SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Juyowa yayi ya k’alleta da mamaki, har ya bude baki zaiyi magana wayanshi ya fara ringing. Hannu yasa a aljihu ya ciro ganin sunan dake jiki tasa ya dauka yana murmushi
“Old Friend, yau ka tuna dani”
Shiru yayi yana sauraren mai kiran yana murnushi Sannan yace
“Oops! Wallhi bana gida naje wani guri bt nan da 1hr I wl b on my way”
Shiru ya k’arayi Sannan yayi dariya mara sauti Yace
“Kah bata haquri ai nima zanzo”
Sallama sukai ya kashe kiran yana k’allan Sulthana da itama shi take K’allo..

Murmushi yamata itama ta maidar mai, mikewa yayi ya bude motan ya ciro wani leda ya mik’a mata.
“Gashi tsaraba nane”
Mak’e kafada tai tana k’allanshi kasa kasa
“A’a idan aka gani a gida dukana za’ayi”
Tsugunawa yayi daidai Saitin Fuskanta Yace
“Ki ansa ai bah nace kije dashi gida bneh”
Amsa tai ta soma bude ledan, Takeway neh da drink sai Icecream da cake. Takeawayn taketa Kici kicin budewa, dariya ya mata ya amsa ya bude mata, K’allan Abincin tai Sannan ta kalleshi
“Duka nawa neh”
Kai ya gyada mata yana cigaba da k’allanta da narkakun idanunshi..

Abincin ta soma ci hannu baka hannu kwarya, Kallanta yake cikeda tausayi, saida taci tai nak sannan ta dago tana mai murmushi
“Nagode Yaya”
Murmushi shima ya mata yasa yatsa ya taba Dimple dinta. Mik’ewa tai dasauri tana zare ido.
“Yaya lokaci na tafiya kuma ban saida gyada tah bah”
Hannu yasa a aljihu yace
“Nawa neh kudin gyadan?”
Girgiza mai kai tai dasauri
“A’a kah barshi wanda nakai jiya saida Baffa yamin Fada”
Kai ya jinjina kawai
“Yaya ka tafi nima zan koma, kah gaida min K’awata”
Bata jira mai zaice bah ta fara tafiya tana waigenshi tareda daga mai hannu. Binta yayi da k’allo harta bace…

*Shin ya labarin Dr Fareed neh??*

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

     *Page 126 to 130*

Bata jira mai zaice bah ta fara tafiya tana waigenshi tareda daga mai hannu. Binta yayi da k’allo harta bace ma ganinshi, Ajiyan zuciya ya sauke sannan ya shiga motarsa yaja yabar wajan…

Saida ya shiga cikin gari sosai Sannan yadau waya ya soma kira, ana dauka yace
“Am on my way na kusa gida”
D’an murmushi yayi Sannan yace
“Ok sai kah karaso”
Ya kashe wayan ya tura a aljihun shi. Bai zame koh ina bah sai gida, a haraban gidan yaci k’aro da Mahnoor ita da wasu masu aiki tana tayasu shara, girgiza kai kawai yayi ya nufi side dinshi. Tana ganin ya wuce ta aje tsintsiyan ta bishi, wanka ya farayi sannan ya fito Cikin Threequaters dah T shirt fari kal, zaune ya samu Mahnoor a falonshi tana K’allo, jin Karan bude kofa ta shagwabe fuska ta dago tana kallanshi
“Bro Masroor shine ka tafi bakaje dani bah koh”

Zama yayi kusa da ita ya kamo hannunta
“Am sorry sis, kinga fah bakwa nan and I cnt wait har sai kun dawo, dnt uh worry wata rana nan zata dawo ku zauna tare”
Zaro ido tai ta saki murmushi
“Allah dagaske bro Masroor”
Kai ya gyada mata shima yana murmushin kujimin wannan masroor din fah taya zata dawo gidansu

Phone dinshi yadau ringing ya dauka Sannan yace
“Ok ganinan zuwa”
Ya kalli Mahnoor wacce itama shi take kallo
“Barinje nayi bako”
Tare suka fito ita ta nufi side dinsu shi kuma ya fita wajan gate, a kofar gidan ya ganshi zaune Cikin mota, karasawa yayi yana y’ar murmushi
“Uh welcome old friend”
Dariya yayi Sukai musabaha, Masroor yace
“Wai gidan bakonka neh dah bazaka shiga bah”
K’asumbarshi ya shafa yana y’ar murmushi
“Banasan Mami ta ganni neh dan nasan sai nasha surutu”
Dariya Masroor yayi mai sauti
“Surutu koh sai kasha shi indai mami ce, saidai kah rufe ido kah toshe kunnuwan kah”

Yasir neh yayi parking ya fito yana murmushi
“Kai wah nake gani haka?”
Hannu yabashi suka gaisa “Dama ana ganinka”
Dariya yayi
“Yasir knan dama kana nan?”
A tare suka shiga cikin gidan zuwa side din Masroor, maids din gidan suka shiga hidima dasu. Jin surutu na tashi daga side din Masroor yasa Mahnoor ta shiga side din tana rarraba ido, dagowa bakonsu yayi yadan zare ido
“Wah nake gani nan kamar Mahnoor, lallai kin zama big girl”
Murmushi tai ta k’arasa kusada shi ta zauna
“Bro Sannu da zuwa”
“Yauwa” yace yana shafa kanta yana murnushi. Zamewa tai daga jikinshi ta fita daga daga side din… batafi minti biyar da fita bah wayan Masroor ya soma ruri..

Dauka yayi yasa a kunni sannan yayi murnushi yace
“Ok gamu nan zuwa”
Dariya ya saki mai sauti yana shafa sumar kanshi, binshi da kallo sukai da mamaki, sai dayayi mai isarshi Sannan yace
“Numbernka ya fito Mami na kiranka, kuma nasan Mahnoor ce ta fada mata”

Dariya Yasir shima yayi
“Kace mai lefi neh?”
Kai masroor ya gyada yana cigaba da dariya a hankali. Murmushi yayi ya mik’e
“Tho ku tashi muje”
Bah musu suka tashi suka nufi side din Mami, A falonta suka sameta zaune da bakuwa, kan carpet suka ya zauna su kuma Masroor da Yasir sukai d’are d’are akan kujera, sunkuyar dakai yayi sannan yace
“Ina yini Mami”

Kallanshi Mami ta tsaya yo jin shiru yasa ya dago suka hada ido ya maida kai dasauri
Murmushi tai
“Likita bokan turai Kama daga kai kawai, wato kasan bakada gaskiya shine harda zama a kasa”
Dagowa yayi yana y’ar dariya
“Mami knan kiyi hakuri, bana zama neh shiyasa”

Masroor da Yasir sai dariya suke mai yanata susunne kai, Mahnoor ce ta shigo falon ta zauna kusadashi a Kasa
“Bro fareed zakaje dani wajan Umma”
niko Ummy Abduol zaro ido nai jin sunan da mahnoor ta fada wah knan take nufi?

*manage dis banida chargi*

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

     *Page 136 to 140*

   *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

       Wannan Shafin Sadaukarwa ce gareku All *Da Bazarmu Writers Association* Members.. Allah ya bar K'auna.

Shekewa da dariya Hafsatu tayi harda tafawa
“Gaskiya neh Baffa haka yayi”

K’ara rushewa da kuka Sulthana tai jin Abinda Baffa yace, Saida tai mai isarta Sannan ta shigo cikin Gidan idanunta a kukumbure. Gyadan daya saba aje mata a kofar dakinshi ta dauka ta daura a wuta ta koma gefe tana cigaba da hawaye…

Yana dahuwa ta sauke ta zuba a tray, batayi mah Mama sallama bah ta tafi, inda suka saba zama ta hango Motar Masroor, ta k’arasa jiki asanyaye ta samu guri ta zauna batareda tamai magana bah. Sam bai lura da tazo wajan bah saida ya leko tah glass din motarshi sannan ya hangota zaune tayi tagumi, fitowa yayi dasauri ya k’araso inda take ya zauna
“Sulthana meke damunki”
Shiru tai k’anta a kasa

Ya marairaice Fuska yana cigaba da K’allanta
“Banasan ina ganinki cikin damuwa kinsan fah ina…”
Kasa k’arasa Maganan yayi ta dago jajayen idanunta tana kallanshi. Ajiyan zuciya ya sauke
“Meyasa yau kike so boyemin damuwarki? Nifah Abokinki neh kuma yayanki”
Hawaye ne ya gangaro mata, ta dago tana k’okarin Fashewa da kuka
“Baffa neh zaimin Aure”
“What?”
Fashewa da kukan tai ta duk’ar dakai K’asa

Rudu Masroor ya shiga ya mik’e ya dawo gabanta ya tsugunna
“Sulthana kin Tabbatar da abinda kike gayamin”
Batace komai bah sai kukan data cigaba
Suman kanshi yaja ranshi b’ace
“Pls Banasan kukan nan, ina jinshi har cikin raina. Just answer my question”

Ganin tak’iyin shirun yasa ya mike tsaye, k’ugunshi ya rik’e da hannu daya, dayan kuma yana cigaba da jan suman kanshi. Nan da nan idanunshi suka kad’a sukai ja
Tsugunawa yayi guiwa biyu a k’asa
“Pls stop crying, fadamin meya faru”

Cikin sheshekan kuka ta bashi labarin duk abinda ya faru
“No!!!” ya fada da k’arfi hakan jaya hankalin mutanen dake wajan suna k’allansu, bai damu da yanda ake kallansu bah saima cigaba da magana dayayi cikin D’aga murya
“No 1 can snach uh from me, u’re mine.”
Duk abinda yake fada bah wanda Sulthana tasan ma’anarshi idan bah no din bah, duk’ar dakai kawai tai saboda yanda mutane ke K’allansu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button