TAKUN SAAKA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAKUN SAAKA 11

      Murmushi Yaya Usman da ke kusa da su yayi yana girgiza kansa kawai. Dan inda sabo sun saba gani. Anjima kaɗan kuma kaga sun koma hirar arziƙi. Kafin awa ɗaya ta rufa sunyi faɗa sau biyu.

        Cikin jin haushi Hibbah tace, “Idanma kaga na sake kulaka dan ALLAH ka tsine min Yaya Ammar”.

          Baki Ammar ya taɓe da faɗin “ALLAH na gode maka na jefar da ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda”.

       “Yaya Usman ka ganshi ko?”. Ta faɗa kamar zatai kuka.

        “Ya isa manta da lamarinsa auta. Ko sannu karki sake masa har ya warke”.

         “Ai baran masa ba ko Yayanmu”. Tai maganar da dungurin wajen ciwon da ke a hannunsa. Ƙaramar ƙara ya saki yana bige mata hannu dan yaji zafi. Ta ƙyalƙyale da dariyar mugunta. Ranƙwashi mai shegen zafi ya bata wanda ya saka bakinta rufewa ruf, sai kuma ta fashe da kuka.

        Yaya Abubakar da duk yake jinsu da ga gaba ko kallo basu ishesa ba. Sai ma waya da ya ɗauka yay kiran maigadi ya buɗe musu gate. Koda suka shiga cikin gidan tsitt yake alamar jama’ar cikinsa harsun ƙwanta. Kusa da inda Yaya Muhammad yay parking shima yayi gab da sashensu.

    Hibbah da ke kukan ranƙwashin da Ammar yay mata ta fara fita domin kaima Yaya Muhammad ƙara tunda Yaya Abubakar bai bada fuska ba.

      “K zoki wuce ciki ki kwanta”. Yaya Abubakar ya dakatar da ita dan bayasan wani dogon magana a yanzu. Yasan kuma indai Hibbah ce bataƙi su kwana ana shashanci ba. Baki ta tura gaba sim-sim ta nufi sashensu.

     Yaya Muhammad yay ɗan murmushi yana kallon Yaya Abubakar ɗin. “Siddiq yau fa gaba ɗaya ka zama masifaffe. Kasa duk auta ta firgita da kai”.

        “Tana da cika ciki ne wani lokacin”. Yaya Abubakar ya bashi amsa yana kashe motar. Yaya Ammar yace, “Dama hakan kowa ke mata da mun huta da shegen ƙiriniyarta tamkar ƴar mage”.

      Kusan duk sai da sukai ƙaramar dariya. Da ga haka suka shige makwancinsu kowa ya nufi ɗakin barcinsa.

        Hibbah ma da ta shiga tanata zunɓure-zunɓure shirin barcin tai tana kunkunin wai dan anga Ummi bata nan kowa ya tsaneta. Gobe a asibiti zata kwana bazata biyosu su cinye ta ba. 

         Da ƙunkunin dai harta kammala shirin barcin ta kwanta bayan tayi addu’a. Sai kuma a lokacin tunanin duk abinda ya faru a wannan yini ya shiga dawo mata. ALLAH dai ya taimaketa barci barawo yaci galaba akanta batare data shirya hakan ba.

*_WASHE GARI_*.

           Yau Yaya Umar ne ya shigo yama Hibbah knocking. Sai da yaji ta tashi sanann ya juya ya fita bayan ya mata gargaɗin karta koma barci ta shiga kitchen idan sun dawo salla zaizo ya tayata haɗa breakfast. Da to kawai ta amsa masa dan harga ALLAH barcin bai isheta ba. Sai dai sanin halin masifarsa yasata bin umarninsa bayan ta idar da sallar tai azkar ta fita kitchen ɗin. Bata jima da fara aikin ba suka dawo. Su dukansu babu wanda bai iya girki ba dan Ummi babu abinda bata sakasu na aikin gida. Shiyyasa bata taɓa damuwa da zama da ƴar aiki ba tun da suka fara tasawa. 

     Yaya Umar ne ya tayata sukai breakfast ɗin. Yaya Usman kuma yanata ƙoƙarin gyara gidan shi da Ammar da ya tayasa dan jikin nasa da sauƙi bakamar jiya ba. Magungunan da aka basa sun taimaka masa matuƙa. Cikin kankanin lokaci suka kammala komai tsaf kowa ya tafi dan watsa ruwa. Sabo da fita aiki yasa duk suka hallara akan lokaci bisa dining. Sai uwar latti ce ko motsinta babu sai da Yaya Muhammad ya je da kansa yay mata knocking.

           Koda ta fito masifa Yaya Umar da Usman suka hauta da shi na sakasu yin latti kamar kullum. Cikin son a kareta ta kalla Yaya Abubakar da Muhammad. Duk murmushi sukai mata da nuna mata kujera alamar ta zauna ta rabu da su Umar ɗin. Fuska a kumbure taja kujera ta zauna kuwa. Da ga haka suka fara karyawa.

      Sunyi nisa sosai acin abincin Abba ya shigo fagan-fagan Hajiya Mama biye da shi. A tare duk suka ɗago suka zuba musu ido. Sai wani irin tsoronsu da shakkarsu ya shigi su Abban lokaci guda. Yaya Muhammad ne ya fara ɗaule kansa ya maida ga abincin gabansa. Suma sauran duk sai suka yi kamar yanda yay ko gaishesu basuyi ba.

      Cikin masifa Hajiya mama tace, Kunci ubanku marasa mutunci. mu zaku kalla ku watsar tamkar wasu kashi?”.

     A mamakinsu ko motsi babu wanda yayi, sai ma cigaba da cin abincinsu sukeyi hankali kwance. Hajiya Mama da Abba sukai galala a tsaye kamar gunkuna suna kallon sabon salon iskanci. Suko sunyi tamkarma basusan da zamansu a wajenba. 

     Wani irin baƙin cikine ya lulluɓe Abba ya shiga zazzaga tujara musamman akan fiddo Ammar, dan dama tun jiya ɗan sandan ya kirasa ya sanar masa. Ya kuma tabbatar masa da Abubakar yana tare da manyansu sosai, idan ya matsa akan Ammar ɗin tofa wata da tafi wadda suka shirya zata taso. Hakan yasa Abbana ɓam da bakinsa. Ya dai ɗauka alwashin zubarma da Ummi tujara tare da sauke duk fushinsa a kanta. Shiyyasa yana kammala sallar safensa da ya keyi a gida kullum bayan rana ta fito ya nufi sashen hajiya Mama ya sanar mata. Shine fa suka taho yima Ummi taron dangi basu san ma bata gidan ba. A zatonsu kuma su Yaya Abubakar ɗin sun fita.

           Duk iya tujarar da sukeyi babu wanda yay koda motsi balle nuna yasan da zamansu a wajen har suka kammala breakfast ɗinsu Ammar da Hibbah suka kwashe kayan zuwa kitchen. A gurguje suka wanke kwanikan ita da shi su ka fito dauke da basket ɗin abincin da suka shiryama Ummi irin wanda doctor da suka kira ya tabbatar musu zata iya ci tunda ta farfado tun daren jiyan.

     Har yanzu Abba da Hajiya Mama na a sashen suna zubda ruwan tujara. Yayinda kuma babu wanda yay musu koda tari. Hakanne ya sake harzuƙa musu zukata da wanann sabon salon rainin wayon su Yaya Muhammad ɗin. A gabansu kuma suka kulle kowanne ƙofar ɗaki da ke a sashen har kitchen sukai ficewarsu suka barsu a falo. Wannan al’amari yayi matuƙar bakanta ran Abba da Hajiya mama. Kai har ma Momy da ƴaƴanta mata huɗu da duk suka fito saboda hargowar su Abban.

         Motar Yaya Muhammad da Yaya Abubakar duk suka shiga yau ma suka fice batare da kowannensu ya hau mashin ba.

     Bayan fitarsu tujara ta gidan duniya babu irin wadda Abba da hajiya mama basuyiba a gidan. Ummi ta sha gori da tonon sililin asalinta. Sai da sukayi mai isarsu sukaga babu mai taya musu Sannan sukai shiru. Abba ya shirya fagan-fagan yabar gidan zuwa inda zuciyarsa ke raya masa domin yin maganinsu Yaya Muhammad ɗin baki ɗaya………….✍

*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button