TAKUN SAAKA 11

“Miya faru kuma?”. Yaya Abubakar dake miƙa mata ruwa ya faɗa. Hawayen data matso suka silalo saman kumatunta. Muryarta na rawa tace, “Yayanmu Yaya Ammar fa?”.
Shiru suka ɗanyi duk suna kallonta. Kafin Yaya Abubakar ya shafa kanta fuskarsa ɗauke da murmushin ƙarfin hali. “Karki damu shima zai dawo, insha ALLAH bazai kwana acan ba. Ƙarasa cin abincinki ina zuwa”. Ya ƙare maganar yana mikewa. Tashi Yaya Usman yay yabi bayansa.
Police station ɗin da aka kai Ammar suka nufa. Tun shigowar su Yaya Abubakar wasu a cikin ƴan sanda suka shaidashi saboda aiki ya taɓa haɗashi da wasu a cikinsu. Amma duk da haka sai ya nuna musu i’d card ɗinsa. A zabure sauran ma suka shiga gaishesa. Aka kuma masa iso ofishin ogan wajan.
Tun a shigowarsu ya shaida Yaya Abubakar ɗin. Amma sai ya maze abinsa. Yaya Abubakar ya cije lip ɗinsa dan akwai ƴar tsama a tsakani. Sai dai yana sama da shi. Cikin nuna bai damu da basarwar tasa ba yay masa bayanin kansa. Tare da buƙatar a bashi Ammar.
Cikin yatsine fuska ɗan sandan yace, “To yallaɓai idan ku matsayinku na manya kuna haka su kuma wanda basu da dangi ƴan sanda kuma fa? Laifi ƙaninka yay aka kawosa nan, sai kuyi haƙuri mu gama tattara bayanai akansa mukai maganar kotu kamar zaifi”.
Sosai Yaya Abubakar ya kafesa da ido. Sai kuma ya saki wani lalataccen murmushi yana miƙewa dan yasan wannan tsarin da ga Abba yake. “Wanann basirar ba taka bace. Amma ga saƙo ka bama wanda ya tsara maka ya kuma biyaka. Ya kiyayi ranar maida murtani dan zata kasance mai ɗaci da tsauri. Ya kuma bar raina allura dan itama ƙarfe ce. Duk randa zuri’ar Aliyu Hamza gwarzo sukaji a ransu zasu maida murtani TAKUN SAAƘAR bazai masa ƙyau ba. Wannan hanunka mai sanda ne”. Yaya Abubakar ya ƙare maganar cike da gargaɗi.
Murmushi Yaya Usman yayi. Dan bai taɓa zato da tunanin yaya Abubakar ɗin nasu ya iya zaro zance haka na. Koda suka fito da kansa yasa a kaisa cell ɗin da Ammar yake. Shine ya amshi key tun daga kanta ya buɗesa da kansa.
Wani irin kallo ya tsaya yanama Ammar da yaci uban duka. Da alama ma ba’a jima da dukan nasa ba, dan duk sabbin raunuka ne a jikinsa dake fidda jini. Komai baiceba a lokacin sai kama hannun Ammar ɗin daya taso da sauri yana tambayarsa “Ina Ummi take?” yayi. Bai amsa masa tambayarsa ba sai da suka iso kantar. Ya duba ƴan sandan wajen da sukai tsuru-tsuru cikin kaushin murya yace, “Su waye sukai wannan aikin?”.
Kallon kallo aka shigayi. A matuƙar tsawace yace, “Ba magana nake ba ne?!!”.
Zabura duk sukayi har tsirarun mutane da sukazo belin ƴan uwansu da masu kawo abinci. Cikin rawar murya wani ɗan sanda yace, “Yallabai wlhy ba laifinmu bane sakamu akayi”. Ya ƙare maganar a hankali cike da raɗa saboda fitowar ogansu da ga office dan jin tsawar da Yaya Abubakar yayi.
Takarda Yaya Abubakar ya fisga ya jefama ɗan sandan da yay maganar. “Ina son duka sunayen members na ƴan sandan dake a station ɗin nan. Wanda sukai wannan dukan kuma sunayensu su kasance a ware”.
Wani busashshen yawu ya haɗiye da ƙyar yana ɗaukar takardar. Jikinsa sai tsuma yake ya shiga zano sunayensu ɗaya bayan ɗaya. Bayan ya kammala cikin girmamawa ya mikama Yaya Abubakar ɗin. Uffan baice masaba ya amsa tare da jan hannun Ammar da Yaya Usman ya riƙe ta ɗayan gefen suka fice da ga station ɗin.
Ko a mota ma babu wanda yay magana dan zuciyar Yaya Abubakar takai ƙololuwar ɓaci game da lamarin Abba. Asibitin suka wuce da Ammar shima. Ba ƙaramin tashi hankalin su Yaya Muhammad yay ba ganin dukan da akaima Ammar. Hibbah kuwa kuka ta fashe musu da shi tare da zuwa ta rungume Ammar ɗin.
“Wash ALLAH auta zafi”.
Ya faɗa cike da shagwaɓa saboda jin ta ƙankame masa hannunsa da yake da tabbacin ƴan sandan sun ji masa ciwo. Saurin sakin hanun nasa tai tana sake fashewa da kuka. Ya kai hannu bisa kanta ya dafa yana murmushin ƙarfin hali. “K karki maidani kamar ba namijiba mana. Bakisan dukan ƙarfi ya ƙara min ba ma”.
A yanda yay maganar ya saka su Yaya Umar yin murmushi suna girgiza kansu. Hibbah kuwa kukan ne ya sake kufce mata.
Yaya Umar ne ya kaisa akai treatment ɗinsa da bashi magunguna. Sauran abincin da Hibbah taki ci suka matsa masa yaci da ƙyar shima. Dan sai da Hibbah ta dinga basa a baki yau babu faɗa. Bayan ya kammala yasha magungunan da aka bashi. Duk yanda sukaso yaje gida ya huta yaƙi, yace shima sai yaga fitowar Ummi.
Sha’awa yanda suke ƙaunar junansu ya bama doctor Bilal. dan haka ya bama Ammar ɗin shawarar yazo office ɗinsa ya kwanta to har komai ya kammala sai a tashe sa. Nanma da ƙyar ya amince bisa umarnin yaya Muhammad. Haka dai ya miƙe yana tura baki Hibbah na masa gwalo.
_____________★★★_____________
Duk yanda yaso yin shirin barci ya kwanta hakan ya gagara. Sai fama kai kawo yake a cikin ɗakin, abubuwa da yawa zuciyarsa ke raya masa game da matakin da ya kamata ya ɗauka a kanta. Inhar zata iya kai masa hari ta samesa a ƙanƙanin lokaci. To wane irin shiri kenan zatai a gaba dominsa? Lallai dole ne yasan ita ɗin wacece? Mi kuma ta taka ne haka?. Shin sakata akai? Kokuwa yin kanta ne?.
Waɗanan jerin tambayoyi suketa faman masa kai kawo a zuciya da hanashi nutsuwa. Shiri ya canja saɓanin pyjamas da ya kamata ya saka sai yasa wasu kayan daban.
Yaransa na falon zaune har yanzu suna sha’aninsu sai ganinsa sukai ya fito. Mamakine ya kamasu dan duk zatonsu ya kwanta.
“Boss da matsala ne?”.
Salisu ya faɗa cike da girmamawa.
Kansa ya girgiza masa yana ƙoƙarin ɗaura agogonsa. Sai da yaje gab da fita a falon yace, “Zanje wani waje ne, wani yazo ya rufe gidan”.
Saurin miƙewa Khalid yayi duk da tambayoyine fal bakunansu amma babu damar yi, dan ya nuna baya buƙatarsu. Su ko saboda trianing da suka samu da ga garesa da kowanne irin yare yay magana ko yay nuni suna fahimtar kayansu.
Koda ya wuce Khalid ya dawo zaman tattaunawa sukai, amma sai basu gano komaiba, dan haka sukai jigum-jigum……
________________________________
Alhmdllhi ƙarfe goma aka fiddo Ummi da ga ɗakin theatre cike da nasara. Bayyana muku irin farin cikin da su Yaya Muhammad suke ciki ɓata lokaci ne. Basu sami damar ganinta ba dan an miƙata ɗakin hutu ne. Sai dai bayanin da Dr Sageer yay musu na narar aikin ya saka zukatansu nutsuwa. Har suka amince da shawararsa ta tafiya gida dan ba’a bukatar kowa tare da Ummin sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu.
Basuyi wani zaman ɓata lokaci ba suka tattara suka wuce bayan an tado Ammar da zazzaɓi mai zafi yayma ligif saboda dukan da yaci. Sosai tausayinsa ya bayyana bisa fiskokinsu. Sai dai komai basuce ba bayan Hibbah da ke ta jera masa sannu kamar zatai kuka. Kaɗan-kaɗan ta ɗaura hannunta a goshinsa.
Suna gab da zuwa gida ya bige hannunta data ɗora masa a karo na babu adadi. “K dalla kin isheni, ga hannunki da sanyi”.
Baki Hibbah ta tura gaba. Cike da tsiwa ta murguɗa masa baki da faɗin, “Oh dama ka samu na damu da kai zaka min wani iyayi”.
“To waya aikeki? Uwar iya mai cinikin iya”. Ya faɗa yana gyara kwanciyarsa jikin kujera.