SULTAN HAUSA NOVEL COMPLETE

SULTAAN 7

 ???? *S U L T A A N*Mss Flower????

*FITATTU HUƊU????*

_RESEMBLANCE OR SIMILARITIES OF STORY/LIFESTYLE SHOULD BE CONSIDERED AS TOTAL COINCIDENCE_

*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

           *07*

*ZEENA POV* 

Sanyin iskar asuba ce ta sanyata buɗe idanunta, da sauri ta ja ƙyallen da ya yi gefe ta kare jikinta, yanda ta ji garin tsit ga duhuwa ya tabbatar mata lallai ba safiya, ko rana ba ce, haka ba farkon dare ba ne, wani irin ciwo kanta yake haɗe da dukkan jikinta musamman ƙasanta da ke mata wani irin zugi, tana ƙoƙarin tashi zaune ta ji wani abu a hannunta, dubanta ta kai sai ta ga sarƙa ce a hannunta, take abin da ya faru tun daga fitowarta gida har kawo yanzu ya shiga dawowa kwanyarta, wani irin hawaye mai mugun zafi suka shiga zubo mata, ta fahimci zafin da take ji fyaɗe aka yi mata kuma ba Nuri ba ne, mammalakin wannan sarƙar ne wanda ta gaza tuna fuskarsa, wani irin ɗaci ta ji tun daga ƙirjinta har kawo kan harshenta, ta yunƙura ta miƙe tare da ɗaura fyallen, a daddafe ta nufi hanyar gida tana jin tsananin azaba, ta yi tafiya da ɗan nisa idonta ya sauka akan gawar Nuri, da gudun bala’i ta ƙarasa inda yake ta shiga jijjigasa tana wani irin kuka haɗe da cewa “ka tashi, don soyayyarmu ka tashi!”, Wani irin kuka take mai fizgar rai kamar ranta zai fita, kafin ta yunƙura cikin layi ta nufi hanyar gidansu, tun kafin ta ƙarasa inda gidajensu yake ta tabbatar da babu lafiya, ganin yanda wasu daga cikin gidajen suka rurrufza, ga ihun mata da kukan ƙananan yara, wani irin firgici ya kuma kama zuciyarta, addu’arta ɗaya kada a ce prophecy da ya zo a kanta ne ya tabbata, rushewar ƙabilarsu ta dalilinta, halakar duk wani makusancinta, duk da azabar da ke ratsa ƙafafuwanta da gudun bala’i ta nufi gidansu, wani irin ƙara ta saki ganin dukkan ɗakunan gidan sun rufta, durƙushewa ta yi tana wani irin kuka mai gunji tare da dafe kanta tana cewa “na shiga uku, na lalace, na rasa kowa, me ya kaini na fita!” 

“Zeeeenaaa!” Ta ji muryar Amma da ke cikin wani irin tsananin ciwo ta kirata, da sauri ta dubi wajen da sautin ya fito kafin ta je da gudu ta durƙushe tana wani irin kuka duk ta rirriƙe Amma da jikinta duk ya ɓaci da jini. 

“Kin tabbatar da boka ba ƙarya ya yi ba ko?” Amma ta ce cikin tsananin ciwo 

“Amma ki yafe min, fyaɗe aka yi min, ban taɓa marmarin karya alƙawarin da na yi miki ba, ki yafe min na roƙeki!” Ta ce hawaye masu mugun zafi na kwaranya daga idanunta. 

“Ki yi nesa da garin nan, kar ki ƙara ba wa mara matsayi zuciyarki, idan ba haka ba haka za ki kashe dukkan wanda ku ka haɗu da su” ta ce da ƙyar

“Amma na tuba, mu je na kai ki wajen me magani!” Ta ce tana ƙoƙarin ɗaga Amman.

“Ruwa!” Amma ta ce da ƙyar. 

Da hanzari ta nufi wani kwano da ya cika da ruwan sama  don randunansu duk sun farfashe, ta ɗebo, tana isowa ta ga idanun Amma a ƙaƙƙafe alamun babu rai a jikinta, wani irin gunjin kuka ta saki tare da kifawa kan gawar tana jijjigata tana cewa “Amma ki tashi don Allah, Amma ki yi min rai ki tashi, Amma ban san inda zan je ba, ba ni da kowa, ban san kowa ba!” Ta ce tana mata wani irin girgizawa. Ta jima tana kuka kafin ta janyo wani baƙin zani da ya yi tsamo-tsamo a ruwa ta lulluɓe gawar, miƙewa ta yi don ta je wajen sauran mutanen garin su san yadda za su yi da gawarwakin don ita tunani da hankalinta ya ɓace ba. 

Wani irin zazzaɓi take ji ga mugun sanyi ga shi komai a jiƙe yake a garin, ga ɗan figigin ƙyalle ne a jikinta, idonta ya sauka kan wata koriyar rigar Nenne a tsakar gidan da ta jiƙe, hawaye ya zubo mata ta durƙusa ta ɗauka tare da sakawa jikinta tana cewa “shi ke nan Nenne kema kin tafi,Abbu ku yafe min don Allah!” Tana kuka da surutai haɗe da tangaɗi ta fice daga gidan. 

Mutane ta tarar bakin gidansu tsiraru waɗanda suka yi ragowa yawanci mata ne sai ƙananun yara, da mugun kallo suke bin ta wanda hakan ya sa ta sha jinin jikinta, sai ta kasa musu magana kawai ta fara bin su da idanu 

“Mayya, kin kashe mana kowa namu, kin kashe mana mazajenmu sun bar mu ƙananan yara!…Mayya ta kashe har da iyayenta!” Suka fara haɗa baki suna cewa. 

“Fice mana daga gari annoba!” Wata tsohuwa ta ce tana ɗaukan dutse tare da jifanta, kamar jira suke suka din ga ɗaukan duwatsu suna jifanta, hakan ya sa ta fara tafiya da sauri-sauri har ta fara haɗawa da gudu, jifanta suke suna ihun “mayya! Mayya, annoba! Annoba!!” 

Da iya ƙarfinta take gudu ganin sun tasamma halakata, har ta isa bakin tafkeken ruwa wanda nan ne ƙarshen garin ba su daina bin ta da jifa ba, hakan ya sa ta nausa daji ta na cin uban gudu. 

Ta yi tafiya mai nisan gaske har yammaci ya yi kafin ta kai wani ɗan ƙaramin ƙauye, duk da baƙar gajiya da ciwon da take ji a dukkan gaɓoɓin jikinta bai hanata jin yunwa ba, wajen wata mata mai gidan abinci da wajen kwana irin na gargajiya haka ta nufa tare da roƙonta ta taimaka mata da abinci, matar ganinta kyakyawa da alamu za ta samu alheri da ita sai ta ja ta zuwa cikin gida, ruwan zafi ta cika mata a bokiti sannan ta ba ta sabuwar tufa ta ce ta sanya in ta yi wanka, bayan ta yi wanka ta fito ta cika mata kwano da abinci, sai da ta ci ta ƙoshi matar ta ce ta zo su je ta haɗata da wani da za su kwana tare za ta biyata, dama gidan ya gaji haka, firrr Zeena ta ƙi hakan ya sa matar ta fusata ta ce sai ta biyata komai da ta bata, Zeena ta kwantar da kai ta shiga roƙonta tare da cewa za ta yi aiki maimakon wannan ɗin, wanke-wanke ta tula mata inda ta shiga yi, bayan ta gama ta share wajen tare da goge dukkan teburan da aka ci aka sha, sai wajen sha biyu na dare sannan kowa ya watse, matar ba laifi ta ga aikin da Zeena ta sha don haka ta ƙirgo ƴan kuɗaɗe masu ɗan kauri ta bata, Zeena ta roƙeta wajen kwana ta ba ta izinin kwana a wani ɗan ɗaki da babu komai a cikinsa, inda Allah Ya taimaka mata ma da katako aka yi ƙasa ba siminti ba don haka sanyin sai ya ɗan sauƙaƙa, ga kuma garwashi da ta ɗebo cikin wata tasa, daren ba ta iya bacci ba sam, sai kuka da ta sha yayin da tunanin ahalinta da wautarta ta kai su ga halaka ya cikata, bacci sam gagara zuwa mata ya yi a wannan rana, ta ci kuka kamar babu gobe, tun da asuba matar nan ta shigo ɗakin ta ce “idan za ki tayani aikin safe ki fito sai na biyaki” 

Jiki babu ƙwari ta yunƙura tare da cewa “zan yi”, kamar mara laka haka ta shiga hura ƙaton murhu sannan ta ɗora ruwan girki, ta shiga yanke-yanken kayan lambu na abinci, ba su sauke tukunya ba sai wajen takwas har da rabi, lokacin maza har sun cika wajen cin abincin, ita ta shiga raba musu, suna cinyewa tana kwashe kwanukan tana wankewa, ga mazan da dama sai jan ta suke, in ta zo wucewa wasu su bugar mata bombom cike da iskanci, waɗanda suka ce zasu kwana da ita daren yau kuwa Allah Ya yi yawa da su, aringizon kuɗi suka din ga yiwa mai abincin duk dalilinta yayin da wasu suka shaida mata da dare da yarinyarta zasu hole. 

*SULTAAN POV* 

A hankali ya buɗe idonsa da suka yi masa nauyi, dafe kansa ya yi dalilin sara masa da ya yi, ganinsa cikin jirgin ruwan suna ta tafiya ya ja wani dogon numfashi tare da ƙoƙarin gyara zamansa daga kishingiɗar da ya yi, jama’ar jirgin da suka yi sabo da su suka shiga ƙyalƙyala dariya suna cewa “wai giyar ce ta bugar da kai haka?” 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button