Uncategorized

TAKUN SAKA 22

 *_Typing????_**_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

________________________

*_Chapter Twenty two_*

……….Da sallama Habib ya shigo tare da ƙarasa shigowa cikin ɗakin, leda ɗin da ke a hannunsa ya ajiye saman mirror ɗin da yake jingine. 

        “Minene wannan ɗin?”.

Ya faɗa yana zuba lumsassun idanunsa bisa kan Habib ɗin.

       A ladabce Habib ya ce, “Makarin abinda aka shaƙa matane”.

        Kallo ɗaya yayma ledar ya ɗauke kansa. Cikin halin ko in kula ya miƙa masa hannu alamar ya bashi. Ɗakko ledar yay ya miƙa masa, ya ɗan janye hannunsa yana girgiza kansa, Habib da ya fahimci mi yake nufi sai ya buɗe ledar ya ciro handkerchief ɗin da ke ciki ya sake miƙa masa. Amsa yay ya zubama handky ɗin ido tamkar mai nazari, kafin yaja numfashi ya fesar yana ɗago agogon da ke a tsintacciyar hannunsa ya kalla. Ganin lokacin sallar la’asar ya gabato sosai ne ya sashi miƙama Habib Handkerchief ɗin. Batare da yayi magana ba ya nufi hanyar fita ɗakin.

       Sukan fahimci abubuwa masu yawa da ga garesa koda ta kurma yay musu. Hakan yasa yanzun ma Habib ɗin ya fahimta. Handky ɗin shima ya maida a ledar ya ajiye saman mirror ɗin ya bi bayansa.

          Koda ya fito bedroom ɗinsa da ke a saman upstairs ɗin ya nufa, sai dai yana da ga can kusan ƙarshen bangon gabas da falon saman, hakan yasa akwai tazara tsakanin shi da inda ya kai Hibba. Tamkar falukan nan ma komai tsaf, bakajin komai sai tashin ƙamshi da sanyin ac da ya gauraye ko ina. Yanda yake kure sanyin zai tabbatar maka shi ɗin ma’abocin son sanyi ne matuƙa. Dan yanda gaba ɗaya saman upstairs ɗin da ke nuna alamar anan komansa yake ya ɗauki sanyin wani bazai iya jimirin zama cikinsa ba. Shiko ko a jikinsa bai damu ba. Agogon hannunsa ya cire ya ajiye saman mirror ɗin ɗakin, tare da tattare dogon hannun rigar jikinsa sannan ya nufi wani ɗan dogon glass daya ci kusan rabin bangon yana facing ɗin gadon sa. Wani abu ya danna ya zuge kansa, yana shiga kuma ya maida ya rufe.

     Baifi mintuna sha biyar ba sai gashi ya fito cikin sabuwar shiga na wandon jeans da t-shirt. Hakama fuskarsa ta canja zuwa wani daban, gaba ɗaya ƙamshinsa ya gauraye ko ina ya danne na fresheners ɗin da ke tashi a sashen.

      Cikin yanayin kamar fushi-fushi da yake cikine ya ƙarama tafiyar tasa bayyana cikin izzarsa da ƙasaita ta musamman. Ya shiga sauka a steps ɗin cikin salon zafin nama da ALLAH ya azurtashi da shi.

         Daga falon ƙasan yake jiyo hayaniyar su Salis da alamu ya nuna suma shirin massallacin duk sukeyi. Batare da ya ko kalli sashen da suke ba ya zauna a kujerar da ke gab da ƙafar benen idonsa akan wayar sa dake hannunsa.. Saman kunne ya kai wayar tare da ɗaura ƙafarsa ɗa ya kan ɗaya. Ana ɗagawa da ga can cikin bada umarni yace, “Ka sameni kai da baba Saude”. Da ga haka ya ajiye wayar a table ɗin kusa da hannun kujerar ya maida idanunsa ya lumshe.

         Mintuna biyu kacal tsakani Khalid ya fito da ga wata ƙofa bakinsa ɗauke da sallama.

     A saman laɓɓa ya amsa masa batare da ya buɗe idanun nasa ba. Sai da baba Saude tai sallama a ƙarshe sannan ya buɗesu a hankali. 

       “Babana an shigo ashe? Sannunku da dawowa”. Dattijuwar tsohuwa mai cikar kamala ta faɗa tana ƙoƙarin kaiwa zaune ƙasan tattausan carpet ɗin dake a tsakkiyar kujerun.

        Kujera ya nuna mata yana girgiza kansa cike da bata girma. Kafin ya buɗe baki tamkar bayaso ya fara magana. “Tun ɗazun na shigo ai. Na zata kina barci ne baba”.

        Murmushi tayi dai-dai tana kaiwa zaune. Ta ce, “Eh barci ya ɗan figeni kam sanda suka shigo. Nima motsinsu ne ya tadani”.

        Kansa kawai ya ɗan jinjina mata, tare da duban baƙin agogon fatar da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa. Cikin rashin son hayaniyarsa ya maida kallonsa ga Khalid da ke tsaye har yanzun. “Tsayuwar zaka cigaba da min a kai. Ko kiransu ku wuce masallaci!”.

       “Ayi haƙuri boss”. Khalid ya faɗa yana ɗan shafa ƙeya da komawa ciki domin kiran ƴan uwansa.

       Master ya janye idanunsa da ga kallon Khalid da yayi ya maida kan baba Saude. “Baba Saude zaki dawo nan da zama. Akwai yarinya zata kasance da mu anan na wani ɗan lokaci ne, ALLAH yasa bamu takuraki ba”.

       Baba Saude ta ɗan wawwaiga falon, dan ita bama ta lura da kowa ba. Amma sai ta ce, “Babu damuwa Babana, sai na dawo nan ɗin tunda ba wani abu nake acan ɗin ba, ba kuma wanine tare da ni ba balle nai tunanin barinsa. Kwana ne dama kawai ke kaini ai. Sai ina neman lamunin tahowa da ƴar marainiyar yarinyar nan dake wajena”. 

      Kansa ya ɗan jinjina mata, kafin a takaice yace, “Nagode”.

      “Ai nice ya kamata nai godiya da karamcinka gareni babana. ALLAH ya saka maka da alkairi ya jiƙan iyaye da rahama. ALLAH ya bani tsahon rai da lafiyar kaiwa ran aurenka”.

      Wani ɗan ƙasaitaccen murmushi ya saki da kaɗan ya nuna akan fuskarsa. Batare da ya ce komai ba ya maida dubansa ga su Habib da ke fitowa da shirin tafiya masallaci.

           “A gyara mata ɗaki a nan ƙasa”.

     Ya faɗa yana miƙewa.

Cikin rashin fahimta Habib ya ce, “Auntyn ko Baba Saude?”.. 

       Wani malalacin harara ya zubama Habib ɗin tare da nufar hanyar fita. Batare da ya amsa masa tambayar ba yace, “Kaje da ita ta duba abinda babu zuwa anjima a faɗa min idan kun dawo salla, dan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu nake son ta dawo gaba ɗaya”.

        Cike da jin daɗi su Habib suka juyo suna duban baba Saude fuska a washe. “Finally baba Saude zata dawo kusa da mu gaba ɗaya”.

        Ƴar dariyar jin daɗi tayi itama cike da so da ƙaunar yaran tana miƙewa domin yin salla. Suma suka fice cike da murna wannan zance na dawowar baba Saude kusa da su saɓanin da da zuwa kawai take tai musu girki ta wuce da yamma.

       

     

★★★★★

         A can gidan su Hibbah kuwa zuwa yanzu ƴan uwanta sun fara shiga ruɗani, dan kamar wasa babu ita babu alamarta a cikin gidan. Lungu da saƙo sun zagaye har sashen su Hajiya mama da basama tunanin zataje. Tun sunayi su kaɗai har mutane da suka farga suka fara tayasu. Da ga cikin gida takai har an fito waje amma babu ko mai kama da ita. Babu ma wanda yace ya ganta bayan wanda suke a falon Ummi.

     Yaya Muhammad ne ya tuno kiran da Shuraim yay mata. Wanda a dalilinsa ya sakata fita waje dan ta amsa. Kuma tabbas daga haka bata dawo ba har suka fita massallaci.

       Kansa ya dafe yana ambaton “innalillahi….”

      Gaba ɗaya suka maida dubansa gareshi a ruɗe. Ya cigaba da faɗin, “Tabbas Abubakar kayi gaskiya yaron nan hatsabibine na gaske. indai har hasashena yana kan dai-dai tun kafin a ɗaura auren nan ya ɗauke Hibbah.”

      “What!?”.

Yaya Abubakar ya faɗa a razane, illahirin jikinsa sai tsuma yake.

            Yaya Muhammad da ke jin juwa na kwasar sa cikin raunin murya yace, “Ƙwarai kuwa Abubakar ya ɗauke mana ita. Dan shine ya kirata lokacin da muke ɗaukar hoton nan amma sai taƙi ɗagawa, nine na korata waje akan taje ta ɗaga. Na tabbatar da ga lokacinne ya sace mana ita”.

     Saurin riƙosa Isma’il dake a bayansa yayi ganin yayo baya zai faɗi. Yaya Umar kam ai dole ya kai zaune dan ya tabbatar ya cigaba da tsaiwar faɗuwar zaiyi shima. Yayinda tuni idanun Usman da Ammar sun fara kawo ruwan hawaye. Sauran abokansu kam da ke wajen kowa ya shiga halin taraddadi da tausayin su Yaya Muhammad. Dan kallo ɗaya zakai musu ka fahimci tsananin ƙauna da sukema ƙanwar tasu.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button