SULTAAN 7

Ya ɗan yi yaƙe yana ƙoƙarin tuna abin da ya faru sai dai sam ya kasa, komai ya goge daga ƙwaƙwalwarsa. Maƙocinsa ya ce “sannu!” Ya miƙa masa ruwan gorarsa, amsa ya yi ya kafa kai sai da ya sha iya shansa sannan ya cire bakinsa, ɗan ƙunshinsa ya ɗauka na abincin da ya siya sannan ya ɗauko gurasa da dabino ya fara ci, don wata yunwa yake ji. Misalin goma na dare suna tsakiyar ruwa jirginsu ya fara gargada, rawa yake sosai tamkar zai kifa, hakan ya sa jama’ar jirgin kowa ya ruɗe, dukkanninsu suka shiga kirana abin bautarsu. Sultaan rufe idanunsa ya yi yana ambaton Allah a zuciyarsa yayin da kunnuwansa ke jiyo ihun mutanen jirgin musamman mata da bazasu wuce biyar ba, sai kwakwazo suke suna “mun mutu mun lalace”. Wata iska ta kaɗa jirgin ya yi wani dutse ya bugesa, take kuwa ya ɓulle ta gefe ruwa ya shiga shigowa ta ciki, ihunsu ya ƙaru, kuka da kururuwa yayin da jirgin kuma ya fara ƙasa, hakan ya sa jama’ar jirgin suna kuka suka fara fita daga jirgin suna faɗawa tekun da ba sa hango ko wata gaɓar ruwa nan kusa…
*????FITATTU HUƊU????*
*????SULTAAN* # Nml grp ~N~ 300 vip ~N~ 500 via 1401611541 Access bank, shaidar biyanki ta wannan numbern 08167888934
*Mss Flower????*
TSINTACCIYA
Nimcyluv
Baƙar fata
Autar manya
DATTIJON ARZIƘI
Real ladingo
Gaba ɗaya 800
Via 6850917335 Na’ima Shu’aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218
*Mss Flower???? 08167888934* For more information????
[ad_2]