SARAN BOYE 77

    Bayan kotu ta sake lafawa alƙali ya fara magana kamar haka, “Ya kamata kuyi hakuri ku bamu haɗin kai, nasan duk wani hukunci da zamu yanke anan bai zama lallai ya gamsar da waɗanda wannan mutane suka cutarba. Amma zamuyi iya bakin ƙoƙarin mu dan ganin mun yima kowa adalci. Sun tafka kura kurai da kowanne idan zamu ɗauka yanada nashi hukuncin ne, to amma kisan kai da suka shigo sun shanye duk wani laifuka nasu. ALLAH kaɗai yasan iya rayukan da suka salwantar, dan kosu a yanzu ba iya lissafawa zasuyi ba. Dan haka wannan kotu mai adalci, ta yankema waɗanan mutane hukuncin kisa ta hanyar rataya”. Yana gama faɗa ya doka gudumarsa.

    A take kotun ta ɗauki ihun kace nace ɗin mutane. Har bakajin zancen wani. Sai dai duk wannan surutai babu mai goyen bayan su papa. Wasuma duk da an ambaci kashesun za’ayi su hukuncin sai bai musu ba. a ganinsu ayi gunduwa-gunduwa da su kamar shine yafi dacewama kowa ya huta. Kamar yanda kotu ke a harmutse haka jama’ar gari ke a harmutse dan ƴan jaridu nata kai rahoto live. A take duniya gaba ɗaya ta ɗauka. Inda wasu ƙungiyoyi kamar Masu kare haƙƙin ɗan adam suka fito suka nuna bore da wannan hukunci. Har suna iƙirarin ɗaukaka ƙara. Sai dai to bamusan zuwa wane kotu suke da burin ƙarar ta kaiba, tunda mudai anan Nigeria a babbar kotun ƙasa gaba ɗaya aka yanke hukuncin.

       Duk yanda Yoohan yaso su mama debora su gana da Papa al’amarin ya gagara dan da ƙyarma aka fiddasu daga cikin kotun. 

______________★★

         Bayan kwanaki biyu da faruwar wannan al’amari da safe su Jay na tsaka da yin breakfast ya samu waya daga alƙali cewar sufa sun gama yanke hukuncin su papa. Dan sun fuskanci al’amarin neman canja salo yakeyi na ƙirƙirar rikici da hukumar kare haƙƙin ɗan adam ke neman haddasa musu. A yanzu haka maganar da ake ga gawarwakin su papa nan, a gaban ƴan jarida akai komi yanzu kuma zasu bada damar a saki labarin.

     Al-amarin ya girgiza zuciyar Jay matuƙa, to amma shima hakan yafi masa sauƙi tunda dai shine hukuncin da aka yanke musu a gaban kowa. Koda sukai sallama da shugaban alƙalai bai iya yima su Yoohan bayanin abinda ya faruba sai Miemaa kawai. Ita kanta duk da tasan su papa masu laifi ne sai da tausayin mama debora ya ƙara kamata da su Victoria. To amma wannan shine dai-dai kuma abinda ya dace..

      Kafin shabiyun rana labari ya gama zagaye ƙasar dama duniya akan zartar da hukuncin da aka yankema su papa. Wasu kam sun ɗauki ɗumi akan hakan, dan duk da mummunan halin su papa suna samun magoya baya musamman masu irin halayyarsu da ayyukansu. To andai yita ta ƙare. labarin su papa kuma ya zama tarihi, sai kuma na baya garesu, dan yanda mutane. kirki basa ƙarewa hakama mutanen banza kullum sake yawaita suke.

     Mama debora dai tasha kuka a ɓoye, dan ɗa da mahaifi sai ALLAH, musamman daya kasance mazan ƴaƴanta har uku. To amma tunda ta rasa mahaifin Yoohan da yafi sonta da ƙyautata mata tai haƙuri, dan ta rasa waɗanan azzaluman minene zaisa ta takura kanta kuma. Su Joy ma dai saida suka koka sosai. danma an hana Abraham da Victoria kallo sam. 

     Yoohan kansa sai da yay hawaye, koba komai yasan su ɗin jininsa ne. Nu’aymah ce kawai ta iya fahimtar shima kukan yayi, dan haka tana ganin ya fita itama ta bisa a sace ta ƙofar kitchen. Acan baya ta hangosa tsaye ya jingina da bango yay shiru idanu a lumshe. Ƙarasawa tai garesa ta kamo hannunsa cikin nata. Kusan a tare duk suka sauke ajiyar zuciya. Batare da yace da ita komaiba ya jawota jikinsa ya rungume. Luf kuwa tayi kusan mintuna uku sannan ya ɗagota yana murmushi. Kafin yay magana tace, “Silly boy! Kuka kakema waɗanda suka kashe mana su Abbabmu saboda son zuciya”.

     A karon farko ya saki murmushi da shafa fuskarta. Murya a raunane yace, “Silly girl! Kin samin ido da yawa fa”.

      Dariya tayi kaɗan ta kwantar da hankali, sannan ta ɗan marairaice fuska cike da kulawa tace, “Sai haƙuri Yah Maleek, haka rayuwa take, wani farkonsa yaji daɗi ƙarshen yasha wahala. Wani yasha wahala a ƙarshe yaji daɗi koba a duniyaba. Kaji labarin gwagwarmayar da Uncle Jay yasha shima shi da Miemaa. Amma bagasu komai ya wuce a garesuba tamkarma bai faru ba. Muma idan mukai haƙuri sai kaga komai ya zama tarihi insha ALLAH ”.

     Cike da jin daɗi ya sake rungumeta da sumbatar laɓɓanta. Ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. “Thanks you Zeeynab. Kin gama bama rayuwata dukkan abinda take buƙata, ALLAH yay miki albarka ya albarkaci Deen, ALLAH yasa ya zama mai gadon baba malam. ALLAH ya gafartama iyayenmu ya ƙara mana haƙuri da abinda ƙaddara ta danƙa mana a tafin hannunmu”.

     “Amin ya rabbi yah maleek”.

Sake rungumota yay jikinsa yana dariya ƙasa-ƙasa da fadin, “Sunan nan fa yayi daɗi Sweet girl”.

      “Sosai ma, Mami da Abba sun iya zaɓen suna. Kaga yanzu ka zama mai suna biyu, danni kam daga yau Abdul-maleek zanke faɗa”.

      “Silly girl! ki rage jan faɗa yanzu akwai Deen a gabanki”. Ya faɗa yana jan hancinta.

    A tare suka sanya dariya, suna maijin farin ciki mai yawa a ransu.

        A daren ranar kuma sai ga saƙon rasuwar Addah ya samesu. Duk da abinda ta tafkama rayuwarsu Nu’aymah sai da taji duk ta rikice. Tasha kuka kuma a daren ranar. Washe gari kuwa tunda safe suka ɗauki hanyar kano a mota harda su Jay, cikin sa’a kuwa suka samu jana’izar Addah, dan sai goma aka kaita masaukinta na gaskiya. Sai kuma aje a girba abinda aka shuka.

     Duk da abinda Addah taima Umm rasuwarta tayi masifar girgizata, dan saida takai an saka mata ƙarin ruwan daya sakata dogon barci saboda ruɗanin data shiga. Jikin kowa ya ƙara sanyi kuma a agidan harma da sauran ƴan uwa. 

        Da yamma su Yoohan suka koma Abuja aka bar Nu’aymah anan kano, sai bayan anyi addu’a Yoohan yace zaizo ya ɗauketa dan zasuje Oman wajen dangin mahaifiyarsa da ƙaddara ta maida can.

        *_BAYAN SATI GUDA_*

Bayan sati ɗaya da rasuwar Addah da mutuwar su papa Yoohan yazo da kansa ya ɗauki Nu’aymah da Deen suka koma Abuja, zuwa yanzu kuma Alhmdllh Umm ta ɗan dake saboda kulawa da baba malam keta bata dan ganin ta samu kwanciyar hankali. Hakama Hajarah daketa fama da tsohon ciki sai Umm ta roƙu mijinta ya barta ta dawo nan gida harta haihu dan itama rasuwar mahaifiyar tata ta taɓata sosai. Bai musaba ya barta ta dawo, tana nan zaune wajen Umn yanzu haka. Zaman natanema ya ɗan ragema Umm raɗaɗi. Hajjo kuma koda yaushe takan yawaita shigowa ta sake kwantarma da Umm hankali itama, hakama Ananah da bata komaba.

*_OMAN_*

       SU Nu’aymah sun isa Oman lafiya, inda suka sami tarba ga dangin Mami (Anum) dan tunkan zuwansu labarin komai yazo musu. Abin mamaki sai su Yoohan suka sami Dr Shikurah acan Oman, ashe kanwarta datake faɗa ɗanta na kama da Yoohan itace ke auren yayan Anum da suke uba ɗaya. Sun haɗune acan Oman da taje karatu, a yanzu haka yaransu kusan shidda. Mahboob mai tsananin kamanni da Yoohan shine yaronsu na farko. Idan ka gansu shi da Yoohan saika ɗauka tagwayene saboda tsabar kamanni da sukeyi da juna, abin mamaki har tafi har maganarsu iri ɗayane. Sosai abin ya birge Yoohan. Har yaji a ransa inama ya amince tun sanda Dr Shikurah ke masa kamanni da Mahboob ɗin ya amince ta kawosa yagansa. To amma ya ɗauka hakan kawai matsayin abinda ALLAH bai hukunta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button