aymah a ƙasa tace, “Eh Miemaa ina kwana?”.

    “Lafiya lau, ya gajiyar gwagwarmaya?”.

     Murmushi Nu’aymah tayi dan kuwa da gaske jiya sunsha gwagwarmaya mai wahalar mancewa a tarihin rayuwa. Miemaa ta bata Deen daketa ajiyar zuciya yana barci. “Kinga bashi abinci, kema bara na haɗo miki ko tea ne kisha ku kwanta ku huta”.

    Babu musu Aymah ta amshesa. Miemaa kuma ta fita haɗo mata tea. Yanda Deen ke amsar abincinsa har tausayi ya bata. Dan ita dai acan bawani samun nutsuwar ƙwarai tayi wajan basa ɗinba. Ta shafa kansa tare da kissing goshinsa, daga shi har mahaifin nasa ɗunbin tausayinsu da ƙaunarsu ya mamaye mata zuciya. Babu jimawa itama Miemaa ta kawo mata tea da bread da soyayyan ƙwai. Amsarsa tayi da cewa. “Zauna kema ki karya, bara naje da shi babansa zai dubasa, idan kin kammala ki kwanta kema ki huta”.

       Godiya Aymah tai mata. Miemaa kuma ta fita.

       A falo Yoohan ya amshi Deen ya dubashi da bashi maganin daya siyo sannan Miemaa ta sake amsarsa ta goya. Sashen Awwab da baya ƙasar yana Spain aka kaisu. Jay yace suyi wanka su sha tea ga shi nan da Miemaa ta haɗa musu suyi barcin gajiya. Sun masa godiya. Su dukansu barcine a idonsu, hakan yasa basu wani zauna zaman maida yanda akayi ba. Dan Yoohan ma sai da yasha magani saboda ciwon kai. da taimakon maganinne ya samu barci mai nauyi yay gaba da shi.

__________★

         Su Aymah sunsha barci sosai. Bayan tashinsu duk suka sakeyin wanka. Zuwa lokacin gida ya cika da su Little bee. Sunsha kuka labarin da Jay ya basu game da ainahin gaskiyar rasuwar Gwaggosu Anum da mijinta. Da kuma tabbatar Yoohan ɗan uwansu. Lamarin ya taɓa musu zukata sosai duk da bama sanin Anum ɗin sukai ba su. Sanda ta rasu Little kaɗai aka haifa, bakuma wanda ya taɓa faɗa musu gaskiyar magana akan rasuwar tata sai yau. Deen yana hannunsu kowa ji yake da shi, hakama da su Yoohan suka tashi sai murnar kowa ta ƙaru. Anuwar ya rungumesa yana kuka. Shima Yoohan ɗin sai da ya koka. Ransa kuwa cike yake da ɗumbin farin cikin tsintar kansa a cikin dangin mahaifiyarsa. Ya ɗauki komai matsayin ƙaddara kamar yanda Uncle Jay ya faɗa.

    Sunci sunsha tare, kafin su zauna kuma aka gabatar da juna. Sannan aka tsaida ranar da zasuje Oman wajen sauran dangin Anum da ke can a yanzu suna rayuwa. Anan kuma Nigeria za’a zagaya dasu cikin danginsu suma insha ALLAH.

       Kiran Jay da aketayine ya sakashi fita dole. Dan yau daga shi har Miemaa da little basu fita aiki ba. Duk da kuwa gari ya ɗauki ɗumi akan kama Papa da yaransa da akayi. Musamman daya kasance an saki video ɗin labarin da papa ya bayar akan saka twin Brother ɗinsa a tarko domin shi ya kuɓutar da kansa. Wannan al’amari ya girgiza zukatan jama’a sosai. Masana nata sharhi akan hukunci daya dace ace ya fuskanta. Wasuma gani suke a kashesan kawai shine babbar mafita ga ƙasar gaba ɗaya. Dan barinsa koda a prison ne wataran wani zai iya fiddosa a ɓoye tunda ƙasar tamu sai a hankali. Hakama jama’ar gari ba’a barsu a bayaba wajen maida yanda akayi dayin sharhi akan wannan al’amari.

      Lokacin da labarin ya isa gidan su Aymah har cikin kunnen Mama debora sai ta yanke jiki da faɗi. Dan su su Abdallah ne sukai zaman faɗa musu yanda komai ya faru ma. Kwasarta akai zuwa asibiti a rikice, su Victoria nata faman kuka dan suna ƙaunar kakar tasu. Musamman daya kasance yau sun wayi gari da wannan tashin hankali na halayen iyayensu da ya ƙara fitowa duniya taji. Basu da kamarta a yanzu, dan sun tabbatar ko ƙauyensu kam yanzu sai ya gagaresu zuwa, dan maimakon tarba da zasu samu daga jama’ar garin kamar da, yanzu idan sunje duka zasuci. 

    Ganin ta farfaɗo baba malam ya hana a faɗama Yoohan. Yace a barsa shima ya hutama ransa, idan ta warware zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sai suma a maidasu Abuja ɗin.

      Su Nu’aymah basu san hidimar da akeba. suna nan cikin zuri’ar data kasance ta Yoohan hankalinsu kwance, kowa zallar ƙauna da kulawa yake ƙoƙarin nuna musu. Tare da bama Yoohan labarin dangi kala-kala dana mahaifiyarsa, tare da hotunanta. Ranar dai haka suka kasance cikin ɗumbin farin ciki, dan ma fitar Uncle Jay ta rage armashin hirar.

    A ɓangaren Jay kuwa ashe kirane na sirri ya samu daga manyan ƙasa. Inda sukai zaman tattaunawa dangane da shari’ar papa. Sun yanke shawarar a miƙasa hannun ƙuliya manta sabo da wuri. Wasuko sunce ai masa allurar poison tun kafin shiga kotun, dan suna tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo musamman da Goshpower ya kasace yaron manyan shegun duniya ne. Babu hanyar da bazasu iya biba domin ganin sun kuɓutar dashi. Barin irin su papa a duniya kam ai tashin hankaline. Dan babu makawa a yini guda suna iya tada jama’ar ƙasa da ƙasar baki ɗayanta. 

        Shi dai Jay bai yarda ya tofa wata maganaba, dan suma ɗin ai baisan yaya nasu zukatan sukeba, balle ayyukansu na ƙarƙashin ƙasa. Sannan baima saniba ko suma ɗin wani abu sukesan binnewa ta wannan hanyar tunda kowa yasan yanda papa ke mu’amula da manyan mutanen ƙasar ai. Sai da duk suka gama surutansu yace shidai a nashi shawaran kawai su bari a miƙasa kotun, yanke hukunci aikin alƙaline ba nashi shi jami’in tsaroba. Idan kaga mai laifi ya rasa ransa a hannun jami’in tsaro sai dai akan kuskure ko kare kansa ga mai laifi idan yanada makami. Amma haka ɓakatatan basu da damar yima goshpower allurar poison. Duk da wasu sun nuna jin haushinsa shidai bai damuba. Yay musu sallama ya wuce office. Gudun zuwan abinda zaije ya dawo ya sakashi tattara duk wasu bayanai dake a hannunsa a yammacin ranar ya tura ƙara kotu sannan ya koma gida.

      Miemaa kaɗai ya sanarma halin da ake ciki, amma su Yoohan baice musu komaiba, saima sakawa yay aka kawo masa Deen da bai gajiya da barci saboda kasancewarsa jariri har yanzu. Kwata-kwata yau kwanansa tara kenan ma a duniyar. Amma ya fara cin karo da gwagwarmayar cikinta.

     Kasancewar Aymah jego take yasa Miemaa tsayuwar daka a kanta ta ƙarasa jegon anan, dan summa gama magana dasu baba malam idan su mama debora zasu wuto Abuja gobe idan ALLAH ya kaimu zasu taho mata da kayanta dana Deen kawai. Koba komai hankalin Nu’aymah yaɗan nutsu waje ɗaya yanzu, hakan yasata ƙagara ma a kawo mata kayanta ta koma sauraren lectures kota online ɗinne kafin suga abinda ALLAH zaiyi akan maganar komawarsu. Danshi kansa Yoohan harma ya ɗauki hutun ƙarshen shekara mai nisan zango sosai.

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button