SARAN BOYE 77

Washe gari su Jay suka tattare al’amarin papa suka miƙa kotu, yayinda dangi keta tururuwar zuwa gidan Jay ganin Yoohan. Dan su Afrah duk sun baza labari ta waya. Khairiyya kanta da ba’a garin take aure ba sai gata a wannan ranar ganin yayansu. Duk da dai bama wani girmanta yayi sosaiba, amma dai little ta girmesa. shiyyasa abu kaɗan ke sakasu fara faɗa. Shi son girma ita son girma. Daya motsa tace shiɗinfa ƙanintane. Shi kuma yace ALLAH ya kiyaye ya zama ƙaninta. Abun nasu na bama kowa dariya. Musamman ma Nu’aymah.
*_WASHE GARI_*
Washe gari su Mama debora da taji sauƙi duk da bata koma garau ba suka iso abuja saboda suna son halartar zaman kotu da za’ayi. Ba kowa ya matsa hakanba kuwa sai mama debora. Dan tasha kuka, acewarta tanason taga idon papa ko zaiji kunyar yaudarar da yay mata na saka ɗanta mutumin kirki a tarkon da aka kashesa.
Da yake tafiyar mota sukayo, kuma sun taho da wuri sai gasu kusan sha biyu sun shigo garin Abuja. Yoohan na tsakkiyar dangi da keta cigaba da zuwa kiran Gebrail ya shugo wayarsa. Ɗagawa yay ya koma gefe. Cikin girmamawa Gebrail ya gaidashi da faɗa masa gasu sun shigo Abuja. Zasu wuce can gidanne kokuwa suzo nan gidan Uncle Jay ɗin su samesa?.
Yoohan yay ɗan jimmm kafin ya furzar da numfashi, yace, “Okay, inaga ku wuce can, nima gani nan zuwa gidan”.
Da girmamawa Gebrail ya amsa masa da to. Yana yanke wayar ya sami Uncle Anuwar da maganar, dan Uncle Jay baya nan ya fita saboda sunata kai kawo akan lamarin papa da yaransa su Solomon.
Uncle Anuwar yace, “Yahya ai daka barsu sun wuto nanɗin kawai, dan an riga da an zama ɗaya yanzu. A gidan nan kuwa munada isassun masauki insha ALLAH. Sanann kusancin zama da zamu samu dasu yanzu zaisa suma idan sunada rabo sai kaga sun karɓa musulinci”.
Cikin ɗan sosa wuya da jin daɗin wannan fata Yoohan yay murmushi idonsa nakan Nu’aymah da suke hira dasu Afrah acan gefensu. Yasan komi rayuwarsa ta zama a yanzu itace sila, dan haɗuwa da ita shine ya zama hasken da ya haska masa hanyar da yake taka ƙafa, iska yaɗan furzan da faɗin, “Okay Uncle bara naje zuwa anjima ai sai nazo dasu ɗin, kagama sannan Uncle Jay ya dawo”.
Kamar yanda Yoohan ya faɗa bayan sallar azhur ya nufi gidansu. Duk an janye ƴan sandan da suke zagaye da gidan, ko maigadi yanzuma babu balle waɗannan guards da ke cike da gidansu a da. Rayuwa kenan, ka shuka alkairi sai ka girbe abinka. Horn yayi kusan sau uku sannan Gebrail yazo da ɗan gudunsa ya buɗe masa gate ɗin. Sai da ya gama ƙarema harabar gidan kallo da duk motocin dake cikinsa kafin ya furzar da nannauyan numfashi ya fito, dan Gebrail ya buɗe masa tuni.
Cikin gidan suka nufa yanama Gebrail tambayoyi, shi kuma yana amsa masa cike da damuwa, dan har cikin ransa kunya da ƙaunar Yoohan ce cike da ruhinsa. Bama shi kaɗaiba, duk sauran ƴan uwansama hakane. Suna shiga kuwa da gudu su Victoria sukazo suka rungumesa. hakama mama debora rungumesa tai tana kuka da rera addu’ar neman sakayya a garesa da yarensu. Ba itaba ko mai saurarenta yaji yanda take addu’an zaisan akwai tausayi a ciki.
Da ƙyar Yoohan ya lallashesu sannan suka zauna suka ɗan sake tattaunawa. Mama debora tace tunda har papa ya kashe ɗan uwansa da matarsa itama ta yarda a kashesa. Yoohan dai kunyar su Gebrail ya hanashi cewa komai akan iyayen nasu, daga ƙarshema yace su shirya zai wuce da su.
Zan iya cemuku a ɗar-ɗar su mama debora suke da zuwa gidan Jay, kamar yanda sukaita ɗari-ɗarin zuwa kano gidansu Nu’aymah. Sai dai abinda ya basu mamaki anan ma sai akai musu tarba ta mutunci da kulawa. Hakan yasa suka sakeji a ransu lallai hausawa nada ƙyaƙyƙyawar zuciya a duk inda suke. Sannan musulmai ba mutanen banza bane kamar yanda a kullum papa ke musu huɗuba a gida da church. Sai gashi tundai suna ɗari-ɗari har suka saki jikinsu. Bayan Jay ya dawo suka zauna aka ƙara tattaunawa. Mama debora da su Momy Destiny sunsha kuka. Su kansu su Joy sunji ciwo da kunyar halayen iyayen nasu matuƙa. Sunata kuka da bama Yoohan haƙuri. Shi dai murmushi kawai yake musu. Nu’aymah ma haƙuri sukaita bata akan abinda sukai mata. Tace babu komai ita ta yafe musu. Gebrail kam ko yarda su haɗa ido Aymah baya yarda suyi sam saboda kunya. Ita har dariyama abin ke bata.
____________
Ranar data kasance za’a shiga kotu da su papa ƴan jarida a abuja har bama magana. Kowa burinsa ayi komai akan idonsa. Kuma burin kowa ya nuna komai live. wannan kuwa duk a cikin shirin su Jay ne. Sun gayyato ƴan jaridune ta kowanne ɓangare dansu katange dukma wata kitumurmura da za’a iya ƙullawa game da shari’ar.
Kotu ta cika maƙil itama da al’umma, musamman waɗanda aka samu ƴaƴansu a gidan papa. Duk da ma wasu iyayen nasu sun gagara ganesu, sukuma basusan daga inda aka ɗakkosu ba dan tun suna ƙanana ne. Shari’a ce da bata buƙatar lauya sam, saboda komai na papa a bayyane yake. Zamane kawai da za’ai maganar ƙarajin abinda ya shuka a yanke hukunci kuma.
Yoohan dai da farko baiso su Gebrail su bisu ba. Amma sai Uncle Jay yace ya barsu suje ɗin dan wannan itace kaɗai damar da zasu samu ganawa da iyayen nasu. Badan yasoba kuwa suka shirya suka tafi kotun, cikin amincin ALLAH kuwa sun sami gaba-gaba saboda sun tafi da wuri.
Sai da kotu ta gama cika tab da al’umma, alƙali ya shigo sannan aka shigo da papa da su Mike. Papa saboda harbin da yasha a kafafu sai a wheelchair, sauran kuwa babu ko ƙwarzanen duka a jikinsu amma a ido zaka gansu a wani irin bala’in galabaice. Su Jay kaɗai sukasan irin horon da sukema rayuwarsu cikin hikima. Bayan buga gudumar alƙali kotu tayi tsitt na wasu mintuna, dan da anata ƴan kananun magana saboda shigo da su papa da akayi.
Alƙali ya sakeyin gyaran murya sannan ya fara magana, “Wannan shari’a ce da kowa zai iya fahimtar bata buƙatar wani kaiwa da komawa balle zaman lauyoyi a tsakani. Dan komai a bayyane yake wa duniya akan masu laifin. Amma duk da haka dolene mu karanto musu laifinsu su amsa kafin mu yanke hukunci”. Bai jira amsar kowaba dan ba ita yake jiraba daman. ya bama jami’an tsaro damarsu. Dawood ne ya miƙe ɗauke da file ɗin dukkan bayanan laifukan Papa ya kai ga alƙali. Batare da alƙali ya amsaba ya bashi damar karanto komai.
Tsayuwa Dawood ya gyara yana fuskantar su papa. Ya fara bayani dalla-dalla. a duk gaɓar da yazo ƙarshe alƙali zai ma su papa tambaya akan shin hakane sun aikata?. sukan ɗan nuna tirjiya kafin papan ya tabbatar da sun aikata ɗin. A haka aka dinga bin duk laifukansu daki-daki tare da shedun da suka gani da ido wajen tabbatarwa. Hakanne yaja shari’ar tai tsaho sosai aka jima ba’a tashiba.
Ƙara jin bayanan sai ya ƙara komawa mutane tamkar sabo a cikin kunne, wasu harda hawaye sukeyi, wasu ko kawai gani suke babu hukuncin da su papa suka dace dashi sai mutuwa. Da ƙyar Alƙali ya samu kotun nan ta lafa da ga hayaniyar data ɗauka akan cecekucen jama’a. Ya ɗauki ruwan dake a gabansa ya sha cike dajin gajiya da damewar tunani wajen yanke wannan hukunci.