SARAN BOYE 77

Da yake anzo dasu mama debora suma sai hakan yasaka dangin Anum ƙara jin daɗi, dan koba komai sun ƙara yarda IBRAHEEM mutumin kirkine shi. Ansha kuka da tunawa da rasuwarsu da yanda rasuwar tazo. tare da jifan su papa da kalmomin ALLAH wadarai danma ana ɗan tagawa darajar mahaifiyarsa dake a wajen.
Deen da Nu’aymah kam lallai sunga soyayya ƴar gaske, dan gatan da Yoohan bai samu ga dangin uwaba a yanzu kowa ƙoƙarin ganin ya nunama Deen yakeyi. Sunga gata kam sun kuma sha daɗi Alhmdllh. Satinsu uku cif suka dawo Nigeria badan ƴan Oman sunso hakaba.
Suna dawowa kuma aka shiga hidimar bikin Naser & Yusrah, Abdallah aka maida masa Adawiya suje su cigaba da haƙuri da juna. Amal da malam ƙarami. Ahmad da Nanah yayar ƙanwar Umm. Ansha biki an raƙashe an ƙwalle Alhmdllh, yayinda Abban Abdallah ke kwance yana fama da kansa shima. Dan shikam bikinma bazaice yasan anyiba. To dama haka rayuwar take ai.
Bayan an gama biki an miƙa amare ɗakunansu komai ya zama Alhmdllh Yoohan ya tattara matarsa da ɗan ɗansu da yay ɓul-ɓul gwanin sha’awa syuka koma ƙasar U.S saboda karatun Aymah, shi kuma zai koma aikinsa na hidima wa al’umma.
Basubar ƙasarba sai da ya nemawa su mama debora gida anan kusa da su Uncle Jay aka saya musu, dan mama debora ta rantse bazata sake zama gidan can da papa ya gina ba. Hakan yasa aka saidashi suka dawo nan. Gebrail da Joy an nema musu makaranta a ghana. Mama debora zata cigaba da zama dasu Victoria dasu mama Destiny da suma suka dawo nan tare da mazajensu. Dan zaman can kauyen kam bazai yuwu yanzu a garesuba.
_____★
Tunda su Nu’aymah suka dawo fa sai ta ɗaura ɗammarar dagewa akan karatunta, haka shima Yoohan ya sake dagewa akan neman iliminsa na addini. Ga renon ɗan ɗansu daketa ƙara girma masha ALLAH.
Soyayyarsu da shaƙuwa kuwa sai abinda yay gaba. Yayinda Hajiya Nu’aymah aketa ƙara canjawa ana hankali da rage fitsara kamar ba itaba. Ga jikinta sai buɗewa yake tana ƙibarta masha ALLAH.
Haka rayuwa ta ciga da gunguramawa waɗanan bayin ALLAH, yau asha zuma gobe asha maɗaci. Da sun sami hutu sukan shirya suje Nigeria, hakama ƴan Nigeria ɗin lokaci-lokaci Yoohan kan ɗakko wasu a cikinsu suzo su musu hutu.
Daga Deen dai Nu’aymah shiru, da alama kuma dai sune asuka tsarama kansu hakan, dan a yanzu haka ga Deen da shekara ta huɗu, Nu’aymah kuwa na shirin kammala karatunta. Yaro ya girma yay wayau, ga miskilanci ga zuciya ko kuturu haka ya gansa ya bari.
burin Yoohan dama nu’aymah ta kammala karatunta ya tarkatasu ya maida Nigeria, cikin amincin UBANGIJI kuwa sai gashi ta kammala lafiya cike da nasarorin rayuwa. Wannan karon kuwa Umm da baba malam ma sunzo U.S, taso azo da hajjo baba malam yaki dan tsufa sosai ya ƙara kamata, ga ciwon ƙafa dake damunta. Kowa ya taya Aymah murna da nasarar data samu daga ita har mijinta, bayan kammala komai suka tattaro zuwa ƙasarsu ta haihuwa, inda Yoohan ya saya musu gida suma duk da su Jay sunso Yoohan ɗin yay zamansa anan gidansu, amma ya ƙi, dan gaskiya yanajin kunyarsu ainun.
Ƴan uwa da abokan arziki sun tayasu murnar gida. Dan ƴan kano ma duk saida sukazo, harda su Aunty Kubrah da zuwa yanzu tayi haƙuri a gidan aurenta duk da ba daɗin zaman takejiba dai.
A wannan dawowane kuma kowa ya fahimci Nu’aymah laulayin ciki takeyi. Anko tayasu murna da addu’ar ALLAH ya raba lafiya.
Dawowarsu baifi da wata guda ba ALLAH yayma abban Abdallah rasuwa shima. Ansha alhini ansha kuka, daga baya kowa ya rakasa da addu’a.
*_A KWANA A TASHI_*
Lallai kam akwana atashi babu wahala wajen UBANGIJI, dan yanzu shekarun Auren Nu’aymah da Yoohan goma kenan. Zuwa yanzu ALLAH ya azurtasu da ƴaƴa uku, Deen, Ibrahim, sai auta Anum. Jay ne ya hana a ɓoye sunan yaran, yace a bari ake kiransu da sunansu hakan zaisashi farin ciki. Dan haka aka barsu kuwa da sunayensu ana kiransu da shi.
Abubuwa da dama kam sun faru a waɗannan shekaru, masu daɗi da akasin hakan sai dai kawai muce Alhmdllhi ala kulli halin.
*_“Sweet girl! Sweet girl!!”_*
Nu’aymah da ke a can backyard tana shanya kayan su Anum data wanke tana mita ta jiyo Yoohan na ƙwala mata kiran mafarauta. Kanta ta dafe dan ta tabbatar su Anum ne suka hanashi barci. Dawowarsa kenan babu jimawa daga asibiti a gajiye matuƙa. Sabodama kar yaran su gansa su hanashi hutawa a wajen gate yay fakin, ya shigo gidan a saɗaɗe saima yay sa’a su suna a can garden suna wasa Nu’aymah ta korasu itama ta huta. Shiyyasa itakam batama cika son weekend tai musu a gidanba. Tafi buƙatar su wuce gidan Uncle jay ko gidan Aunty Little ko wajen su maman Destiny.
Jin ya cigaba da ƙwala mata kiran yasa ta ajiye abin matse kayan dake a hannunta ta nufi ciki da sauri. Ilai kuwa samun duk yaran tayi a bedroom ɗinsa ɗane-ɗane bisa gado kusa da shi kowa na ihun sai ya tashi an kaisa gidan Abie (Jay). Kai Nu’aymah ta dafe sannan ta ɗaure fuska ta daka musu tsawa. Tsitt kuwa sukayi kowa na kwaɓe fuska.
Sai a lokacin Yoohan ya janye filon daya cusa kansa a ciki ya tashi zaune, kallon yanda yaran duk suka zuba tagumi yay, ya kuma dubi yanda Nu’aymah tai bala’in tsare gida. Sai shima kawai yay tagumi kamar yanda yaran sukayi ya zuba mata ido. Hararsu tayi su duka ta ida shigowa cikin ɗakin. Da sauri Ibrahim dake da shekaru shida ya matsa jikin Yoohan ya lafe, sai itama Anum dake da uku ta matsa ta lafe. Duk yanda Yoohan yaso daurewa sai ya kasa ya saki ƙaramar dariya yana kama kunnuwansu yaja kaɗan.
“Wato kuɗinnan fa nagama ni kuka raina a gidan nan, ita Mie-mie kuna tsoronta, amma ni kunma maidani Uncle Jay kakanku ko?”.
Yanda yay maganarne ya saka Nu’aymah yin dariya itama, ta yamutsa fuska da faɗin, “Dan ALLAH ka tattarasu ni kama kaisu gidan Miemaa, abar min Deen kawai anan”.
Cikin ɗage gira Yoohan yace, “Oh, saboda kinga yarona mai hakuri kina samin shi aiki ko. To naƙi wayon, waɗanan tom and jerry ɗin zan bar miki anan, Abbana kuwa kano ma zan kaisa yayma Umm Hutu da Uncle Muhammad. Inama yake?”.
“Haba Yah Maleek dan ALLAH kar muyi haka da kai, waɗanan mi suka iya banda takurama mutane”.
“Hhhh kunfi kusa ai. Kai mai jan kunne ina Abbana yake?”. Yoohan ya faɗa dajan kunnen Ibrahim.
Ƙwaɓe fuska yaron yayi yana tashi daga jikinsa ya koma wajen Nu’aymah. “Mie-mie ALLAH nama fasa sayama Dada birthday gift ɗin da nace miki tunda bazai daina cemin maijan kunne ba. Gashi nan har Wannan Anum ɗin ta kama bayan itama jajayen kunnen ne da ita”.
Sosai Yoohan da Nu’aymah suka kwashe da dariya. Cikin dariya Yoohan yace, “A to indai hakane bazan sakeba Abban Mie-mie. Zomu shirya kaji”.
Ɗan jimm yaron yayi, sai kuma ya kalli Aymah. “Mie-mie kin yarda na shirya da shi?”.