TAKUN SAAKA 10
Kansa ya ɗan girgiza da kai kofin coffee ɗinsa saman baki yana barin wajen nasu zuwa jikin windown ƙaramin falon da suke ciki na gidan da ya kawosu ɗazun. Wanda har yanzu basu san taka-maimai a cikin wace anguwa yake ba, dan basu fita ko soro ba har yanzu. Shi kadai ne ya fita bayan awanni takwas ya kuma dawo.
Wani hatsabibin murmushi ya sake saki idonsa kyam akan ƙwan wutar lantarki da ke a tsakar gidan. Haka ya cigaba da tsaiwa a jikin window ɗin yana cigaba da shan coffee ɗinsa da sauraren iya shegen yaransa akan Comments ɗin mutane da suka koma bibiya suma suna kwasar dariya.
Kofin da ya sake kaiwa baki yaji babu komai a ciki ya sakashi ɗago kofin ya kalla. Ba komai ciki ya shanye, hakan sai ya bashi dariya. Amma sai ya gintse kayansa baiyiba sai a zuciya. Juyowa yay da baya ya ajiye cup ɗin ya ɗauka file ɗin da Habib ya ajiye. Cikin muryarsa da sautinta ke fita da nutsuwa da amo yace, “Ayi addu’a kafin a kwanta. Goodnight”.
Kusan a tare suka haɗa baki wajen faɗin, “ALLAH ya tashemu lafiya boss. Sweet dream tare da ƙarin ƙyaƙyƙyawar idea akan ƴan ruda”.
Daƙƙuwa yay musu batare da ya juyoba. Sai dai ya saki murmushi dai-dai yana shigewa. Duk da basuga murmushin nasa ba kasancewar ya juya musu baya hakan bai hanasu yin kananun dariyar farin ciki ba gaba dayansu.
Yana shigewa suka farma gasassun kajin da ya kawo musu tun shigowarsa da ci. Dama sun ɗan ɗaga kafa ne ganin yazo a cikin yanayin babu wasa. Yanzu ko sunsan komai normal ne, sai abinda ba’a rasaba saboda rikita-rikitar Master ɗinsu bata taɓa karewa. Daya toshe waccan matsalar zai ɓallo wata da kansa kafinma ƙurar wadda ya tayar ta lafa.
Shima ko da ya shiga ɗakin zazzafan numfashi ya furzar. Ko’ina fes dan tun bayan barinsu da yayi suka gyara komai. Ya jefa file ɗin hannunsa saman madai-daicin gadon. Kayansa ya shiga zamewa alamar son watsa ruwa. Ya rage da ga shi sai singlet da boxer. A haka ya nufi toilet ɗin.
Tsahon mintuna ashirin ya ɗauka a ciki kafin ya kammala, tun kafin ya fito da ga bayin ya ziro hannu ya kashe wutar ɗakin baki ɗaya. Batare da damuwa da duhun da ya mamaye ko ina ba ya fito a haka. Ta cikin duhun ya iso bakin gadon, ya kai zaune cikin lalube ya ɗakko wayarsa ƙarama. Fitilarta ya kunna, tare da ɗaukar file ɗin da Habib ya bashi. Sam ba’a ganin fuskarsa. Sai dai shi yana ganin rubutun file ɗin kasancewar shi ya haska kai tsaye. Sai alamun bathrobe ɗin dake a jikinsa wadda iya inda hasken ya haska kawai ake gani.
“What?!”.
Ya faɗa cikin subucewar baki ganin bayanan na nuna cewar da taimakon mace aka kai musu harin ɗazun. Macen ma ƴar 18 years kacal. Cikin wani irin rawar jiki yay wurgi da file ɗin yana faɗin, “Impossible! Ni! Ni! Ni ne yarinya ƙarama kamar wannan zata hara. Hari irin wanda wani mahaluki bai taɓa samun galabar yimin shi ba. Kuturun ubacan kayyasa????…………✍
*_HHHH anayi muna ɓallar rake na funtuwa mai zaƙi. Alaji Master yaya take ne?????????????. In baka saniba ma yanzu ne wasan zai fara????????????_*
*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*
*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????
#team ZAFAFA BIYAR????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*
[ad_2]