HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

Page 1-2

 

Sanyin la’asar ne ya sauka ya haɗe da sanyayar iskar da ke kaɗawa, giza-gizai na gudu hadari sai gangamuwa ya ke yayinda garin sai ƙara lumshewa ya ke yana ƙara duhu.
Mutane sai harhaɗa kaya suke suna guduwa,abubuwan hawa na ta wucewa kowa na ƙoƙarin ƙarasawa gida kafin ruwa su sauko saɓanin malam Nur da ya ƙara gyara zama akan kujerar shi sai cigaba da koyar da karatu ya ke ba tare da yayi la’akari da yadda Ɗalibai sai leƙen waje suke ta manyan tagogin ajin ba.

Cikin dadaɗar muryar shi ya ke rero ƙira’a mai shiga rai da ɓargon jiki amman sam Ɗaliban hankalin su bai wajen shi.
Lura da hakan yasa shi rufe Qur’anin yana fuskantar su “ku nutsu in kuna nutsuwa dan babu wacce za ta fita sai ta biya min wannan shafin tom”ya faɗa yana tamke fuska tamau alamun babu wasa a ciki,sanin halin malam Nur yasa duk suka shiga hankalin su duk da ya kasance mai barkwanci amman wani sa’in ya kan rikiɗe ya koma miskilin malami ta yadda ko ƙwaƙwaran motsi mutum bai yi in yana cikin aji musamman lokacin karatu.

Karatu suka cigaba da yi cikin nutsuwa suna koyon yanayin yadda duk ya lanƙwasa ƙira’a wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya ke ma malam Nur ba.
Tun da aka fara karatun yana lura da ita yadda ta takure wuri guda sai ƙanƙame jikinta take alamun jin sanyi duk da tana cikin ƙaton hijabi.Zuciyar shi ce ta fara rawa,tausayinta ya tsargu a ran shi cikin hikima ya sallami ɗalibai cike da murna suka fara fita aji duk yana kallonta har lokacin da ƙawarta Samira ta kama hannunta suka fice.

Lumshe ido yayi yana sauraren bugun zuciyar shi,tunda ya sanyo ƙafa makarantar nan ƴan mata suka fara rubibin shi daga masu nuna alamar suna son shi sai masu turo mashi saƙo amman ita ko kallon shi bai dameta ba.
Buɗe ido yayi jin ƙarar saukar ruwan,miƙewa yayi ya buɗe window yana leƙawa yayafi ne ake amman masu zowa da gudun nan.

Cikin zuciyar shi ya ke tambaya “shin ko har ta kai gida?”dan ya ga alamu bata son sanyi sosai,huci ya sauke kafin ya ɗauki makulin motar shi ya fito.

Filin makarantar tsit ya ke dan dama duk sauran malumai sun dade da tashi ajin shi ne wanda ya kasance ajin ƙarshe(na manya ga ba ɗaya)kawai ya tsayar da su.
Ƴar ƙaramar ƙofa yabi ya fita inda yayi parking ya nufa ya shige tare da yi ma motar key bai tsaya ko ina ba sai bakin tangamemen get ɗin gidan su ba,horn yayi mai gadi ya buɗe ya shige.
Tun kafin ya shiga falon ya ke jin ƙarar sauti na tashi,cak ya tsaya yana kallon su yadda suke rawa tamkar ƴaƴan makaɗa sam ba su lura da shi ba sai sauka wayar courant suka ji ihu suka fara suna neman agaji amman ƙarar tv ta hana aji sai da yayi masu lilis sannan ya ƙyale su tare da kashe tv.Sai kuma a lokacin Maman ta sauko tana hararen su kafin ta tsayar da malam Nur da ke ƙoƙarin buɗe ɗakin shi “Ustaz sai yanzu ka dawo tun ɗazu nike ta tsimayen ganin ka”tsayawa yayi jin muryar mahaifiyar shi,gaisheta yayi sannan ya ƙara da “eh Maman shigowata kenan kuma sai na tarar da uwacan maras hankalin suna shaƙiyanci duk da sun san sun yi laifi na ƙin zuwa makaranta shine suka ƙara da wani laifin”ya ƙarashe maganar yana ƙyaci alamun jin zafi abun.

Inda suke a rakuɓe Maman ta kalla tace “ku tashi ku fice min da gani in ba shashanci ba ana ruwa zaku saka kiɗa maimakon karatun Alkur’ani,ai Ustaz in ka dara ta uwanan sai su hauda maka hawan jini”tana gama rufe baki suka miƙe cikin azama suka shige ɗakin su.
Ƙarasowa yayi kusa da mahaifiyar tashi yana kallon ƙullin maganin da ke hannunta,miƙa mashi tayi ya karɓa tare da dubanta yace “na miye kuma wannan?”
“Cikin ruwan wanka zaka zuba shi sannan ka kaɗa cikin madara ka sha,dan Allah kar kace min a’a ko tambayata ba’asi”shiru yayi yana nazarin maganai kafin yace “toh maman in shaa Allah zan yi yadda kika ce”da murmushi Maman ta dafa kan shi tace “Allah yayi maka albarka ya cika maka burin ka na alkairi”da “Amen”ya amsa kafin ya wuce part ɗin shi ita kuma Maman ta shiga kitchen.

 

Sanin darajar mahaifiya da girman alƙawari shi yasa Ustaz yin amfani da maganin ba tare da ya san ko na minene ba,abinda ya sani dai uwa ba za ta taɓa cutar da Ɗanta ba.
Yana fitowa daga wanka ya saka doguwar jallabiya fara sol ya kunna ƙira’a a Sheikh Sudais yayinda kuma yake yin tasbihi da hannun shi,idon shi a lumshe suke yana jin sautin ƙira’ar na ratsa shi gefe guda kuma tunani Nazifa ne maƙale a zuciyar shi sai dai da zarar ya fara sai yakice ta a rai kasancewar yau Litinin yana ɗauke da azumi a bakin shi.

Kiran sallah da portable ɗin shi ta ɗauka ne ya sa shi saurin miƙewa ya ɗauro alwala ya fito falo inda kayan buɗa bakin shi ke jiran shi.Kamar kullum yau ma Maman ta ƙayata ɗan ƙaramin moquette ɗin da ya ke zama lokacin shan ruwa da kayan ciye-ciye.
Zaunawa yayi akai tare da tanƙwashe ƙafafun shi,addu’o’in shi na yau da kullum ya fara kafin ya gabatar da buɗe bakin.
Sanyayar ajiyar zuciya yayi lokacin da ya kwankwaɗi jus de pein de singe wanda ya sha kayan haɗi,wani jus ɗin ya ƙara tsiyayawa a kofi ya ɗan saka maganin da maman ta bashi ya motse sannan ya shanye.

Ruwan saman da ake ne suka ɗan tsagaita wanda ya ba musulmai maza fitowa yin Sallah magrib,duk da an yi ruwa masallacin cike ya ke da jama’a su Ustaz sune a sawun gaba kamar kullum.
Sai bayan an gama sallah ne ya gaida mahaifin na shi wanda mafi akasari shi ke jan sallah magrib, isha’i da asubah.Cike da kulawa Baba ya amsa yana tambayar shi journée ɗin shi “bien passé Baba ya gajiya ?”cewar malam Nur,a takaice Baba ya amsa mashi da “alhamdullah”kafin suke rankayowa gida.

Ko da suka zo gida sun tarar da Maman da ƴan matan ta suna cin abinci,hararen su Nur yayi yana amsa barka da shan ruwa da Maman ke mashi kafin ya wuce part ɗin shi.
Ƙaton hoton cadre ɗin ya ƙura ma ido yadda take murmushi gwanin kyau sai ta banbanta da sauran Ɗalibain da alamu ita bata ma san an ɗauki hoton ba,daidai fuskarta ya shafa ya na mai dafe saitin zuciyar shi.

 

 

A ɓangaren Nazifa kuwa tun zuwanta gida ta duƙunƙune cikin bargo tana hawayen azaba yayinda ƴan gidan su suka yi cirko-cirko suna jajanta ma juna game da ciwon Nazifa wanda sai gaba ya ke babu sauƙi.

Inna ce ta ƙarasa kusan da ita ta yaye bargon tana mai taɓa wuyanta,rau ya ke sai ɗan karen zafi kamar garwashi haƙoranta kuwa sai karkar suke suna gamuwa.Cikin tausayi Inna ta dubi yaya Ɗalhat tace “ko likitar mu ke zuwa?tunda maganin ya ƙi yi mata aiki” ajiyar zuciya ya sauke yace “toh Inna mu je can ɗin amman ba zuwan ba kar mu je su tsula mana kuɗi”murya na rawa Inna tace “a’a ai likitar gwamnati za mu je tunda can kuɗin cahier kawai zamu biya,je ka taro mana ɗan sahu “da sauri Ɗalhat ya fita ba jimawa sai gashi ya dawo duk ya jiƙe da ruwa,kamar wata gawa haka ya naɗota cikin bargo tare sungumarta ya shigar da ita adaidaita.Gaba ya shiga ita kuma Inna ta zauna baya tare da Nazifa ,CSI Ali Shaibu ɗan sahun ya kai su kamar yadda suka buƙata.
Adaidaitar na tsayawa Ɗalhat ya fito zai ɗaukar ta cikin murya maras lafiya tace “zan iya tafiya da kaina”taimaka mata yayi yana tattare bargon suka nufi ciki,Inna na ƙoƙarin kwance kuɗi ta sallami mai ɗan sahu yace ta bari godiya tayi mashi ta mara masu baya.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button