SARAN BOYE 77

“Hhhh haba Abbana wake fushi da babansa dama inba shashasha ba”.
“Ai dama nima bana fushi da shi ko Dada?”.
Yay maganar da matsawa jikin Yoohan dake kallonsu da murmushi. Rungumesa yayi sannan ya dubi Aymah da wani narkakken kallo. “Wai ina Abbana?”.
Miƙewa tai tana bashi amsa. “Yana ɗakinsufa yana gyarawa, dukansa nai shiyyasa yaƙi fitowa, yana can yana faman haɗiyar zuciya uwa budiddigin ƙwaɗo”.
Sakkowa Yoohan yay daga gadon ɗauke da Anuma yana faɗin, Ayyah Mie-Mie mi mukayi haka ne harda taɓa mana lafiyarmu?”.
“Miskilancin da kuka saba mana. Yaron nan a gabansa na gama gohon gyara musu ɗaki wai dan wulaƙanci yana zaune a ɗakin su Anum suka sake hargitsashi bai hanasuba shi shugaban miskilawan Najeriya. Shiyyasa na dakesa dan gobe idan sunyi ai ya hanasu ko”.
“Aiko a kansu zansa ya rama. Abbana kana ina?”.
Kafin Aymah ta bashi amsa Deen ya fito daga ɗakinsu baki cike da iska. Yana ganin Yoohan sai gashi da gudu yazo ya rungume Dadan sa.
Cike da so da ƙauna Yoohan yace, “Oh my sweetheart so sorry yeah. Bar Mie-mie anayin hutu Kano zan kaika wajen Umm da Uncle. Aiko cike da jin daɗi yaron ya hau murna. Yayinda su Ibrahim suka koma jikin Aymah suka lafe wai sunan jealous ya motsa. Dariya Yoohan yayi suma ya miƙa musu ɗayan hannunsa. Da gudu kuwa suka ƙaraso ya haɗasu ya rungume yana maijin farin ciki a ransa da samuwarsu a garesa matsayin ƴaƴa. Waɗanda suka fito daga tsatson Nu’aymahrsa mai rigima da tsiwa. Shikam babu abinda zaicema ALLAH sai godiya kuma, dan ya gama masa dukkan rahama. Ko a musilinci n daya tsunta kansa a ciki bayan dulmiyar da shi da su papa sukayi ai ya gamacin ribar rayuwa. Balle kuma daɗin daɗawa ga ƙyautar mace ta gari da ƴaƴa nutsatstsu da ALLAH ya bashi. Wanda ya tabbatar tarbiyyar mahaifiyarsu ma tana taka rawar gani wajen samuwar tasu. Shiyyasa akace ka nemawa ƴaƴanka uwa ta gari, matama su nemawa ƴaƴansu uba na gari. Fatansa ALLAH ya raya masa su da baiwar ilimin addini tamkar mahaifiyarsu. Duk da shima zuwa yanzun Alhmdllh, ya sauke alkur’ani mai girma haryayi nisama a hadda. Yasan littatafai masu yawa na addini, bai kuma tsaya a hakaba yana cigaba da neman ilimi babu dare babu rana. Dolene ya kasance mai yawan ambaton Alhamdulillahi ala kulli halin a kowanne dakiƙa na rayuwarsa, suka kalli juna shida matarsa suna murmushi, hannu ya miƙa mata itama tazo ta haɗasu ta rungume cike da godiyar UBANGIJI mai rahama mai jinƙai